Saudiyya Ta Ja Kunnen Iran, Ta Faɗi Illar Rikita Gabas ta Tsakiya

Saudiyya Ta Ja Kunnen Iran, Ta Faɗi Illar Rikita Gabas ta Tsakiya

  • Ƙasar Saudiyya ta zargi Iran da kai hare-hare kan muhimman wuraren fararen hula a yankin Gulf da sunan ramuwa
  • Gwamnatin Riyadh ta karyata zargin Tehran cewa jiragen yaki sun tashi daga Saudiyya domin kai hari
  • Ta yi gargadin cewa Iran ce za ta fi kowa hasara idan rikicin ya kara kamari kuma aka ci gaba da kai mata hari

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Saudi Arabia – Kasar Saudiyya ta bayyana cewa Iran za ta kasance mafi girman mai asara idan har hare-haren da ake kai wa kasashen yankin Gulf suka ci gaba.

Wannan na daga cikin kalaman da Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta yayin da yakin da Isra'ila da Iran suka jawo ya shiga kwana na 10.

Kara karanta wannan

Iran ta fusata, ta kai hare hare Dubai, Saudiyya, mutane sun mutu

Saudiyya ta gargaɗi Iran
Yariman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed bin Salman Hoto: @insharifain
Source: Twitter

Al-Jazeera ta ruwaito Ma’aikata ta yi Allah-wadai da hare-haren da ta kira na rashin tausayi da ake zargin Iran da kai wa Saudiyya da wasu kasashen Larabawa da na Musulmi.

Saudiyya ta zargi Iran da kai hare-hare

Arab News ta wallafa cewar ma’aikatar ta ce hare-haren da aka kai kan wuraren fararen hula sun hada da filayen jiragen sama da wuraren samar da mai, lamarin da ta ce barazana ce ga tsaro da zaman lafiyar yankin.

Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta bayyana cewa hare-haren da aka kai kan muhimman wuraren jama’a sun saba wa dokokin kasa da kasa.

Sanarwar ta ce irin wadannan hare-hare na nuna niyyar tada zaune tsaye a yankin tare da kawo cikas ga zaman lafiyar Gabas ta Tsakiya.

Saudiyya ta ce Iran za ta fi yawan asara a yakin da Amurka da Isra'ila suka jawo
Shugaban Amurka, Donald J Trump Hoto: Getty
Source: Getty Images

Ta kara da cewa kai hari kan wuraren jama’a, musamman filayen jiragen sama da cibiyoyin man fetur, ya sabawa yarjejeniyoyin kasa da kasa da dokokin da suka shafi kare rayukan fararen hula.

Kara karanta wannan

Lamari ya rincabe: Saudiyya ta gaji da shiru, ta gargadi Iran kan hare-harenta

Gwamnatin Saudiyya ta ce wadannan hare-hare ba su nuna komai ba face yunkurin barazana ga tsaro da kwanciyar hankali a yankin Gulf.

Za a iya samun tashin hankali - Saudiyya

Haka kuma Ma'aikatar ta ce irin wadannan matakai na iya haddasa karin tashin hankali da kuma kara dagula alakar kasashen yankin.

A bangare guda kuma, Saudiyya ta yi watsi da zargin da Tehran ta yi cewa Riyadh ta bari jiragen yakin kasashen waje su tashi daga kasarta domin kai hari a yakin da ake yi.

Ma’aikatar harkokin wajen Saudiyya ta bayyana wannan zargi a matsayin karya, tana mai cewa jiragen da ake magana a kansu suna gudanar da sintiri ne kawai.

Suna bin sararin samaniya domin kare sararin samaniyar Saudiyya da na kasashen kungiyar Gulf daga makamai masu linzami da jiragen marasa matuka.

Saudiyya ta yi gargadin cewa ci gaba da kai hare-haren da ake zargin Iran da yi na nufin kara dagula rikicin da ake fuskanta a yankin.

Sanarwar ta ce irin wannan mataki zai yi tasiri mai zurfi ga alakar da ke tsakanin Iran da kasashen yankin a yanzu da kuma nan gaba.

Kara karanta wannan

Iran ta gargaɗi Amurka, ta faɗi abin da zai faru da jiragen da Trump zai tura Hormuz

Ta ce:

“Mun jaddada cewa matakan da Iran ke dauka a halin yanzu ba su nuna hikima ba, kuma ba su nuna cewa tana son kaucewa kara fadada rikicin ba."

Ta kara da cewa idan aka ci gaba da irin wannan yanayi na tashin hankali, to Iran ce za ta fi kowa yin hasara a sakamakon fadada rikicin.

Amurka ta ja layi da jagoran Iran

A baya, mun wallafa cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sabon jagoran Iran ba zai daɗe a mulki ba idan bai samu amincewar ƙasarsa ba.

Donald Trump ya yi zargin cewa Iran na shirin mamaye Gabas ta Tsakiya baki ɗaya yayin da ƙasarsa da Isra'ila suka fara kai mata hari a makon jiya.

Shugaban ya kuma ce Amurka ba ta cire yiwuwar tura sojojin musamman domin kwace sinadarin uranium da ya dade yana tsone masu ido saboda batun nukiliya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng