Ba Sauki: Mayakan Hezbollah Sun Yi Wa Sojojin Isra'ila Kwanton Bauna, Sun Yi Masu Illa
- Ana ci gaba da gwabza fada tsakanin mayakan kungiyar Hezbollah da dakarun sojojin Isra'ila a Kudancin Lebanon biyo bayan yakin da ya barke a tsakaninsu
- Kungiyar Hezbollah ta bayyana cewa ta yi wa dakarun sojojin Isra'ila kwanton bauna inda ta samu nasarar yi masu illa a yakin da ake yi
- Hakazalika, ta bayyana cewa mayakanta sun kai hare-hare ta hanyar amfani da rokoki da makamai masu linzami kan dakarun sojojin Isra'ila a wurare da dama
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Beirut, Lebanon - Mayakan kungiyar Hezbollah da ke kasar Lebanon sun kaddamar da hare-hare kan dakarun sojojin Isra'ila.
Mayakan na Hezbollah sun kaddamar da hare-haren ne kan dakarun sojojin Isra'ila a Kudancin Lebanon.

Source: Getty Images
Tashar Aljazeera ta kawo rahoton cewa mayakan na Hezbollah sun kaddamar da hare-haren ne a ranar Talata, 10 ga watan Maris 2026.
An yi kwanton bauna ga sojojin Isra'ila
Kungiyar ta bayyana cewa mayakanta sun yi wa sojojin Isra'ila kwanton ɓauna a gefen birnin Khiam kuma sun yi nasarar samun tankokin yaƙi na Merkava guda uku.
Ta bayyana an ga motocin na yaki guda uku suna ci da wuta sakamakon harin da aka kai musu, shafin Middleeasteye ya kawo labarin.
Tun da farko, kungiyar ta ce ta harba jerin makaman rokoki guda biyu kan dakarun Isra'ila a garin Markaba, sannan ta kai harin manyan bindigogi kan dakarun Isra'ila a yankin Khanouq na ƙauyen Aitaroun.
Hezbollah ta kai hare-hare kan sojojin Isra'ila
Haka kuma ta yi iƙirarin kai hari ta hanyar harba rokoki kan sojojin Isra'ila a kan tsaunin Kahil da ke gabashin garin Maroun al-Ras da ke kan iyaka.
Ƙungiyar ta Hezbollah da ke Lebanon ta ce ta ƙaddamar da harin rokoki kan sansanin kula da jiragen sama marasa matuƙa na Givaa, da ke gabashin birnin Safed na Isra'ila.
Hakazalika, ta bayyana cewa harba rokoki kan barikin Yiftah da ke kusa da kan iyaka a Kudancin Lebanon da Arewacin Isra'ila.

Source: Twitter
Hezbollah ta kuma bayyana cewa ta kai harin jirgi mara matuƙi kan sansanin Tziporit, da ke gabashin Haifa, a safiyar ranar Litinin, da kuma harin makami mai linzami kan sansanin Tel Hashomer, kusa da Tel Aviv, da yammacin ranar.
Fada dai ya barke ne tsakanin Hezbollah da sojojin Isra'ila tun bayan da Amurka da Isra'ila suka kaddamar da hare-hare ta sama kan kasar Iran.
An samu sabani tsakanin Amurka da Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa sabani ya gitta tsakanin Amurka da Isra'ila kan yakin da suke yi da kasar Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.
Sabanin dai ya auku ne kan wasu hare-hare da Isra'ila ta kai kan rumbunan adana man fetur guda 30 na kasar Iran, wadanda suka jawo gagarumar barna.
Amurka tana fargabar cewa hare-haren Isra'ila kan kayayyakin more rayuwa da ke amfanar talakawan Iran na iya haifar da koma-baya ta fuskar dabarun yaƙi.
Asali: Legit.ng

