China Ta Shata Wa Amurka da Isra'ila Layi kan Sabon Jagoran Addinin Iran, Mojtaba Khamenei

China Ta Shata Wa Amurka da Isra'ila Layi kan Sabon Jagoran Addinin Iran, Mojtaba Khamenei

  • Kasar China ta yi gargadi kan masu yunkurin farmakar sabon jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei
  • Ta bayyana cewa nadin Mojtaba domin ya gaji mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei lamari ne na cikin gida kuma bai karya dokar Iran ba
  • Wannan na zuwa ne bayan sojojin Isra'ila sun yi barazanar kai hari kan duk wanda aka nada a matsayin jagoran addinin Iran

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

China - Gwamnatin China ta yi gargadi da babbar murya kan duk wani yunkuri da Isra'ila ko Amurka za su yi na farmakar sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei.

China ta bayyana cewa nadin Mojtaba Khamenei a matsayin Jagoran Addini na Iran bayan kashe mahaifinsa lamari ne na cikin gida, tana mai adawa da duk wani yunkuri na kai masa hari.

Kara karanta wannan

Ana cikin musayar wuta, Shugaba Putin ya aika sako ga sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei

Jagoran Iran.
Sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Isra'ila ta yi barazanar farmakar Mojtaba

Tashar Al-Jazeera ta kawo rahoto cewa sojojin Isra'ila sun yi barazanar kai hari ga duk wanda zai gaji tsohon jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, wanda aka kashe a farkon hare-haren da aka kai.

A baya, shugaban Amurka Donald Trump ya raina Mojtaba Khamenei inda ya kira shi “mai rauni”, sannan ya dage cewa ya kamata ya taka rawa wajen zaben sabon jagoran Iran.

China ta yi gargadi kan jagoran Iran

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Guo Jiakun, ya shaida wa manema labarai ranar Litinin cewa nadin Mojtaba Khamenei ya yi daidai da kundin tsarin mulkin Iran.

“China na adawa da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kowace kasa, kuma dole ne a mutunta ikon Iran, tsaronta da cikakken 'yancin kasancewarta kasa,” in ji shi.

Isra’ila da Amurka na ci gaba da kai hare-hare kan Iran, yayin da Tehran ke mayar da martani da harba makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuka zuwa Isra’ila da wasu kasashen yankin Gulf da ke da sansanin sojojin Amurka.

Kara karanta wannan

Mojtaba Khamenei: Iran ta zabi sabon jagora da zai kalubalanci Trump da Isra'ila

Beijing na daya daga cikin manyan kawayen Tehran, kuma ta yi Allah-wadai da kashe Ali Khamenei, duk da cewa ta kuma soki hare-haren Iran kan kasashen Gulf, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Xi Jinping.
Shugaban kasar China, Xi Jinping da jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Lintao Zang
Source: Getty Images

China ta bukaci a tsagaita wuta

Jakadan China na yankin Gabas ta Tsakiya, Zhai Jun, ya bukaci a warware rikicin ta ruwan sanyi yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen Saudi Arabia, Faisal bin Farhan, a ranar Lahadi.

“China na kira ga dukkan bangarori da su tsagaita wuta, su dakatar da duk wani tashin hankali, kuma su kauce wa jefa mutanen yankin cikin karin wahala,” in ji Zhai Jun.

Macron ya yi magana da shugaban Iran

A baya, kun ji cewa Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya yi waya da shugaban Iran a kokarin ganin an dakatar da yakin da ya barke a karshen Fabrairun 2026.

Macron ya bukaci a bude mashigar ruwa ta Hormuz domin zirga-zirgar jiragen ruwa, sannan ya kuma nuna damuwa kan shirin nukiliyar Iran.

Hakan ya sa Macron ya zama shugaban kasa daga kasashen Yamma na farko da ya yi magana da shugaban Iran tun bayan fara yakin da Amurka da Isra'ila da Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262