IRAN Ta Gargaɗi Amurka, Ta Faɗi abin da zai Faru da Jiragen da Trump zai Tura Hormuz

IRAN Ta Gargaɗi Amurka, Ta Faɗi abin da zai Faru da Jiragen da Trump zai Tura Hormuz

  • Kasar Iran ta yi gargaɗi cewa duk jirgin ruwan Amurka da ya shiga Tekun Gulf zai iya nutsewa domin ba za ta lamunta ba
  • Shugaban sojojin ruwa na Amurka ya ce za su fara raka jiragen mai a mashigar Hormuz bayan Iran ta rufe hanyar
  • Ministan harkokin wajen Iran ya zargi Amurka da kai hari kan cibiyar tace ruwan sha a tsibirin Qeshm

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kasar Iran – Rundunar sojin Iran ta yi martani ga ikirarin Amurka na cewa za ta fara raka jjiragen mai su wuce ta Hormuz da ta rufe.

Iran ta yi gargaɗi cewa duk wani jirgin ruwan Amurka da ya shiga 'Gulf' zai iya gamuwa da mummunar kaddara, inda ya ce zai iya nutsewa har ƙasan teku.

Kara karanta wannan

Ba sauki: Iran ta kai hari mai zafi kan sansanin sojojin Amurka

Iran ta ce ba za ta sassauta wa Amurka ba
Shugaba Masoud Pezeshkian yana jawabi a yayin wani taro Hoto: Getty
Source: Getty Images

Aljazeera ta wallafa cewa rahotanni sun ce rundunar ta bayyana hakan ne yayin da rikicin siyasa da na tsaro ke ƙara tsananta tsakanin Iran da Amurka.

Iran ta nemi Amurka ta shiga taitayinta

ETV Bharat ta wallafa cewa wani babban jami’in sojan Iran ya bayyana cewa sun shirya kare kasarsu daga duk wani abu da za a ɗauka a matsayin barazana ga tsaro.

A cewarsa, duk wani yunƙuri na matsa wa Iran lamba ta hanyar amfani da karfin soja na iya janyo sakamako mai tsanani.

Wannan gargaɗi na Iran ya zo ne bayan tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya ce rundunar sojin ruwansu za ta fara rakiyar jiragen dakon mai da ke wucewa ta mashigar Hormuz.

Trump ya ce wannan shiri zai fara aiki cikin gaggawa domin kare zirga-zirgar jiragen mai a yankin da Iran ta rufe.

Muhimmancin Hormuz da Iran ta rufe

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran

Mashigar Hormuz na daga cikin manyan hanyoyin da ake jigilar man fetur a duniya, inda kasashe da dama ke amfani da ita wajen fitar da mai zuwa kasuwannin duniya.

Amurka ta yi ikirarin fara wucewa ta Hormuz
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Twitter

Saboda haka duk wani rikici a yankin na iya shafar kasuwancin man fetur da kuma tattalin arzikin duniya.

A wani sabon zargi kuma, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Amurka ta kai hari kan wata cibiyar tace ruwan sha da ke tsibirin Qeshm a tekun Gulf.

Ya bayyana cewa harin ya janyo matsala ga samar da ruwa ga kauyuka da dama a yankin.

Ministan ya ƙara da cewa harin ya shafi samar da ruwan sha ga kimanin ƙauyuka 30 da ke yankin.

Ya kuma yi gargaɗi cewa kai hari kan muhimman kayayyakin more rayuwa na ƙasa kamar cibiyoyin ruwa na iya haifar da sakamako mai tsanani.

A cewarsa, wannan lamari ya nuna wani sabon mataki a rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka, inda ya ce Amurka ce ta fara ɗaukar irin wannan matakin, ba Iran ba.

An kai karar Iran Majalisar dinkin duniya

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya bayyana sharadi 1 tak da zai iya kawo karshen yakin Amurka da Iran

A wani labarin kun ji cewa Qatar ta tura wasiku biyu zuwa Majalisar Dinkin Duniya kan hare-haren da Iran ta kai kasarta musamman wurin da fararen hula ke zaune.

Wakiliyar Qatar a Majalisar Dinkin Duniya ce ta mika wasikun, wadanda ke kunshe da korafin kasarta kan rikicin da ya barke tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila a makon da ya gabata.

Ta yi ikirarin cewa Iran ta harba makamai masu linzami 83 da jirage marasa matuƙi 12 zuwa Qatar tun bayan fara yakin a ranar Asabar 6 ga watan Fabrairu, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng