Ana cikin Musayar Wuta, Shugaba Putin Ya Aika Sako ga Sabon Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei

Ana cikin Musayar Wuta, Shugaba Putin Ya Aika Sako ga Sabon Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei

  • Shugaba Viladimir Putin na kasar Rasha ya aika sakon taya murna ga sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei
  • Kasar Rasha na da kyayyawar alaka da jamhuriyar Musulunci ta Iran, kuma ana zargi tana taimaka mata a yaki da Amurka/Isra'ila
  • Putin ya jaddada goyon bayansa ga Mojtaba Khamene, yana mai cewa Rasha na tare da gwamnatin Iran a wannan lokaci na yaki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Russia - Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin ya taya Mojtaba Khamenei murnar zama sabon jagoran addini na Iran.

Shugaba Putin ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da sabon jagoranta a daidai lokacin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara tsananta.

Mojtaba Khamenei.
Jagoran addinin kasar Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaban Rasha, Vladimir Putin Hoto: Sergey Fadeichiv
Source: Getty Images

Yadda Iran ta nada magajin Ali Khamenei

Tashar Al-Jazeera ta ce Iran ta samu sauyin shugabanci ne bayan rasuwar marigayi Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya mutu a hare-haren sama da Amurka da Isra'ila suka kai makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Mojtaba Khamenei: Iran ta zabi sabon jagora da zai kalubalanci Trump da Isra'ila

Majalisar malaman addini, wadda ke da alhakin zaɓen jagoran addini, ta sanar da nadin Mojtaba Khamenei a tsakar darem ranar Litinin.

Tun da dadewa ana kallon Mojtaba Khamenei a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa, duk da cewa bai taba rike wani babban mukamin gwamnati ba.

An zaɓe shi ne a kan wasu manyan ‘yan takara da suka hada da Alireza Arafi, Mohsen Araki da kuma Hassan Khomeini, jikan wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Shugaban Rasha ya tura sako ga Mojtaba

A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar Rasha da ke Kremlin ta fitar, Putin ya bayyana cewa Mojtaba zai ci gaba da tafiyar da harkokin mulki yadda mahaifinsa ya tafi ya bari.

“Ina sake jaddada cikakken goyon bayanmu ga Tehran da kuma haɗin kanmu da abokanmu na Iran,”

- in ji Putin a sakon taya murna da ya aika wa sabon jagoran.

Ya kara da cewa shugabancin Mojtaba zai bukaci jarumtaka da sadaukarwa, musamman a lokacin da Iran ke fuskantar hare-haren yaki.

Ana zargin Rasha na taimakawa Iran

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar musayar wuta, an zabi wanda zai zama sabon jagoran addini a Iran

A wani bangare kuma, rahotanni sun nuna cewa Rasha na bai wa Iran bayanan sirri kai tsaye kan wuraren da sojojin Amurka suke a Gabas ta Tsakiya.

Rahoton Times of India ya ce wasu jami’ai uku sun bayyana cewa Moscow na tura bayanai kan wuraren da jiragen ruwan yaki, jiragen sama da sauran kayan aikin sojan Amurka suke tun bayan fara yakin.

Shugaban Rasha.
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin a fadar gwamnatinsa Hoto: Alexander Zuliana
Source: Getty Images

An ce ana iya amfani da wadannan bayanai domin taimaka wa Iran wajen kai hare-hare kan sojojin Amurka a yayin rikicin da ke gudana a yankin.

Putin ya yi magana da Shugaban Iran

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya tattauna da takwaransa na Iran, Masoud Pezeshkian ta wayar tarho bayan barkewar yaki da Amurka.

An ruwaito cewa Shugaban Iran ya gode wa Putin bisa abin da ya kira goyon bayan Rasha ga al’ummar Iran, tare da ba shi bayani kan yadda rikicin ke tafiya.

Putin ya jaddada bukatar kawo karshen faɗa a Gabas ta Tsakiya, yana mai cewa ya kamata a koma kan hanyar tattaunawa da diflomasiyya domin warware matsalar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262