Tofa: Trump Ya Koma Neman Taimako da Iran Ta Jefa Makamai kan Kadarorin Amurka

Tofa: Trump Ya Koma Neman Taimako da Iran Ta Jefa Makamai kan Kadarorin Amurka

  • Gwamnatin Donald Trump ta nemi taimakon Ukraine don amfani da kwarewarsu wajen kakkabo jiragen Iran dake addabar kasashen Gulf
  • Volodymyr Zelensky ya amince da bukatar amma da sharadin Amurka za ta ba Ukraine na'urorin kariya na Patriot domin yaki da Rasha
  • Kasashen duniya na fargabar wannan sabon yakin zai dauke hankalin Ukraine yayin da Rasha ke samun kudin shiga daga tashin mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ukraine - Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya bayyana cewa gwamnatin Amurka ta nemi taimakon ƙasarsa a yaƙin da take yi da Iran.

Zelensky ya ce Shugaba Donald Trump na son Ukraine ta taimaka masa don kare ƙasashen da ke ƙawance da Amurka a yankin Gulf daga hare-haren jiragen Iran.

Trump ya nemi taimakon Ukraine a yaki da Iran
Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky na musabaha yayin wani taron manema labarai a Florida. Hoto: Jim WATSON / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Amurka ta nemi taimakon Ukraine

Kara karanta wannan

Rasha ta fadi dalilin da ya sa ba ta kai dauki ga Iran ba a yakinta da Isra'ila

Ya bayyana cewa abokan hulɗarsu na ƙasashen duniya, musamman Amurka, sun mika buƙatar samun gogewar Ukraine wajen kakkabo jiragen Shahed waɗanda Iran ke, in ji rahoton BBC.

A yayin da yaƙin Gabas ta Tsakiya ke ƙara ruruwa, Zelensky ya ba da umarnin tura ƙwararru da kayan aiki zuwa yankin domin tabbatar da ba Amurka gudunmawa.

Shugaban na Ukraine ya bayyana cewa duk wanda ya taɓa fuskantar harin Iran ya san cewa jiragen Shahed suna da wuyar kakkabowa ba, har sai an samu ƙwarewa da makaman da suka dace.

Ukraine ta kwashe shekaru tana fuskantar hare haren waɗannan jirage waɗanda Rasha ke amfani da su, wanda hakan ya ba su ƙwarewar da duniya ke buƙata a halin yanzu.

Sharuɗɗan Ukraine da martanin Trump

Zelensky ya tuntuɓi shugabannin ƙasashen Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Qatar, Bahrain, Jordan, da Kuwait domin yi musu alkawarin matakai na zahiri wajen kare sansanonin soji da gine-ginen fararen hula.

Duk da wannan tayi, Zelensky ya gindaya sharuɗɗa cewa wannan taimako ba zai rage ƙarfin kariya na ƙasarsa ba, sannan dole ne Ukraine ta samu moriyar diflomasiyya.

Kara karanta wannan

Adadin mutanen da aka kashe a Iran, Isra'ila da kasashe 7, Amurka ta rasa sojoji 6

Ya ba da shawarar musayar jiragen kakkabo jirage marar matuka da na'urar kariya ta Patriot daga Amurka domin kare Ukraine daga makamai masu linzami na Rasha.

Lokacin da aka tambayi Shugaba Donald Trump game da wannan tayi na Ukraine, ya bayyana cewa:

"Zan karɓi kowane irin taimako daga kowace ƙasa".
Zelensky ya ce Ukraine za ta ba da gudunmawa amma sai idan Amurka za ta ba ta kariya
Shugaban kasar Ukraine, Zelensky yana tattaunawa da majalisar tsaro kan rikicin Gabas ta Tsakiya. Hoto:@ZelenskyyUa
Source: Twitter

Tasirin bukatar Amurka ga Ukrain

Wannan buƙata ta Amurka ta ba wa ƴan Ukraine mamaki, duba da yadda gwamnatin Trump ta daina bayar da tallafin makamai kai-tsaye tun bayan hawansa mulki, kodayake tana ci gaba da ba da bayanan sirri masu muhimmanci.

Akwai fargaba cewa rikicin Gabas ta Tsakiya na iya raba hankalin abokan ƙawancen Ukraine, sannan ƙaruwar farashin mai na iya taimaka wa Rasha yau.

Sai dai shugaban kasar na Ukraine, Zelensky na ƙoƙarin yin amfani da wannan rikicin domin kare muradun ƙasarsa.

Adadin shugabannin Iran da aka kashe

A wani labari, mun ruwaito cewa, shugaban ƙasar Donald Trump ya bayyana cewa "babban hari" na soja da Amurka za ta ɗauka kan kasar Iran yana nan tafe.

Kara karanta wannan

Iran ta ce ta kashe sojojin Amurka 500 a luguden wuta da ta masu

Donald Trump ya yi ikirarin cewa hare-haren da Amurka ta kaddamar sun yi sanadin mutuwar shugabannin Iran guda 49 tun farkon fara yakin a ranar Asabar.

Da aka tambaye shi ko Amurka tana yin wani abu bayan harin soja domin taimaka wa al’ummar Iran su ƙwato ikon ƙasarsu, Trump ya ce, “Eh.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com