Rasha Ta Fadi dalilin da Ya Sa ba Ta Kai Dauki ga Iran ba a Yakinta da Isra’ila
- Fadar Kremlin a Rasha ta yi magana game da rashin shiga yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra'ila da aka fara a karshen makon jiya
- Kakakin Kremlin, Dmitry Peskov ya ce matsayin Rasha kan rikicin Iran bai sauya ba duk da ƙara tsanantar yaƙin Gabas ta Tsakiya
- Vladimir Putin ya yi alhinin kisan Ali Khamenei amma bai yi tsokaci kai tsaye kan hare-haren kasashen Amurka da Isra’ila ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Moscow, Russia - Fadar Kremlin a Rasha ta yi karin haske game da rashin taimakawa Iran yayin da ake ci gaba da yaki tsakaninta da Isra'ila.
Kasar ta ce Iran ba ta taɓa neman taimakon sojoji daga Rasha ba tun bayan da Amurka da Isra’ila suka fara kai hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar.

Source: Getty Images
Rasha ta magantu kan yakin Iran da Isra'ila
Mai magana da yawun Kremlin, Dmitry Peskov, ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wani taron yau da kullum da aka gudanar a Moscow, cewar Al Jazeera.
A cewarsa, gwamnatin Iran ba ta miƙa wata buƙata ga Rasha domin neman taimakon soja kan rikicin da ke ƙara tsananta a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rasha dai na daga cikin ƙasashen da ke da kusanci da Iran a harkokin siyasa da tsaro wanda ake mamakin rashin shigarta yakin.
A wannan makon ma wakilin Rasha a Majalisar Ɗinkin Duniya ya soki hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran, inda ya bayyana su a matsayin farmaki na gangan da aka shirya tun da wuri.
A shekarar 2025 ne Rasha da Iran suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta haɗin gwiwa ta dabarun tsaro domin tunkarar barazanar da suke ganin suna fuskanta tare.
Sai dai yarjejeniyar ba ta ƙunshi cikakken alƙawarin kare juna da sojoji ba kamar yadda Rasha ta yi da wata ƙasa kamar Koriya ta Arewa.

Source: Getty Images
Putin ya jajanta kan kisan Khemenei
Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana alhinin kan abin da ya kira kisan gilla na jagoran addinin Iran Ali Khamenei.
Sai dai duk da haka Putin bai fito fili ya yi magana kan hare-haren da Amurka da Isra’ila ke ci gaba da kai wa Iran ba.
Masu nazari kan harkokin siyasa sun ce ana iya ganin cewa martanin Rasha kan rikicin zai tsaya ne a kalaman siyasa a wuraren tattaunawa na duniya kamar Majalisar Tsaro ta United Nations.
Peskov ya kuma jaddada cewa matsayin Rasha kan rikicin ya kasance iri ɗaya kuma babu wani sauyi a manufofin ƙasar.
Ya ƙara da cewa rikicin Gabas ta Tsakiya bai kamata ya shafi farashin man fetur ko fetur a cikin Rasha ba, cewar The Moscow Times.
Amurka ta cafke wanda ya so kashe Trump
An ji cewa Rundunar tsaron Amurka ta ce Shugaba Donald Trump ya sha da kyar bayan sojojin kasar sun kashe wani babban jami’in Iran da ake zargi da jagorantar shirin kashe shi.

Kara karanta wannan
Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa
Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka yi a hedkwatar ma’aikatar tsaron Amurka.
Hegseth ya ce jami’in Iran da aka kashe shi ne ke jagorantar wata ƙungiya da ake zargi ta shirya yunkurin kashe Trump a baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

