Bakin Hayaki Ya Turnuke Tehran, Amurka Ta Yi wa Iran Mummunar Barna a Karfon Farko
- Amurka da Isra'ila sun farmaki rumbunan man fetur na Iran a karon farko inda aka kashe ma'aikata hudu tare da haddasa gobara
- Benjamin Netanyahu ya lashi takobin ci gaba da kai farmaki kan shugabannin Iran ba tare da jin kai ba domin ruguza tsarin mulkin kasar
- Zuwa yau, yaƙin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 1,300 a Iran, 300 sun mutu a Lebanon, sannan wasu mutane 12 sun mutu a Isra'ila
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Iran - A rana ta tara da kaddamar da gagarumin yaƙi kan ƙasar Iran, haɗaƙar dakarun Amurka da Isra'ila sun kaddamar da munanan hare-hare ta sama waɗanda suka taba rumbunan adana man fetur na Tehran a karon farko.
Wannan farmaki ya haddasa tashin baƙin hayaki da ya turnuke sararin samaniyar birnin Tehran, inda warin danyen mai dake cin wuta ya mamaye ko'ina.

Source: Getty Images
Amurka/Isra'ila sun tafka barna a Iran
Kamfanin rarraba man fetur na Iran ya tabbatar da cewa ma'aikatansa guda huɗu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon wannan harin, in ji rahoton Reuters.
Hare-haren na ranar Lahadi sun shafi rumbunan mai guda huɗu da kuma cibiyar tura mai dake Tehran da lardin Alborz.
Daga cikin wuraren da aka daka akwai rumbun mai na Aghdasieh, matatar mai ta Tehran, da rumbun mai na Shahran, inda shaidu suka bayyana cewa man fetur ya malala har zuwa kan tituna.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta daki waɗannan wurare ne domin ana amfani da su wajen tura wa dakarun soja makamashi, yayin da kafafen yaɗa labaran Iran suka bayyana harin a matsayin "ta'addancin Amurka.".
Netanyahu: "Ba sauran jin kai ga Iran"
Jim kaɗan bayan hare-haren, Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fitar da wani saƙon bidiyo inda ya lashi takobin ci gaba da kai farmaki kan shugabannin Iran "ba tare da jin ƙai ba".
Netanyahu ya bayyana cewa suna da tsari na musamman mai cike da "abubuwan mamaki" domin ruguza tsarin mulkin Iran da kuma samar da canji.
Ya ƙara da cewa akwai sauran wurare da dama da suke shirin farmaka nan gaba kaɗan, cewar rahoton jaridar The Times of Israel.

Source: Getty Images
Adadin mutanen da suka mutu a Iran
Duk da barnar da aka yi, hukumomin Iran sun bayyana cewa babu matsalar rarraba mai a cikin ƙasar, kuma jami'an kashe gobara suna ci gaba da ƙoƙarin shawo kan wutar.
Zuwa yau, yaƙin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 1,300 a Iran, yayin da mutane 300 suka mutu a Lebanon, sannan wasu mutane kusan 12 suka mutu a Isra'ila.
Masu sharhi na ganin wannan hari kan ma'aikatun man fetur a matsayin wani ɓangare na "yaƙin sunkuru" domin tsoratar da ƴan ƙasar Iran.
Abin da zai kawo karshen yakin Amurka da Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Donald Trump, ya ce yaƙin Gabas ta Tsakiya na iya ƙarewa ne kawai idan aka rusa shugabancin Iran.

Kara karanta wannan
An nemi Na'ibin limami da wasu mazauna Katsina an rasa bayan hare haren yan ta'adda
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce wasu ƙasashe sun fara ƙoƙarin shiga tsakani domin sasanta rikicin, amma Trump ya nuna baya so.
Rikicin ya ƙara tsananta yayin da hare-haren Amurka da Isra’ila suka jawo asarar rayuka da lalacewar kayayyaki.
Asali: Legit.ng

