Abin da Najeriya da Jagororin Afrika ke Fadi kan Yakin Iran, Amurka da Isra'ila
Shugabannin Afrika sun yi maganganun neman sulhu da goyon baya tun da Amurka da Isra'ila suka takalo yaki da Iran a ƙarshen makon da ya gabata.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Nahiyar Africa – Shugabannin nahiyar Afrika sun yi kira da nuna goyon baya da niyyar shiga tsakani bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai kan Iran a ƙarshen mako.
Isra'ila ta yi iƙirarin cewa an haɗa gwiwa da Amurka, inda aka ji Donald Trump na alfahari da yadda jami'an leken asirin ƙasar suka dade suna shiri kafin harin.

Source: Facebook
BBC ta wallafa cewa Amurka da Isra'ila sun kai hari Iran a ranar 28 ga watan Fabrairu, lamarin da ya hallaka jagoran addini na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei.
Tun daga wannan lokaci lamari ya hautsine, sai dai yawancin ƙasashen Afrika sun yi kira da a sassauta rikicin tare da mutunta dokokin ƙasa da ƙasa, tare da fadin yadda yakin zai shafi nahiyarsu.
Legit ta tattaro wasu daga cikin abubuwan da ƙungiyoyin Afrika da ƙasashen yankin suka ce game da yaƙin.
Kiran ƙasashen Afrika kan yaƙin Iran:
1. Kungiyar AU
RFI ta wallafa cewa kungiyar AU ta fitar da sanarwa cewa hare-haren soji da kuma martanin da Iran ta mayar ma nuni da ƙarin tsananta rikici mai hatsari da matuƙar tayar da hankali.
Ƙungiyar ta ce lamarin da ke tsananta a Gabas ta Tsakiya na barazanar jefa yankin gaba ɗaya cikin wani yanayi na tashin hankali da zai gagari kundila

Source: Facebook
Ta kuma buƙaci dukkanin ɓangarorin da su mutunta dokokin ƙasa da ƙasa da kuma yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya domin kare zaman lafiya da tsaro na duniya.
Shugaban ƙungiyar ta AU, Mahamoud Ali Youssouf, ya yi kira da a yi haƙuri, a sassauta rikicin cikin gaggawa, tare da ci gaba da tattaunawa mai dorewa.
Ya jaddada cewa:
“Ƙarin tsananta rikici na iya ƙara dagula zaman lafiyar duniya, tare da mummunan tasiri kan kasuwannin makamashi, tsaron abinci da ƙarfin tattalin arziki – musamman a Afrika, inda rikice-rikice da matsin tattalin arziki ke ci gaba da ƙamari.”
2. ECOWAS
A makon nan, Thisday ta ruwaito ECOWAS ma ta bayyana matuƙar damuwarta kan yadda rikicin ke ƙaruwa a yankin Tekun Fasha.
Ta jaddada cewa duk wani dogon tangarda a yankin Tekun Fasha zai iya kawo barazana ga samuwar man fetur da iskar gas a duniya.

Source: Twitter
Ƙungiyar ta ce:
“Ƙaruwar farashin makamashi zai yi tasiri kai tsaye kan tattalin arzikin ƙasashen Yammacin Afrika, waɗanda tuni hauhawar farashi da dogaro da shigo da man da aka tace suka raunana su.”
ECOWAS ta kuma yi nuni da barazanar da hakan ka iya haifarwa ga wadatar abinci, ganin cewa yawancin ƙasashen Afrika na dogaro da shigo da hatsi da kayan aikin gona ta hanyoyin kasuwanci masu rauni.
3. Najeriya
Gwamnatin Tarayya ta yi kira da a sassauta rikicin cikin gaggawa tare da nuna matuƙar haƙuri a yankin Tekun Fasha, bayan hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka kai kan Iran.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin X na Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya jim kaɗan bayan fara musayar wuta tsakanin ƙasashen.

Source: Twitter
A sanarwar da kakakin ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya buƙaci dukkanin ɓangarorin da abin ya shafa da su nuna matuƙar haƙuri tare da gujewa duk wani mataki da ka iya ƙara tsananta rikicin.
Ya jaddada muhimmancin fifita tattaunawa maimakon yaki, tare da yin kira da a bi ƙa’idojin yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya.
Haka kuma ya nemi a girmama yarjejeniyar Geneva, musamman dangane da mutunta ikon ƙasa, cikakken ikon iyaka, da warware rikice-rikice ta hanyar lumana.
4. Afrika ta Kudu
Anadolu Ajansi ta ruwaito Shugaban Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya ce ƙasarsa a shirye take koyaushe domin taimakawa wajen sasanta rikicin da ke ƙara kamari a Gabas ta Tsakiya, yayin da hare-haren Amurka da Isra'ila kan Iran suka janyo ramuwar gayya daga Tehran.

Source: Facebook
Ya ce:
"Pretoria a shirye take ta taka rawa, ko ta fuskar shiga tsakani ko wata hanya, idan aka buƙaci hakan. Mu ‘yan ƙasa ne na duniya, don haka za mu iya taka duk rawar da Majalisar Ɗinkin Duniya za ta buƙaci mu taka.”

Kara karanta wannan
An ji duriyar Firaministan Isra'ila, Netanyahu ana tsaka da rade radin Iran ta tura shi lahira
"Afrika ta Kudu ta yi kira da a tsagaita wuta nan take tare da kawo ƙarshen wannan hauka inda ya ƙara da cewa ko da yake Shugaban Amurka Donald Trump na mayar da hankali kan yaƙin, Pretoria za ta ci gaba da matsa kaimi kan tattaunawa idan damar hakan ta samu."
Ramaphosa ya jaddada cewa tattaunawa ita ce hanya mafi dacewa don kawo ƙarshen yaƙin da hana ƙarin asarar rayuka marasa amfani.
6. Kenya
DW ta ruwaito Shugaban Kenya, William Ruto, tun kafin fara yaƙin Amurka da Isra'ila da Iran ya yi kira da a nuna haƙuri, a tattauna, tare da buƙatar sassauta rikicin domin wanzuwar zaman lafiya.

Source: Facebook
Ruto ya ce:
“Kenya na Allah wadai da hare-haren da aka kai kan Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar, Saudiyya, Iraki, Oman, Kuwait, Jordan da Bahrain a cikin wannan rikici da ke ƙara yaduwa a Gabas ta Tsakiya.”
“Ya bayyana karara cewa yaɗuwar rikicin zuwa ƙasashe da dama na haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da tsaron duniya. Kenya na kira da a gaggauta haɗa kan masu ruwa da tsaki domin sassauta rikicin.”
Iran ta yi magana kan sulhu da Amurka
A bayan mun wallafa cewa Iran ta bayyana cewa ba ta da niyyar tattaunawar sulhu da Amurka kuma za su ci gaba da fafatawa har sai abin da hali ya yi bayan kashe jagoranta.
Babban jigon siyasar Iran, Mohammad Mokhber ya ce kasarsa na da karfin ci gaba da wannan yaki, wanda ya shiga rana ta biyar bayan takalar Amurka da Iran a ƙarshen mako.
A ranar Asarar, 28 ga watan Fabrairu na shekarar 2026, Amurka da Isra'ila suka kashe Ayatollah Ali Khamenei, lamarin da Iran ta ce sai ta dauki fansa a kan wadanda suka yi aikin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



