Iran Ta Jawo wa Amurka Asarar Miliyoyin Daloli, Ta Lalata Na’urar Kare Makamanta

Iran Ta Jawo wa Amurka Asarar Miliyoyin Daloli, Ta Lalata Na’urar Kare Makamanta

  • Rahotanni sun ce Iran ta lalata wata na’ura mai kare makamai mallakin Amurka mai darajar miliyoyin daloli a wani sansanin soja a Jordan
  • Masana tsaro sun ce lalata radar din THAAD zai iya barin gibin sa ido kan makamai masu linzami a yankin Gulf, lamarin da ka iya shafar tsarin kariya
  • Hotunan tauraron dan adam sun nuna an lalata radar AN/TPY-2 a sansanin Muwaffaq Salti, abin da masana ke cewa na daga cikin manyan hare-haren Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Tehran, Iran - Rahotanni sun ce kasar Iran ta lalata wata na’urar da take kare makamai mallakin Amurka a farkon kwanakin yakin da ke gudana a yankin Gabas ta Tsakiya.

An ce na'urar, AN/TPY-2 mai darajar dala miliyan 300 na cikin tsarin kare makamai na THAAD da Amurka ke amfani da shi domin gano makamai masu linzami daga nesa.

Iran ta sake illata Amurka a Jordan
Cibiyar na'urar kare makaman Amurka a Jordan da marigayi Ali Khamenei. Hoto: @khameneni_ir, AP.
Source: UGC

Hotunan tauraron dan adam sun nuna cewa an lalata cibiyar tare da wasu kayan tallafi a sansanin sojin sama na Muwaffaq Salti da ke Jordan, cewar TRT World.

Kara karanta wannan

Yakin Amurka/Isra'ila da Iran: Muhimman abubuwan da suka faru a rana ta 5

Iran ta lalata wata cibiyar Amurka a Jordan

Wani jami’in Amurka ya tabbatar da lalacewar na’urar, bayan rahotanni sun ce Iran ta kai hare-hare biyu a Jordan a ranakun 28 ga Fabrairu da 3 ga Maris.

Masana tsaro sun ce lalata cibiyar na iya haifar da babban gibi wajen sa ido kan makamai masu linzami a sararin sama.

Wani masani, Ryan Brobst, ya ce idan harin ya yi nasara, zai kasance daya daga cikin hare-haren Iran mafi tasiri tun bayan fara yakin, cewar The Business Standard.

Sai dai ya kara da cewa sojojin Amurka da abokan kawancensu suna da wasu cibiyoyi da za su iya ci gaba da samar da kariya daga hare-haren makamai.

An lalata cibiyar kare makaman Amurka a Jordan
Shugaba Donald Trump yayin kamfe a New York. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Yadda Iran ke jawo wa Amurka asara

Rahotanni sun ce yanzu tsarin kare sararin samaniya zai fi dogaro da makaman Patriot saboda cibiyar na THAAD ya lalace saboda harin da Isra'ila ta kai ya yi mata illa sosai.

Wannan lamari na zuwa ne bayan wata cibiyar mallakin Amurka a kasar Qatar ma ta samu lalacewa a wani hari da Iran ta kai a baya yayin da ake ci gaba da yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa

Masana sun ce hare-haren da aka kai a Jordan, Qatar da kuma wasu wurare na nuna kokarin Iran na lalata manyan na’urorin sa ido na tsaron yankin Gulf da ke fama da yake-yake a yanzu.

Iran ta yi wa Amurka da Isra'ila babbar illa

Kun ji cewa rundunar juyin juya hali ta Iran ta kai farmaki kan wani jirgin yaki kirar F-15E na Amurka yayin da aka shiga rana ta bakwai da fara musayar wuta.

Sojojin IRGC sun sanar da kaddamar da zayage na 22 na hare-haren kare kai da ramuwar gayya da suke kai wa kan kayayyakin Amurka da Isra'ila.

Gwamnatin Iran dai ta sha nanata cewa ba gudu ba ja da baya a wannan yaki, inda ta ce ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarin kare kanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.