Tofa: Rigima Ta Barke tsakanin Amurka da Isra'ila kan Yaki da Iran, an Ji Dalilin Sabanin
- Ana ci gaba da gwabza fada a yankin Gabas ta Tsakiya biyo bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kaddamar a kan kasar Iran
- An samu sabani tsakanin Amurka da Isra'ila sakamakon wasu hare-hare da aka kai kan Iran a ranar Asabar, 7 ga watan Maris 2026
- Amurka ta nuna damuwa kan yadda Isra'ila ta kaddamar da hare-haren duk da cewa ta sanar da ita cewa za ta kai su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Hare-haren da Isra'ila ta kai wa rumbunan adana man fetur 30 na Iran ya kawo sabani tsakaninta da Amurka.
Harin na ranar Asabar, 7 ga watan Maris 2026 ya zama sabani na farko da ya auku tsakanin Amurka da Isra'ila tun fara yaki da kasar Iran.

Source: Twitter
Tashar Axios News ta rahoto cewa hare-haren sun wuce yadda Amurka take tsammani lokacin da Isra'ila ta sanar da ita tun da fari.
An samu sabani tsakanin Isra'ila da Amurka
Wani jami'in Amurka, jami'in Isra'ila, da kuma wata majiya mai masaniya kan lamarin suka bayyana hakan.
Amurka tana fargabar cewa hare-haren Isra'ila kan kayayyakin more rayuwa da ke amfanar talakawan Iran na iya haifar da koma-baya ta fuskar dabarun yaƙi.
Ta nuna cewa hakan na iya haɗa kan al'ummar Iran don su marawa gwamnati baya da kuma tura farashin man fetur ya yi tashin gwauron zabi.
Hare-haren dakarun sojojin saman Isra'ila na ranar Asabar sun haifar da mummunar gobara a Tehran, inda harshen wuta ya dinga tashi ana ganinsa yayin da hayaki mai nauyi ya mamaye babban birnin.
Isra'ila ta fadi dalilin kai harin
Rundunar sojojin Isra'ila (IDF) ta yi iƙirarin cewa rumbunan adana man gwamnatin Iran ce ke amfani da su wajen ba wa sassa daban-daban mai, ciki har da hukumomin sojoji.
Wani jami'in sojan Isra'ila ya ce an kai hare-haren ne a matsayin wani ɓangare na gaya wa Iran ta daina kai hari kan kayayyakin more rayuwa na farar hula a Isra'ila.

Kara karanta wannan
Tofa: Ana cikin yaki da Iran, Amurka ta tsallake majalisa don faranta ran Isra'ila
Jami'an Isra'ila da na Amurka sun ce rundunar IDF ta sanar da sojojin Amurka kafin kai hare-haren. Amma wani jami'in Amurka ya ce sojin Amurka sun yi mamakin yadda hare-haren suka kazanta sosai.
Wani babban jami'in gwamnatin Amurka ya bayyana cewa:
"Ba mu yi tunanin cewa hakan kyakkyawan tunani ba ne."
Wani jami'in Isra'ila ya ce sakon Amurka zuwa ga Isra'ila shi ne na mamaki da nuna rashin amincewa.
Fadar White House da rundunar IDF ba su yi tsokaci ba.
Amurka ta nuna damuwa kan harin
Ko da yake wuraren da aka kai wa harin ba wuraren tace mai ba ne, jami'an Amurka sun damu cewa hotunan bidiyo na rumbunan adana man da ke cin wuta na iya tsoratar da kasuwannin mai da kuma tura farashin makamashi sama fiye da haka.
Wani mai ba shugaban kasar Amurka, Donald Trump shawara ya bayyana cewa:
"Shugaban kasa ba ya son harin. Yana son a adana man ne. Ba ya son a kona shi. Kuma hakan yana tunatar da mutane yadda farashin gas zai kara tashi."

Source: Facebook
Iran ta yi gargadi bayan kai harin
Tashar Aljazeera ta ce kakakin hedkwatar Khatam al-Anbiya ta Iran, wadda ke kula da ayyukan sojoji, ya yi gargaɗin cewa idan har aka ci gaba da kai wa kayayyakin man fetur na Iran hari, Tehran na iya mayar da martani da makamantan hare-hare a faɗin yankin.
Ya kara da cewa zuwa yanzu Iran ba ta hari kayayyakin man fetur da makamashi na yankin ba, kuma ya yi barazanar cewa idan har Iran ta yi hakan, farashin mai na iya kaiwa $200 kan kowace ganga.
Harin kasar Iran ya girgiza Isra'ila
A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta kai hari kan Isra'ila ta hanyar amfani da wani makami mai linzami da ke rarrabewa.
Ana zargin cewa makamin da ya zo daga Iran ya zo da sabon salo inda ya rarrabu zuwa sassa da dama kafin ya sauka a ƙasa.
Irin wannan makami na ɗauke da ƙananan bama-bamai da ke rabuwa daga babban makamin a sama, sannan su watse bayan fashewar farko.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

