Wata Sabuwa: Sanatocin Amurka Sun Kunnowa Gwamnatin Trump Wata Wuta kan Yaki da Iran
- Wasu sanatocin jam'iyyar Democrat sun taso gwamnatin Donald Trump a gaba kan wani hari da ake zargin Amurka ta kai a Iran
- Sanatocin da ke bangaren adawa sun bayyana cewa sun kadu matuka kan harin wanda ya jawo sanadiyyar rasuwar mutane 170
- Matsin lambar sanatocin na zuwa ne bayan wani sabon faifan bidiyo ya nuna cewa akwai alamun dakarun sojojin Amurka ne suka kai harin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Manyan sanatoci daga jam’iyyar Democrat a Amurka sun yi kiran da a gudanar da bincike kan harin da aka kai wa wata makarantar yara mata a Kudancin Iran.
Sanatocin sun bayyana cewa dole ne ma’aikatar tsaro ta Pentagon ta ba da cikakkun amsoshi game da lamarin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutane 170.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta ce ’yan majalisa guda shida ne suka fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa a daren Lahadi, 8 ga watan Maris 2026.
Sanatoci sun kadu da harin da aka kai a Iran
'Yan majalisar sun bayyana cewa sun “firgita” da harin da aka kai wa makarantar yaran da ke birnin Minab a lokacin harin farko na haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila ranar 28 ga Fabrairun 2026.
Jaridar Haaretz ta ce sanatocin su ne manyan mambobin jam’iyyar Democrat a kwamitocin tsaron ƙasa na Amurka.
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“Kisan yaran makaranta abin ban tsoro ne kuma ba za a amince da shi ba a kowane irin yanayi."
Hari kan makaranta a Iran ya yi barna
Wannan matsin lamba ya zo ne yayin da wani sabon faifan bidiyo na harin ya nuna cewa akwai yiwuwar makami mai linzami na Tomahawk ne ya samu makarantar, makamin da Amurka ke amfani da shi wanda Isra’ila da Iran ba su da shi.
Harin bam ɗin a Minab ya zama babban misali na yadda adadin fararen hula da ke mutuwa a wannan rikici yake ƙaruwa.
Jami’an Iran sun bayyana cewa hare-haren Amurka da Isra’ila sun lalata wasu makarantun, da kuma asibitoci, gidajen jama'a, kasuwanni, matatar sarrafa ruwan sha, da sauran wuraren farar hula.
A cewar mataimakin Ministan lafiya na Iran, Ali Jafarian, hare-haren Amurka da Isra'ila sun kashe mutane 1,255, akasarinsu fararen hula tun farkon fara yaƙin.
Sanatoci sun bukaci a gudanar da bincike
Sanatocin sun bayyana a cikin sanarwar su cewa Ministan tsaro Pete Hegseth ya fito fili yana alfahari da sassauta dokokin yaƙi a hare-haren da ake kai wa Iran, don ba wa dakarun Amurka damar yin ruwan bama-bamai ba tare da takura ba.

Source: Facebook
Wani bangare na sanarwar na cewa:
“Minista Hegseth yana buƙatar tabbatar da cewa binciken da ma’aikatar tsaro ke gudanarwa kan wannan hari ya kasance mai zurfi, sannan ya ba wa al’ummar Amurka da Majalisa cikakkun amsoshi kan yadda da kuma dalilin ya sa wannan bala’i ya faru."
Waɗannan ’yan majalisa waɗanda suka haɗa da Brian Schatz, Jeanne Shaheen, Jack Reed, da Elizabeth Warren sun jaddada cewa dole ne a gudanar da bincike mai zaman kansa kan wannan lamari da duk wani makamancinsa.
Trump ya magantu kan kawo karshen yakin Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan kawo karshen yakin kasarsa da Iran.
Shugaba Donald Trump ya sake maganar da ke nuna cewa yakin da ya ke yi da Iran ya kusa zuwa karshe.
Donald Trump ya ce yakin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran zai kare nan ba da jimawa ba, bayan kwanaki 10 ana kai hare-hare masu tsanani a yankin Gabas ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


