"Mun Shirya Mutuwa," Saƙon da Hezbollah Ta Aika wa Isra'ila Ana cikin Ɓarin Wuta
- Shugaban Hezbollah Naim Qassem ya bayyana cewa kungiyarsa ba za ta taba mika wuya ga zaluncin Amurka da kasar Isra'ila ba
- Naim Qassem ya jaddada cewa Hezbollah za ta ci gaba da yakar Israila don ramar irin azabar da aka yi wa mutanesu na watanni 15
- Akalla mutane 72 ne suka mutu a kasar Lebanon yayin da wasu dubunnai tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren Isra'ila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Lebanon - Shugaban ƙungiyar Hezbollah dake ƙasar Lebanon, Naim Qassem, ya lashi takobin cewa ƙungiyarsa ba za ta mika wuya ko da baya a yaki da Isra'ila ba.
Naim Qassem ya ce Hezbollah za ta dake kan duk wani "zaluncin Amurka da Isra'ila" har zuwa lokacin da za su shaki numfashin ƙarshe.

Source: Getty Images
Hezbollah za ta ci gaba da yaki da Iran
A jawabin da aka nuna a gidan talabijin na ƙungiyar, wanda Aljazeera ta rahoto, Naim Qassem ya bayyana cewa wannan yaƙi ya zama "a mutu ko a yi rai."
Yayin da ya dage cewa Hezbollah za ta ci gaba da fafatawa da Isra'ila har sai sun cimma burinsu, ya kuma ce:
"Muna fuskantar zalunci... mun yanke shawarar tunkarar wannan zaluncin har zuwa numfashinmu na karshe, ba za mu taba mika wuya ba, don ba ma jin tsoron mutuwa."
Wannan shi ne jawabi na farko da shugaban ya yi tun bayan kisan Ayatollah Khamenei da ya jefa yankin cikin ruwan wuta ranar Asabar.
Naim Qassem ya bayyana cewa hare-haren da Hezbollah ke kai wa Isra'ila yanzu martani ne ga "zaluncin watanni 15" da ƙasar ta yi wa Lebanon.
Hezbollah ta kai hare-hare kan Isra'ila
Hezbollah ta sanar a yau cewa ta tura gungun jiragen yaki mara matuƙa domin farmakar na'urorin radar na garkuwar Iron Dome dake sansanin Kiryat Elazar a birnin Haifa.
Haka kuma ƙungiyar ta ce ta farmaki sansanin sojin sama na Palmachim dake kudancin Tel Aviv, wanda ke da nisan kilomita 140 daga kan iyakar Lebanon, in ji rahoton RFI.
Waɗannan hare-hare sun zo ne a matsayin martani ga ruwan bama-bamai da Isra'ila ke yi wa biranen Lebanon, ciki har da kewayen birnin Beirut.
Mummunar asara a Lebanon
Ma'aikatar Lafiya ta Lebanon ta tabbatar da cewa akalla mutane 72 ne suka riga mu gidan gaskiya tun daga ranar Litinin, yayin da wasu 437 suka jikkata sakamakon hare-haren Isra'ila.
Ministan jin ƙai na ƙasar ya ƙara da cewa adadin mutanen da suka rasa gidajensu ya haura 83,847 kamar yadda rahoton The Times of Israel ya nuna.
Isra'ila na ci gaba da farmakar yankuna daban-daban na ƙasar domin murkushe Hezbollah, yayin da ƙungiyar ke ƙoƙarin kare kanta da makaman da take samu daga Iran.
Asali: Legit.ng

