Iran Ta Yi Zargin an Yi Karya da Sunanta a Harin da aka Kai Turkiyya
- Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi waya da Shugaban Masoud Pezeshkian na Iran domin tattauna rikicin yankin
- Tayyib Recep Erdoğan ya jaddada cewa Türkiye na son buɗe ƙofa ga diflomasiyya domin rage tashin hankali a Gabas ta tsakiya
- Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya ce makaman roka da suka shiga sararin samaniyar Türkiye ba daga Iran suka fito ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Turkey – Shugaban ƙasar Türkiye, Recep Tayyip Erdoğan, ya yi wata muhimmiyar tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, bayan gwamnatin Iran ta nemi a yi magana.
A yayin kiran, Erdoğan ya bayyana cewa akwai buƙatar a buɗe ƙofar diflomasiyya domin a rage rikicin da ke ƙara kamari a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Ana cikin musayar wuta, Shugaba Putin ya aika sako ga sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei

Source: Twitter
A sakon da gwamnatin kasar ta wallafa a shafin X, ya ce Türkiye na yin ƙoƙari sosai wajen taimaka wa a samar da yanayin da zai ba da damar tattaunawa da sasanta rikici.
Kasar Turkiyya ta tattauna da Iran
Erdoğan ya kuma bayyana cewa Türkiye ba ta goyon bayan duk wani shiga tsakani da ta saba wa dokokin ƙasa da ƙasa da ake yi kan Iran.
Sai dai a lokaci guda, ya nuna damuwa kan hare-haren da ake kai wa wasu ƙasashen yankin da Türkiye ke ɗauka a matsayin 'ƙasashe ‘yan’uwan juna.'
A cewarsa, kai farmaki kan ƙasashen yankin ba zai amfanar da kowa ba, don haka ya kamata dukkannin ɓangarori su dakatar da irin waɗannan hare-hare domin kauce wa ƙara tayar da rikici.
Shugaban ya kuma nuna cewa rikicin da ke faruwa a yankin yana shafar Türkiye kai tsaye, duk da cewa ba ta cikin ɓangarorin da ke rikicin.
Damuwar Turkiyya kan yaƙi da Iran
Raccep Tayyib Erdogan ya ce wannan yaki na kawo barazana ga tsaron yankin da kuma zaman lafiya gaba ɗaya.
Erdoğan ya kuma jaddada cewa keta sararin samaniyar Türkiye, ko ta wane dalili ne, ba abin da za a iya amincewa da shi ba.
Ya ce gwamnatin Türkiye za ta ci gaba da ɗaukar duk matakan da suka dace domin kare sararin samaniyarta da tsaron ƙasar.
A cewarsa, duk wani yunkuri da zai karya dokokin sararin samaniyar Türkiye zai fuskanci matakan kariya da hukumomin ƙasar ke da su.
Har ila yau, Erdoğan ya nuna alhini matuƙa kan asarar rayukan da aka yi a wasu hare-hare, musamman mutuwar yara a harin da aka kai makaranta a garin Minab da ke Iran.

Source: Getty Images
Ta'aziyyar Khamenei da martanin kasar Iran
Shugaban na Türkiye ya kuma sake miƙa ta’aziyyarsa kan rasuwar jagoran addini kuma jagoran ƙasa na Iran, Ali Khamenei.
Ya bayyana fatan cewa zaɓen Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran koli zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a yankin.
A nasa ɓangaren, shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya shaida wa Erdoğan cewa makaman roka da suka shiga sararin samaniyar Türkiye ba daga Iran suka fito ba.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Iran za ta gudanar da cikakken bincike domin gano yadda lamarin ya faru.
Amurka ta sabunta barazana kan Iran
A baya, kun samu labarin cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi gargadi mai tsauri ga Iran kan yiwuwar hana zirga-zirgar mai ta mashigar Hormuz.
Donald Trump ya ce Amurka za ta kai hari mai matukar muni fiye da yadda aka taba yi idan Iran ta katse hanyoyin wucewar mai da kasashen duniya ke amfani da shi.
Shugaban ya kara da cewa kasashe da dama, musamman China, za su amfana idan aka ci gaba da bude mashigar domin a ci gaba da jigilar mai lami lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

