Trump Ya Sake Maganar Kawo Karshen Yaki da Iran, Ya Yi wa Duniya Albishir
- Shugaban Amurka ya sake magana game da yunkurin kawo karshen yakin da ya hada kai da Isra'ila ya afkawa Iran a karshen Fabrairun 2026
- Donald Trump ya yi magana ne a jihar Florida bayan cika kwanaki 10 da fara yakin, inda ya bayyana nasarorin da ya yi ikirarin sun samu
- Bayanin da ya yi a Florida ya biyo bayan wata sanarwa da ya fitar jim kadan bayan tattaunawa da Firaministan kasar Rasha, Vladimir Putin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya sake maganar da ke nuna cewa yakin da ya ke da Iran ya kusa zuwa karshe.
Tun da aka fara yaki a ranar 28 ga Fabrairun 2026, Donald Trump na ikirarin yana samun nasara, inda ita ma Iran ke nuna ita ce ke maganin Amurka da Isra'ila.

Source: Getty Images
Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa Shugaban Amurka ya yi bayani game da wasu nasarori da ya ce sun samu wajen kai hare-hare a kwanki 10 da suka wuce.
Batun kawo karshen yaki da Iran
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yakin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran zai kare nan ba da jimawa ba, bayan kwanaki 10 ana kai hare-hare masu tsanani a yankin Gabas ta Tsakiya.
CNN ta ce Trump ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a Doral da ke jihar Florida, inda ya ce yakin na iya kasancewa gajere kuma yana sa ran za a kawo karshensa cikin kankanin lokaci.
Shugaba Trump bai bayyana ainihin lokacin kawo karshen yakin ba, amma maganar da ya yi ta yi kama da wacce ya yi a baya, inda ya ce yakin ya cimma manufarsa a yanzu.

Source: Getty Images
Nasarar da Donald Trump ya ce ya samu
Shugaba Donald Trump ya ce hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai sun lalata muhimman wurare da kayayyakin soji na Iran.
A cewarsa, sojojin Amurka da Isra’ila sun kai hare-hare kan wurare kusan 5,000 a cikin Iran tun bayan fara yakin da ya hada kai da Isra'ila.
An fara rikici ne a ranar 28 ga Fabrairu lokacin da hare-haren hadin gwiwa na Amurka da Isra’ila suka kashe jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, lamarin da ya jawo rikici mai girma a yankin.
Tun daga lokacin, Iran ta fara mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuki kan wurare daban-daban a yankin Gabas ta Tsakiya.
Faransa ta yi magana kan yakin Iran
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya yi magana game da yakin da Amurka da Irsa'ila ke yi da Iran.
Macron ya tabbatar da cewa ya yi wayar tarho da shugaban Iran domin lalubo hanyar da za a magance matsalar ta hanyar diflomasiyya.
Wasu rahotanni sun kara da cewa shugaba Macron ya yi magana da wasu shugabannin Gabas ta Tsakiya game da yadda za a magance rikicin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

