Amurka Ta Taɓo China a Yaƙin Iran, Ta Tura Gargaɗi kan Rufe Mashigar Hormuz

Amurka Ta Taɓo China a Yaƙin Iran, Ta Tura Gargaɗi kan Rufe Mashigar Hormuz

  • Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi gargadi mai tsauri ga Iran kan yiwuwar hana zirga-zirgar mai a mashigar Hormuz
  • Trump ya ce Amurka za ta kai hari sau 20 fiye da yadda aka taba yi idan Iran ta katse hanyoyin wucewar mai
  • Shugaban ya kara da cewa kasashe da dama, musamman China, za su amfana idan aka ci gaba da bude mashigar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

USA – Shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump, ya gargadi Iran cewa Amurka za ta mayar da martani mai tsauri idan kasar ta dauki wani mataki da zai hana zirga-zirgar mai a mashigar Hormuz.

Ya yi wannan barazana ne a yayin da Iran ta ce za ta nutsar da duk wani jirgin ruwa da Amurka ta turo rakiyar jiragen mai a yankin.

Kara karanta wannan

Trump ya tona ƙullin da Amurka ke yi wa sabon jagoran addini na Iran

Trump ya yi sabuwar barazanar kan mashigar Hormuz
Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Twitter

Trump ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, wanda Fadar White House ta wallafa a shafin X.

Barazanar Trump ga Iran

Donald Trump ya ce Amurka ba za ta lamunci duk wani yunkuri da zai kawo cikas ga safarar mai a wannan muhimmin wuri na duniya ba.

A cikin sakon nasa, Trump ya ce idan Iran ta dauki matakin, Amurka za ta kai hari mai tsanani fiye da yadda aka taba gani.

Ya ce:

“Idan Iran ta yi wani abu da zai dakatar da wucewar mai a mashigar Hormuz, Amurka za ta kai mata hari sau 20 mafi tsanani fiye da yadda aka taba kai mata .”

Trump ya kara da cewa Amurka na da karfin da za ta iya lalata wasu wurare da ake iya kai hari cikin sauki, wadanda a cewarsa za su sa Iran ta kasa sake farfadowa a matsayinta kasa.

Kara karanta wannan

Iran ta gargaɗi Amurka, ta faɗi abin da zai faru da jiragen da Trump zai tura Hormuz

Ya ce:

"Za mu lalata wasu wurare masu saukin kai hari da za su sa kusan ba zai yiwu Iran ta sake dawowa da karfi a matsayin kasa ba.”

Fatan Trump a kan Iran

Sai dai duk da kalaman nasa masu tsauri, Trump ya ce yana fatan kada irin wannan lamari ya faru.

Trump ya kuma bayyana cewa ci gaba da bude mashigar Hormuz na da muhimmanci ga kasashe da dama da ke dogaro da ita wajen safarar mai.

Trump ya yo addu'a a yaki da Iran
Donald J Trump, Shugaban Amurka Hoto: Getty
Source: Getty Images

Ya ce:

"Mutuwa, wuta da fushi za su mamaye su (Iran)— amma ina fata kuma ina addu’a kada hakan ya faru.”

A cewarsa, kokarin Amurka na kare zirga-zirgar mai a mashigar na da amfani ga kasashe da dama a duniya.

Trump ya ce:

“Wannan wata kyauta ce daga Amurka ga China da kuma dukkannin kasashen da ke amfani sosai da mashigar Hormuz.”

Ya kara da cewa yana fatan kasashen da ke cin gajiyar wannan hanya za su nuna godiya ga kokarin Amurka.

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya bayyana sharadi 1 tak da zai iya kawo karshen yakin Amurka da Iran

Mashigar Hormuz na daya daga cikin hanyoyin ruwa mafi muhimmanci a duniya wajen safarar mai, inda kaso mai yawa na man fetur da ake fitarwa daga yankin Gabas ta Tsakiya ke bi ta cikinta zuwa kasuwannin duniya.

Iran ta gigita Yahudawa

A baya, mun wallafa cewa Isra’ila ta fara binciken wani makami mai linzami daga Iran da ake zargin ya rabu gida-gida kafin ya fāɗi a Tel Aviv, babban birnin ƙasar

Rahotanni sun nuna makamin na iya kasancewa nau’in da ke fitar da ƙananan bama-bamai bayan ya rabu a sama, wanda Amurka, Isra'ila da Iran su ƙi da hannu kan kin samar da su.

Masu bincike na kokarin gano ko wannan alama ce ta sabon ci gaba a fasahar makaman Iran da su ke adawa da ita yayin da ake ci gaba da haɗa gwiwa ana kai mata hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng