Iran Ta Yi Wa Amurka Gagarumar Barna, Trump Zai Halarci Karbar Wadanda Aka Kashe

Iran Ta Yi Wa Amurka Gagarumar Barna, Trump Zai Halarci Karbar Wadanda Aka Kashe

  • Shugaba Donald Trump na Amurka zai halarci bikin karbar gawarwakin sojoji shida da Iran ta kashe a kasar Kuwait
  • Fadar White House ta tabbatar da cewa Trump zai halarci wannan taro, wanda za a gudanar a sansanin sojojin sama na Dover da ke Amurka
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da musayar wuta tsakanin Amurka/Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

America - Shugaban Amurka, Donald Trump, zai halarci bikin karɓar gawarwakin sojojin Amurka shida da suka mutu a wani harin da Iran ta kai a ƙasar Kuwait.

Fadar gwamnatin Amurka da aka fi sani da White House ce ta sanar da hakan a ranar Juma’a, 6 ga watan Maris, 2026.

Trump.
Shugaban Amurka, Donald J. Trump a fadar White House da ke birnin Washington DC Hoto: Donald J Trump
Source: Getty Images

Yadda Iran ta kashe sojojin Amurka

Rahotan tashar Al-Jazeera ya ce sojojin sun mutu ne ranar Lahadi bayan wani jirgin sama maras matuƙi ya kai hari kan sansanin sojojin Amurka da ke tashar masana’antu ta Port Shuaiba a kudancin Kuwait.

Kara karanta wannan

Tana tsakiyar karbar wuta daga Amurka, Iran ta samu taimako daga kasar Indiya

Harin ya faru ne kwana guda bayan da Amurka da Isra'la suka kaddamar da babban farmakin soja kan Iran.

Za a gudanar da bikin karbar gawarwakin ne a sansanin sojin sama na Dover Air Force da ke Amurka, domin karrama sojojin kamar yadda aka saba.

Amurka za ta karbi gawawwakin sojojinta

Sojojin da suka rasu, maza biyar da mace guda, masu shekaru tsakanin 20 zuwa 54 duk suna aiki ne a rundunar 103rd Sustainment Command, wacce ke kula da samar wa sojoji abinci, man fetur, kayan aiki da alburusai.

A yayin bikin, ana sauke akwatunan gawarwakin sojojin, waɗanda aka rufe da tutar Amurka, daga jirgin sama, inda wasu abokan aikinsu a wannan runduna za su yi masu rakiya.

Daga nan kuma ana kai su zuwa cibiyar binciken gawarwaki ta rundunar sojoji domin tantancewa da shirya su don jana’iza, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Dalilin halartar shugaba Trump

Mai magana da yawun fadar White House, Karoline Leavitt, ta ce Shugaba Trump zai je sansanin Joint Base Dover domin halartar bikin da nufin girmama sojojin shida da suka mutu.

Kara karanta wannan

Yaki na kara zafi, Trump ya ja da baya, ya ki tura sojoji Iran

Harin da ya kashe sojojin ya nuna irin haɗarin da ke fuskantar sojojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya yayin da rikicin Amurka da Iran ke ƙara tsananta.

Sojoji.
Jami'an rundunar sojojin sama ta kasar Amurka a bakin aiki Hoto: Christopher Furlong
Source: Getty Images

Jami’an Amurka sun kuma yi gargadin cewa yaƙin na iya ƙara tsananta a kwanaki masu zuwa, yayin da Iran ke ci gaba da harba jirage marasa matuƙi da makamai masu linzami kan wuraren Amurka da kawayenta a yankin.

Sojojin Iran sun kara rikita Amurka/Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa rundunar juyin juya hali ta Iran ta kai farmaki kan wani jirgin yaki kirar F-15E na Amurka yayin da nusayr wuta tsakanin kasashen ke iara kamari.

Dakarun IRGC sun bayyana haka ne yayin da suke bayani kan hare-haren makamai masu linzami, zagaye na 22, da suka kaddamar kan Amurka da Isra'ila.

Sojojin na Iran sun kuma bayyana cewa sun harbo wani jirgin sama maras matuƙi na Isra'ila mai suna Heron drone, wanda ke shawagi a birnin Isfahan da ke tsakiyar ƙasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262