Yaki na Kara Zafi da Amurka, An Ji Shirin da Iran Take Yi na Nada Magajin Ayatollah Khamenei
- Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi bayani kan halin da ake ciki game da nada sabon jagoran addini da zai gaji marigayi Ayatollah Ali Khamenei
- Wani mamba a Majalisar koli ta Iran, wadanda ke da alhakin zabar jagoran addini, Ahmad Khatami ya ce suna kokarin gudanar da zabe nan kusa
- Wannan na zuwa ne bayan hare-haren hadin gwiwa tsakanin kasashen Amurka da Isra'ila sun yi ajalin jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Yayin da yaki ke kara zafi tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila, Jamhuriyar Musulunci na ci gaba da kokarin nada sabon jagoran addini na kasa bayan mutuwar Ayatollah Ali Khamenei.
Da safiyar yau Laraba, hukumomin kasar Iran sun bayyana cewa suna kokarin gaggauta nada magajin Khamenei, wanda zai ci gaba da jagorantar harkokin mulki a kasar.

Kara karanta wannan
Khamenei: An ɗage taron jana'izar jagoran addini a Iran yayin da ake harin magajinsa

Source: Getty Images
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa harin hadin gwiwa na Amurka da Isra’ila ne ya yi sanadiyar mutuwar Ayatollah Ali Khamenei a karshen makon da ya gabata.
Kasar Iran ta bayyana shirin da take yi
Ahmad Khatami, mamba a Majalisar Koli ta Jagoranci a Iran, wadda ita ce ke da alhakin zabo sabon jagora, ya ce:
"Muna iya kokarinmu, Insha Allahu, za a nada jagora a duk lokacin da dama ta samu nan ba da dadewa ba. Mun kusa cimma hakan, amma halin da ake ciki yanayi ne na yaki."
Tun da fari a ranar Laraba, Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya bayyana cewa duk wani jagoran addini da Iran ta zaba domin ya gaji Khamenei, “tabbas za mu yi kokarin kashe shi.”
Martanin Iran game da baranazar Isra'ila
Khatami ya mayar da martani inda ya ce “akwai bukatar yin taka-tsantsan” duba da wannan barazana, yana mai kara cewa zaben sabon jagoran ya kusa kankama.

Kara karanta wannan
Yadda dan Khamenei da zai iya gadonsa, Mojtaba ya tsallake harin Amurka da Isra'ila
Wannan majalisa da ke sa alhakin zabar sabon jagoran addini a Iran, tana da mambobi 88 wadanda ake zaba duk bayan shekaru takwas.
Rahotanni daga kafofin yada labaran Iran sun nuna cewa a ranar Talata, harin Amurka da Isra’ila ya shafi wani gini na wannan majalisa da ke birni mai tsarki na Qom.
Kwana daya kafin nan, Amurka/Isra'ila sun kai hari babban ofishin majalisar da ke Tehran, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta ruwaito.

Source: Getty Images
Iran ta fara shirin mika mulki ne tun ranar Lahadi, kwana daya bayan mutuwar Khamenei, wanda ya jagoranci kasar tun daga shekarar 1989.
A halin yanzu, shugabannin riko da ke tafiyar da kasar sun hada da Masoud Pezeshkian (Shugaban Kasa) Gholamhossein Mohseni Ejei (Alkalin Alkalai/Shugaban bangaren shari’a) da Alireza Arafi (Malamin addini kuma mamba a Majalisar Koli).
'Dan Khamenei ya tsallake harin Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa 'dan marigayi Ayatollah Ali Khamenei mai suna Mojtaba ya tsallake hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai Iran a karshen makon da ya wuce.
Wasu majiyoyi biyu na Iran sun shaida wa manema labarai, a ranar Laraba, 4 ga Fabrairun 2026 cewa Mojtaba Khamenei yana na da rai har yanzu.
Mojtaba Khamenei ya kasance malamin addini ne mai matsakaicin matsayi wanda ke da kusanci da rundunar juyin juya halin Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng