Switzerland Ta Tsoma Baki a Yakin da Isra'ila da Amurka Suka Ƙaddamar a kan Iran
- Ministan tsaron Switzerland ya ce hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran sun karya dokokin ƙasa da ƙasa
- Gwamnatin Switzerland ta bayyana cewa irin waɗannan hare-hare sun saɓa da dokar hana amfani da ƙarfi tsakanin ƙasashe
- Wasu manyan jami’an Turai da masana sun nuna shakku kan halaccin wannan yaƙi a dokokin duniya bayan Isra'ila da Amurka sun haɗa kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Switzerland – Martin Pfister, ministan tsaron ƙasar Switzerland, ya bayyana cewa hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai kan Iran sun saba da dokokin ƙasa da ƙasa.
Pfister ya ce majalisar ministocin ƙasar Switzerland ta yi nazari kan lamarin kuma ta yanke shawarar cewa irin waɗannan hare-hare sun keta dokokin duniya.

Source: Twitter
Al-Jazeera ta wallafa cewa Ministan ya bayyana takaici game da yada aka fara wannan yaƙi tun farko ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan
"Na ga ana kuka"; Malamin addini ya yi hasashen wanda zai yi nasara a yakin Iran da Amurka
Martanin Switzerland ga yakin Amurka, Isra'ila da Iran
Reuters ta wallafa cewa Ministan ya ƙara da cewa irin wannan mataki ya saɓa da ƙa’idar da ke hana amfani da ƙarfi tsakanin ƙasashe a harkokin hulɗar duniya.
Pfister ya ce:
“Ra’ayin majalisar gwamnatin tarayya shi ne cewa harin da aka kai kan Iran ya zama karya dokokin ƙasa da ƙasa.”
A cewarsa, duk wani ɓangare da ke da hannu a rikicin ya kamata ya dakatar da faɗa domin kare rayukan fararen hula da ba su da hannu a yaƙi. Pfister ya kuma bayyana cewa kalamansa ba wai ga ƙasa ɗaya kawai ba ne, domin ya ce duk wata ƙasa da ta saɓa da dokar hana amfani da ƙarfi ta karya dokokin ƙasa da ƙasa. Ya ce:
“Amurkawa da Isra’ila sun kai hari kan Iran ta sama. Ta wannan mataki, su ma kamar Iran sun karya dokokin ƙasa da ƙasa.”
An damu kan yakin Amurka da Iran
Kalaman ministan tsaron Switzerland sun yi kama da na mataimakin firaministan ƙasar Germany, Lars Klingbeil, wanda ya nuna shakku kan halaccin yaƙin a mahangar dokokin duniya.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ana tsaka da yaki da Iran, 'dan Majalisar Amurka ya dauko batun Najeriya

Source: Getty Images
Lars Kingbeil ya ce yana da shakku mai girma a kan ko wannan yaƙi ya dace da dokokin ƙasa da ƙasa.
Ya kuma yi gargaɗin cewa akwai babbar barazana ga tsarin duniya idan ƙasashe suka fara yin abubuwa ba tare da bin ƙa’ida ba.
A cewarsa, akwai haɗarin cewa duniya na iya shiga wani yanayi da dokoki ba za su ƙara aiki ba, inda ƙarfi kawai zai zama abin da ake bi.
Haka kuma, ƙasar Spain ta fito ta yi Allah-wadai da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, inda ta bayyana su a matsayin mataki mai haɗari da kuma wanda ya saɓa da doka.
Iran ta gargadi Amurka
A bayan mun wallafa cewa kasar Iran ta yi gargaɗi cewa duk jirgin ruwan Amurka da ya shiga Tekun Gulf zai iya nutsewa domin ba za ta lamunci keta alfarmarta ba.
Rundunar sojojin ruwa na Amurka ya ce za su fara raka jiragen mai a mashigar Hormuz bayan Iran ta rufe hanyar yayin da yaki ke ƙara ƙazanta a tsakanin ƙasashen.
Iran ta ce matukar Amurka ta cika wannan iƙirarin da ta yi, za ta tsinci jiragen ruwan da a ta aika da wadanda za ta raka su wuce ta hanyar Hormuz za su tsinci kansu a kasan teku.
Asali: Legit.ng