Bayan Kwanaki 7, Iran Ta Sauya Salon Yaki da Amurka, Ta Sassautawa Larabawa

Bayan Kwanaki 7, Iran Ta Sauya Salon Yaki da Amurka, Ta Sassautawa Larabawa

  • Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya yi bayani game da salon yakin da za su cigaba da yi bayan mako suna fafatawa da Amurka da Isra'ila
  • Pezeshkian ya bayyana cewa kasashen Larabawa za su samu sassauci matukar ba su hada kai da Amurka ko Isra'ila an kai musu hari ba
  • Ya kuma bukaci hada kai da kasashen Musulmi domin tabbatar da zaman lafiya da kawo kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya baki daya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Yakin da ake yi tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila zai dauki sabon salo yayin da hare-haren Tehran za su mayar da hankali kan Tel Aviv kadai.

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya ce Majalisar rikon kwarya ta amince cewa ba za a ƙara kai hari kan ƙasashen maƙwabta ba, sai dai idan an kai nusu hari daga waɗannan ƙasashen.

Kara karanta wannan

Shugaba Trump ya bayyana sharadi 1 tak da zai iya kawo karshen yakin Amurka da Iran

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian
Shugaba Masoud Pezeshkian yayin wani jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton da Al-Jazeera ta wallafa ya nuna cewa shugaban ya kuma ba da haƙuri ga ƙasashen maƙwabta saboda hare-haren da suka faru a kwanakin baya.

Jawabin Shugaban Iran kan rikicin Amurka/Isra'ila

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ba da haƙuri ga ƙasashen Larabawa na yankin Gulf a wani jawabi da ya yi da safiyar Asabar, 7 ga watan Maris 2026, yana mai cewa Tehran za ta daina kai musu hari.

“Ni da kaina ina ba da haƙuri ga ƙasashen maƙwabta da Iran ta kai wa hari,”

- Inji shi a wani jawabi da aka watsa a talabijin na gwamnati.

CNN ta wallafa cewa ya ce:

“Ba mu da niyyar kai hari ga ƙasashen maƙwabta. Kamar yadda na sha faɗa, su ’yan’uwanmu ne.”

Ya ƙara da cewa majalisar shugabanci ta mutum uku da ke rike da mulkin Iran na ɗan lokaci ta:

“Umarci sojoji cewa daga yanzu kada a kai hari ga ƙasashen maƙwabta ko a harba makamai masu linzami sai dai idan za a kai mana hari daga waɗannan ƙasashen.”

Kara karanta wannan

Tofa: Trump ya koma neman taimako da Iran ta jefa makamai kan kadarorin Amurka

“Na yi imani ya kamata mu warware wannan ta hanyar diflomasiyya maimakon yaƙi da kuma samun matsala da ƙasashen maƙwabta,”

- Inji shugaban Iran

Ƙasashen Larabawa sun sake fuskantar hari

Saudi Arabia, Qatar, Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun fuskanci sababbin hare-hare na jiragen yaƙi marasa matuƙa da makamai masu linzami a yau Asabar.

Filin jirgin saman Dubai da yake daga cikin mafi cunkoso a duniya ya fuskanci hare-hare da dama, inda fasinjoji suka ce sun ji saukar makamai aƙalla sau ɗaya, yayin da aka tare wasu daga sama.

Filin jirgin saman Dubai
Jirage a filin jirgin saman Dubai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoto ya nuna cewa an dakatar da tashi da saukar jiragen sama na wasu sa’o’i, amma ana sa ran za a ci gaba daga baya a yau Asabar, 7 ga Maris, 2026.

Iran: Kasar Saudi ta zauna da Pakistan

A wani labarin, kun ji cewa Ministan tsaron Saudiyya, Khalid bin Salman ya gana da shugaban rundunar sojin Pakistan game da hare-haren Iran.

Ministan ya bayyana cewa sun tattauna batutuwan da suka shafi inganta tsaro a Gabas ta Tsakiya da yadda za a magance hare-haren Iran a Riyadh.

Tun a shekarar 2025 Saudiyya da Pakistan da ta mallaki makaman nukiliya suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro a tsakaninsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng