Sanatocin Amurka Sun Kada Kuri'a kan Hana Trump Cigaba da Yaki da Iran

Sanatocin Amurka Sun Kada Kuri'a kan Hana Trump Cigaba da Yaki da Iran

  • Majalisar Dattawan Amurka ta kada kuri'a domin hana Shugaban kasar Donald Trump cigaba da shigarwa Isra'ila yaki da Iran
  • Kudirin ya samu kuri’u 47 ne kacal, yayin da 53 suka ki amincewa da duk wani yunkuri na sanya wa Trump takunkumi kan batun
  • Duk da haka ana sa ran Majalisar Wakilai za ta yi kuri’a kan irin wannan kudiri a wannan rana ta Alhamis 5 ga watan Maris, 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States of America - Majalisar Dattawan kasar Amurka ta yi watsi da wani yunkuri da ‘yan jam’iyyar Democrat suka dauki nauyi.

Kudurin na son a tilasta wa gwamnatin Shugaban kasa, Donald Trump, ta dakatar da yakin da Amurka ke yi da Iran ba tare da izinin Majalisa ba.

Kara karanta wannan

Yakin Amurka/Isra'ila da Iran: Muhimman abubuwan da suka faru a rana ta 5

Shugaban Amurka Donald Trump ya samu goyon bayan Sanatoci a yaki da Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

TRT World ta wallafa cewa kuri’ar da aka kada a ranar Laraba 4 ga watan Maris 2026 ta nuna cewa sanatoci 47 ne suka goyi bayan kudirin.

Sanatocin Amurka sun bi bayan Trump

BBC ta ruwaito cewa Sanatocin Amurka 53 suka yi watsi da kudirin yan Democrat na son a haramta wa Trump shiga yaki da Iran ba tare da izini ba.

Wannan ya hana kudirin samun damar fita daga kwamitin harkokin kasashen waje na Majalisar Dattawa domin a tattauna shi a matsayin cikakken kudiri.

Sanatocin jam’iyyar Democrat, wato Tim Kaine, Adam Schiff da Chuck Schumer ne suka gabatar da kudirin.

Sanata daga jam'iyyar Trump ya ki amincewa da yaki a kan Iran
Dondl J Trump, Shugaban Amurka da ke taya Isra'ila yaki ba izinin majalisa Hoto: Donald J Trump
Source: Twitter

Sun nemi a tilasta wa gwamnatin Amurka dakatar da shiga yakin da ake yi da Iran matukar Majalisa ba ta amince da amfani da karfin soji ba.

Yawancin sanatocin jam’iyyar Republican sun yi watsi da kudirin, lamarin da ya kawo cikas ga yunkurin farko da Majalisar ta yi na takaita hare-haren da Amurka ke kai wa Iran.

Kara karanta wannan

Asara ta fara bin Amurka, ta rasa biliyoyin Daloli kwanaki 5 da fara yakin Iran

Sanata daga jam'iyyar Trump ya bi 'yan Democrat

Sai dai wani Sanata na Republican, Rand Paul, ya saba wa matsayar jam’iyyarsa inda ya goyi bayan kudirin.

A daya bangaren kuma, sanatan Democrat John Fetterman ya kada kuri’ar kin amincewa da shi, inda ya koma bayan Trump.

Kafin a kada kuri’ar, Kaine ya shaidawa manema labarai cewa bai kamata Amurka ta shiga yaki ba tare da cikakken muhawara da kuma kuri’ar Majalisa ba.

Shugabannin jam’iyyar Republican a Majalisar sun kare matakin shugaban kasa, suna cewa yana da ikon jagorantar hare-haren sama da ake kaiwa kan Iran domin kare muradun Amurka.

Ko da a ce kudirin ya samu nasara a Majalisar Dattawa da kuma Majalisar Wakilai, akwai yiwuwar shugaban kasa ya yi amfani da ikon kin amincewa da shi.

Duk da cewa ‘yan Democrat sun san kudirin na fuskantar babban kalubale, sun ce ya zama dole a tilasta wa ‘yan majalisa su fito fili su bayyana matsayinsu a yau Alhamis 5 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Luguden wutar Iran ya jefa Amurkawa cikin tsoro, suna korafi ga Trump

Amurka tana yin asara a yakin Iran

A baya, mun wallafa cewa kididdigar barnar da Iran ta yi wa Amurka na nuna cewa an yi asarar kayan aikin soja da kudinsu ya kai kusan Dala biliyan 1.9 a yan kwanakin nan.

Wata na'urar Amurka ta 'Radar' mai darajar dala biliyan 1.1 a sansanin Al Udeid da ke Qatar na cikin manyan kayayyakin da aka lalata a ramuwar gayyar da Iran ke yi.

Iran ta kai hari kan sansanonin soja da ofisoshin jakadancin Amurka a kasashe da dama na Gabas ta Tsakiya bayan harin da aka kai mata da ya kashe Ayatollah Khamenei.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng