Alireza Arifi: Abubuwan Sani game da Sabon Shugaban Rikon Iran
Bayan kashe Ayatollah Ali Khamenei a harin da Amurka/Isra'ila suka kai a ranar Asabar, 28 ga Fabrairun 2026, Iran ta zabi jagoran riko, Ayatollah Alireza Arafi.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - A karshen makon da ya wuce ne kasashen Amurka da Isra'ila suka hada kai wajen kai hari Iran, lamarin da ya jawo mutuwar Ayatollah Ali Khamenei.
Biyo bayan lamarin, masu ruwa da tsaki sun zabi Ayatollah Alireza Arafi a mastayin wanda zai maye gurbinsa a matsayin jagoran riko.

Source: Twitter
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da Ayatollah Alireza Arafi.
Yaushe aka haifi Alireza Arafi?
An haifi Ayatollah Alireza Arafi a shekarar 1959 a tsohon garin Meybod da ke tsakiyar lardin Yazd na kasar Iran, kuma ya fito ne daga gidan malaman addini.
BBC Hausa ta wallafa cewa a shekarar 1969, lokacin da yake da shekaru 11 kacal, ya koma birnin Qom domin kara zurfafa karatun addininsa, wanda tun da farko ya fara yi a karkashin kulawar mahaifinsa a Meybod.

Source: Getty Images
Alireza Arafi lokacin juyin juya hali
A cewar bayanan cibiyar bincike ta Middle East Institute (MEI) a lokacin juyin juya halin Iran na shekarar 1979, Alireza yana da shekaru 21 ne kawai, kuma bai kai matsayin da zai taka muhimmiyar rawa ba.
Saboda haka, cibiyar ta ce ba daidai ba ne a sanya Ayatollah Arafi cikin wadanda ake kira 'yan juyin juya hali na farko a gwamnatin Iran.

Source: Getty Images
Bincike ya nuna cewa har a 1980, matashin malamin addinin, Arafi bai yi wani abin da ya bambanta shi sosai da sauran matasan malamai da dama da suka shiga sahun Jamhuriyar Musulunci ba.
Lokacin da Arafi ya fara shahara a Iran
Economic Times ta wallafa cewa sunan Arifi ya fara yin fice bayan Khamenei ya zama Jagoran Koli a shekarar 1989, kuma a shekarar 1992 aka fara naɗa shi a matsayin limamin sallar Juma’a a garinsu na Meybod.

Kara karanta wannan
Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa
A lokacin yana da shekara 33 kacal, wanda ake ganin mai ƙaramin shekaru ne ga irin wannan muƙami, kuma hakan ya nuna irin amincewar da Khamenei yake da ita a kansa.

Source: Getty Images
An ce shirye-shiryen da Khamenei ya yi na naɗa Arafi a manyan muƙamai masu muhimmanci da kuma waɗanda ke da matuƙar tasiri sun nuna kwarin gwiwa da yake da shi kan ƙwarewarsa a harkokin gudanarwa.
Mukaman da Ayatollah Arifi ya rike a Iran
Kafin a naɗa shi jagorancin riko a Iran, Ayatollah Arafi yana riƙe da muƙamai uku daga cikin mukamai mafi tasiri a ƙasar a lokaci guda.
An bayyana cewa yana rike da matsayin daraktan tsarin manyan makarantun addini na Iran a faɗin ƙasar, mamba a majalisar kundin tsari, da kuma mamba a majalisar kwararru.

Source: Getty Images
Press TV ta rahoto cewa Fafaroma Francis ya karɓi baƙuncinsa a wata ganawa ta musamman a fadar Vatican a watan Mayu na shekarar 2022 — wani mataki da ba kasafai ake gani ba na diflomasiyyar addinai tsakanin manyan limaman Iran.
Harsunan da Arafi ya ke ji a duniya
Duk da cewa ya taso cikin tsari mai ƙarfi a tsakanin malamai birnin Qom, Arafi ya zama na daban cikin jiga-jigan malamai da ke aiki a gwamnatin Iran.
Ana ɗaukarsa mutum mai ilimi sosai, wanda ke iya harsuna da dama, kuma yana magana da Larabci da Turanci cikin ƙwarewa bayan yaren Farisa da ya iya.

Source: Getty Images
Rahoton Hindustantimes ya ce an san shi da kwarewa a fannin fasaha. Sau da dama yana jaddada muhimmancin amfani da sababbin fasahohin AI.
Majotaba Khamenei yana raye a Iran
A wani labarin, kun ji cewa kasar Iran ta fadi halin da dan marigayi Ayatollah Ali Khamenei mai suna Mojtaba ya shiga bayan kai hari kasar.
Iran ta yi bayani ne yayin da aka rika yada jita-jita game da halin da ya shiga bayan harin da Amurka da Isra'ila suka hada kai suka kai Tehran.
Gwamnatin Iran bayyana cewa a lokacin da aka kai harin, Mojtaba Khamenei ba ya zaune a Iran, kuma yanzu haka yana cikin koshin lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

