Amurka Ta Gamu da Gagarumar Matsala a Yaki da Iran, Spain Ta Juya baya ga Trump

Amurka Ta Gamu da Gagarumar Matsala a Yaki da Iran, Spain Ta Juya baya ga Trump

  • Gwamnatin Spain ta haramta wa sojojin Amurka amfani da sansanoninta na Rota da Moron domin kai hare-hare kan kasar Iran
  • Firayim Minista Pedro Sanchez ya kira hare-haren Amurka da Isra'ila kan Iran a matsayin barazana ga dokokin kasa da kasa
  • To sai dai, Biritaniya da Jamus sun amince su ba Amurka goyon baya don maida martani ga hare-haren makaman linzamin Iran

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Spain - Gwamnatin ƙasar Spain ta bayyana cewa Amurka ba ta amfani da sansanonin sojin da suke haɗin gwiwa a ƙasarta don kai hare hare Iran.

Spain, ta kuma jaddada cewa ba za ta ba Amurka damar yin amfani da sansanonin sojin hadin gwiwar don kai hare-hare a kasar ta Gabas ta Tsakiya ba.

Spain ta ce ba za ta ba Amurka damar kai hari Iran daga kasarta ba.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi kamari, Faransa ta tura jirage UAE da Iran ke kai hare hare

Spain ta ce Amurka ba za ta yi amfani da sansanoninta wajen kai hari Iran ba
Wani jirgin Amurka da aka ajiye a sansanin sojojin hadin gwiwa na Moron de la Frontera da ke Spain. Hoto: CRISTINA QUICLER/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Spain ta juya wa Amurka baya

Ministan harkokin wajen Spain, Jose Manuel Albares, ya shaida hakan ga gidan talabijin na ƙasar, kamar yadda Aljazeera ta rahoto.

Jose Manuel Albares ya ce bisa bayanan da yake da su, Amurka ba ta samu izinin amfani da sansanonin Rota da Moron domin wannan yaƙi a halin yanzu.

Wannan mataki ya zo ne bayan da Firayim Minista Pedro Sanchez ya yi tir da hare-haren Amurka da Isra'ila, yana mai kiran su da "daukar matakin soja mai haɗari" wanda ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

Albares ya jaddada cewa gwamnatin Spain ba za ta amince da amfani da waɗannan sansanoni ga duk wani abu da ya saɓa wa yarjejeniyar da ke tsakaninsu ko kuma ya ci karo da ƙa'idojin Majalisar Ɗinkin Duniya ba.

Ko da yake Amurka tana aiki a waɗannan sansanonin, ikon mallakarsu yana hannun ƙasar Spain ne.

Kara karanta wannan

An ji duriyar Firaministan Isra'ila, Netanyahu ana tsaka da rade radin Iran ta tura shi lahira

Motsin jiragen Amurka a kasar Spain

Ma'aikatar tsaron ƙasar ta ƙara da cewa sansanonin ba za su ba da wani tallafi ba, face dai idan bukatar hakan ta taso ta fuskar jin ƙai kawai yanzu.

Duk da iƙirarin gwamnatin Spain, bayanan taswirar FlightRadar24 sun nuna cewa akalla jiragen yaƙin Amurka 15 ne suka tashi daga sansanonin kudancin Spain tun bayan fara hare-haren, in ji rahoton Reuters.

Bayanan sun nuna cewa akalla bakwai daga cikin jiragen sun sauka ne a sansanin Ramstein dake ƙasar Jamus yanzu.

Wannan ya nuna yadda Amurka ke ƙoƙarin sauya fasalin dabarunta sakamakon ƙwaƙƙwarar adawar da Spain take nuna wa yaƙin.

Spain ta yi Tur da hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa Iran
Sansanin sojojin hadin gwiwar Amurka da Spain na Moron de la Frontera da ke kusa da Sevilla. Hoto: CRISTINA QUICLER/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Rarrabuwar kan kasashen Turai

Matsayin Spain ya bambanta sosai da na sauran manyan ƙasashen Turai yanzu, kamar yadda wani rahoto na France24 ya nuna.

Da fari, Biritaniya ta ƙi bayar da izin amfani da sansanoninta, amma a ranar Lahadi, Firayim Minista Keir Starmer ya ba da izinin amfani da su domin "kariya ga kai."

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Trump ya fadi wasu dalilai 2 da suka sa ya kai hare hare Iran

Ƙasashen Faransa da Jamus su ma sun nuna shirye-shiryensu na goyon bayan Amurka a wannan yaki da ake fafatawa.

A wata sanarwar haɗin gwiwa, shugabannin Biritaniya, Faransa, da Jamus sun bayyana fargabarsu game da "hare-haren makaman linzami da Iran ke kaiwa ba kakkautawa" ga ƙasashen da ba su ji ba ba su gani ba.

Makaman Amurka a yaki da Iran

Kun dai ji cewa, Amurka ta fitar da sunayen manyan jiragen yaki da makaman da take amfani da su a samamen Operation Epic Fury.

Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin kaddamar da samamen Operation Epic Fury domin kai hare-hare a sassa daban daban na Iran.

Operation Epic Fury ya hada da amfani da jiragen yaki masu kauce wa radar da makaman da ke tarwatsa rumbun makaman nukiliya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com