Isra'ila Ta Kai Mummunan Hari Beirut, Ta Kashe Manyan Sojojin Iran 5, an Saki Sunayensu

Isra'ila Ta Kai Mummunan Hari Beirut, Ta Kashe Manyan Sojojin Iran 5, an Saki Sunayensu

  • Sojojin ruwan Isra'ila sun kashe manyan kwamandojin Iran guda biyar a wani harin hadin gwiwa da suka kai otal din Ramada dake Beirut
  • Kasar Isra'ila ta yi ikirarin cewa kwamandojin da aka kashe sun boye a cikin otal na fararen hula domin gudanar da ayyukan ta'addanci
  • Sama da mutane 150, ciki har da jami'an diflomasiyya na Iran sun fice daga Lebanon sakamakon barazanar Isra'ila na ci gaba da kashe su

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Lebanon - Rundunar tsaron Isra'ila (IDF) ta sanar a ranar Lahadi cewa ta yi nasarar kashe manyan kwamandoji biyar na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC).

Rundunar ta IDF ta ce ta hallaka wadannan manyan kwamandoji na Iran ne a wani hari da sojojin ruwanta suka kai wani dakin otal a birnin Beirut.

Kara karanta wannan

Hezbollah ta kakkabo jirgin yaƙin Isra'ila, an kashe fiye da mutane 1330 a Iran

Isra'ila ta kashe sojojin Iran a wani otel a Lebanon
An ga ma'aikatan jin kai a cikin otel din Ramada, jim kadan bayan harin Isra'ila da ya yi ajalin sojojin Iran. Hoto: Ibrahim AMRO / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Isra'ila ta kashe manyan sojojin Iran

IDF ta bayyana cewa, kwamandojin da aka kashe mambobi ne na dakarun Quds Force, reshen IRGC dake gudanar da ayyuka a kasashen waje, musamman a Palashtinu da Lebanon, in ji rahoton The Times of Israel.

Isra'ila ta bayyana cewa wadannan jami'an na boye ne a cikin wani otal na fararen hula, inda take zargin gwamnatin Iran da yin amfani da mutane a matsayin garkuwa domin gudanar da ayyukanta na ta'addanci.

Jami'an da aka kashe dai sun hada da masu kula da rarraba kudade da kuma tattara bayanan sirri domin taimaka wa kungiyoyin Hezbollah da Hamas.

Wannan hari na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Isra'ila ta yi barazanar cewa za ta farmaki dukkan jami'an Iran dake kasar Lebanon idan ba su fice ba.

Sunayen kwamandojin Iran da aka kashe

Rundunar sojin Isra'ila ta fitar da sunayen manyan dakarun Iran biyar da ta samu nasarar kawarwa a wannan harin na dare:

Kara karanta wannan

Bakin hayaki ya turnuke Tehran, Amurka ta yi wa Iran mummunar barna a karon farko

  1. Majid Hassini: Babban jami'in kudi dake da alhakin tura kudade daga Iran zuwa kungiyoyin Lebanon.
  2. Ali Reza Bi-Azar: Shugaban sashen tattara bayanan sirri na IRGC a Lebanon.
  3. Ahmad Rasouli: Shugaban sashen tattara bayanan sirri na IRGC a yankunan Palasdinu.
  4. Hossein Ahmadlou: Wani jami'in sirri a rundunar Lebanon.
  5. Abu Muhammad Ali: Wakilin Hezbollah a sashen Palasdinu na IRGC.

Halin da ake ciki a otal din Ramada

Jami'an kasar Lebanon sun tabbatar da cewa harin ya afku ne a otal din Ramada dake gabar teku, inda aka ga dakin da aka daka ya lalace baki daya, in ji rahoton France 24.

Fiye da mutane 150 daga Iran ciki har da jami'an diflomasiyya ne suka fice daga Lebanon
Jami'an ba da agajin gaggawa sun taru a otel din Ramada bayan harin Isra'ila a ranar 8 ga Maris, 2026. Hoto: IBRAHIM AMRO / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Wannan hari ya haifar da tsoro a tsakanin jami'an Iran dake kasar, inda rahotanni suka nuna cewa tuni sama da mutane 150, ciki har da jami'an diflomasiyya da iyalansu, suka fice daga Lebanon.

Isra'ila ta jaddada cewa ta yi amfani da na'urori masu hangen nesa da makaman zamani domin tabbatar da cewa ba a raunata fararen hula dake otal din ba.

Sai dai wannan sabon farmaki ya kara rura wutar yakin dake gudana tsakanin Iran da Isra'ila, wanda ya shiga rana ta 10 yau, inda ake fargabar kara tsanantar mayar da martani daga dakarun dake karkashin ikon Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta gamu da matsala, Isra'ila ta farmaki jirage sama da 15 a Tehran

Sojojin ruwan Isra'ila sun kashe manyan kwamandojin IRGC guda biyar a wani otal a Beirut. Jami'an Iran sun fara tserewa daga Lebanon sakamakon barazanar yanzu.

Hezbollah ta kakkabo jirgin Isra'ila

A wani labari, mun ruwaito cewa, Hezbollah ta kakkabo jirgin yakin Isra'ila yayin da dakarun commando suka yi kokarin mamaye garin Nabi Sheet Harin.

Hezbollah ta bayyana cewa ta gano "shigar kusan jirage masu saukar ungulu 15 na abokan gaba" daga ɓangaren iyakar Siriya zuwa gabashin Lebanon.

Akalla mutane 1,332 ne suka riga mu gidan gaskiya a Iran sakamakon hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra'ila da ya shiga rana ta 10.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com