Magana Ta Fito: Yadda Aka Tsara Hallaka Khamenei yayin da Yake Ganawar Tsaro
- Rahotanni daga hukumomi a Iran sun tabbatar da cewa an hallaka jagoran addini a kasar, Ali Khamenei a birnin Tehran
- Wasu majiyoyi suka ce ya mutu a hare-haren sama na hadin gwiwar Amurka da Isra’ila a Tehran da taimakon hukumar CIA
- Akalla mutane 787 sun mutu a Iran yayin da hare-hare da ramuwar gayya ke ci gaba kan Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Rahoto ya bayyana cewa bayan fiye da shekaru 30 yana jagorantar Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya mutu a hare-hare.
Hakan ya biyo bayan wasu hare-haren sama da Amurka da Isra’ila suka kai a safiyar Asabar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2026 a Tehran.

Source: Getty Images
Rahoton Al Jazeera ya ce Hukumar Leken Asiri ta Amurka (CIA) ta tattara bayanai kan wani taro da manyan hafsoshin sojojin Iran za su yi tare da Khamenei, sannan ta mika bayanan ga Isra’ila.

Kara karanta wannan
Ronaldo ya lallaɓa ya bar Saudiyya saboda rikicin Isra'ila, Iran? an ji gaskiyar zance
Yawan mutanen da suka mutu a Iran
Hukumar agajin gaggawa ta Iran ta tabbatar da mutuwar akalla mutane 787 a sassan kasar, yayin da daruruwa suka jikkata sakamakon hare-haren.
A martaninta, Iran ta kai hare-hare kan Isra’ila da wasu sansanonin sojin Amurka a kasashen Gulf ciki har da Qatar da Saudiyya.
Shugaban Amurka Donald Trump ya kare hare-haren, yana mai cewa za su ci gaba har sai an cimma abin da ya kira “zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya”.

Source: Twitter
Yadda CIA ta taimaka aka hallaka Khamenei
An ambato majiyoyi da ba a bayyana sunayensu ba amma suna da masaniya kan aikin, Hukumar Leken Asiri ta Amurka (CIA) ta tattara bayanai kan wani taron safiyar Asabar da zai hada Khamenei da manyan hafsoshin sojin kasar.
Haka kuma, kafar talabijin ta CBS, ta ambato wani jami’i da ba a bayyana sunansa ba, cewa CIA ta bai wa Isra’ila bayanan inda Khamenei yake a lokacin.

Kara karanta wannan
Bayan hari a Saudiyya, Iran ta gamu da farmakin Isra'ila, an gano asarar da aka yi
Khamenei ya jagoranci kasar tun daga shekarar 1989 bayan rasuwar Ruhollah Khomeini, bayan ya taba rike mukamin shugaban kasa tun 1981.
An ce jiragen yakin Isra’ila sun tashi da safiyar Asabar 28 ga watan Fabrairun 2026, inda suka jefa bama-bamai kan wani gini a tsakiyar Tehran da ke dauke da ofisoshi da muhallin jagoran.
Harin ya kuma hallaka wasu manyan jami’an tsaro ciki har da hafsoshin dakarun IRGC da ministan tsaro da wasu manyan jami'an tsaro.
Rahoton ya ce hotunan tauraron dan Adam sun nuna hayaki na tashi daga gine-ginen da aka lalata bayan harin.
Isra'ila ta bar jirgin Netanyahu a Jamus
Mun ba ku labarin cewa Isra’ila ta mayar da jirgin gwamnati zuwa Jamus bayan Iran ta rike wuta wajen kai harin ramuwar gayya ƙasar Yahudawan.
Iran ta nanata cewa ba za ta saurara wa kowa ba bayan harin Amurka da Isra'ila ya hallaka Ayatollah Khamenei a ranar Asabar 28 ga watan Fabrairun 2026 da muke ciki.
Jirgin “Wing of Zion” na dauke da na’urorin sadarwa na zamani masu tsaro, kuma shi ne jirgin da Benjamin Netanyahu ke hawa.
Asali: Legit.ng