An Kai Wa Amurka Dauki da Kasar Iran Ta Matsa da Kai Hare Hare da Makamai Masu Hadari

An Kai Wa Amurka Dauki da Kasar Iran Ta Matsa da Kai Hare Hare da Makamai Masu Hadari

  • Amurka ta fara amfani da sansanonin soji guda biyu na kasar Birtaniya domin kare kanta daga hare-haren Iran a Gabas ta Tsakiya
  • Hakan na zuwa ne yayin da aka shiga rana da takwas da fara musayar wuta tsakanin Amurka/Isra'ila da kuma Iran
  • Da farko Birtaniya ba ta yi niyyar shiga wannan yaki ba, amma daga bisani ta amince da bukatar Amurka na amfani da wasu sansanoninta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United Kingdom - Amurka ta fara amfani da wasu sansanonin soja na kasar Birtaniya domin kare kanta daga hare-hare a yaƙin da ake yi da Iran a Gabas ta Tsakiya.

Ma’aikatar tsaron Birtaniya ta sanar a ranar Asabar cewa Amurka ta fara amfani da wadannan wuraren domin ayyukan kariya na musamman da nufin hana Iran harba makamai masu linzami zuwa wasu ƙasashen yankin.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta farmaki wani jirgin yaki, ta kara yi wa Amurka da Isra'ila babbar illa

Amurka.
Jirgin sojojin Amurka lokacin da ya sauka a daya daga cikin sansanonin sojin Birtaniya Hoto: Christopher Furlong
Source: Getty Images

Birtaniya ta kai wa Amurka dauki

Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa gwamnatin Birtaniya ta amince Amurka ta yi amfani da sansanonin soji guda biyu, da suka hada da RAF Fairford da kuma Naval Support Facility Diego Garcia.

A safiyar yau Asabar, 7 ga watan Maris, 2026 aka ga wani jirgin yaƙin Amurka samfurin B-1 Lancer ya sauka a sansanin Fairford.

Haka kuma an ga jirgin jigilar kaya na Amurka C-5 Galaxy a kan titin saukar jiragen sama na sansanin.

Rikici tsakanin Amurka da Birtaniya

Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya janye tare da kin shiga kai tsaye a yaƙin da Shugaba Donald Trump na Amurka da Isra’ila suka fara da Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Wannan matakin ya fusata Shugaba Trump, wanda ya ce “bai ji dadin wannan matsaya ta Birtaniya ba”, har ma ya yi wa Starmer shagube da cewa, “Ba Winston Churchill, muke hulɗa da shi ba.”

Kara karanta wannan

Iran ta ce ta kashe sojojin Amurka 500 a luguden wuta da ta masu

Daga baya Starmer ya amince da bukatar Amurka, amma ya ce Birtaniya ta ba kasar izinin amfanin da sansanonin domin kariya kawai.

Starmer ya bayyana cewa dole ne kowanne matakin da Birtaniya za ta ɗauka ya kasance bai saba wa doka ba kuma yana da tsari mai kyau.

Makaman Iran.
Daga cikin makaman da Iran ke harba wa a yakinta da Amurka da Isra'ila Hoto: Jaafar Hamad
Source: Twitter

Birtaniya ta taimaki Amurka a yakin Iran

Amma daga baya ya sauya ra’ayi bayan Iran ta fara mayar da martani da makamai masu linzami da jirage marasa matuƙi kan Amurka da kawayenta a yankin.

Ya ce wannan martani na Iran yana barazana ga muradun Birtaniya da abokan kawancenta a Gabas ta Tsakiya.

Wani binciken ra’ayin jama’a da aka yi kan mutane 1,045 a Birtaniya ya nuna cewa 56% sun ce Starmer ya yi daidai da farko da ya ƙi shiga yaƙin yayin da 27% kawai suka ce ya yi kuskure

Wannan na nuna cewa yawancin ‘yan Birtaniya ba sa son ƙasarsu ta shiga yaƙin kai tsaye, kamar yadda RFI ta rahoto.

Amurka ta sayar da makamai ga Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Amurka karkashin Donald Trump ta amince da yiwuwar sayar wa Isra'ila makaman da darajarsu ta kai $151.8m.

Kara karanta wannan

Sanatocin Amurka sun kada kuri'a kan hana Trump cigaba da yaki da Iran

Amurka ta yi amfani da ikon "gaggawa" domin kauce wa bukatar amincewar majalisa yayin da Washington da Tel-Aviv ke ci gaba da kai hare-hare kan Iran.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ofishin harkokin siyasa da soja na ma'aikatar wajen Amurka ya fitar ranar Juma'a, 6 ga watan Maris 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262