Epic Fury: Amurka Ta Jero Miyagun Makamai 23 da Take Amfani da Su a Yaki da Iran
- Rundunar sojin Amurka ta fitar da sunayen manyan jiragen yaki da makaman da take amfani da su a samamen Operation Epic Fury
- Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin kaddamar da samamen Operation Epic Fury domin kai hare-hare a sassa daban daban na Iran
- Operation Epic Fury ya hada da amfani da jiragen yaki masu kauce wa radar da makaman da ke tarwatsa rumbun makaman nukiliya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Rundunar sojin Amurka ta CENCOM ta fitar da jerin sunayen manyan makamai da jiragen soji da take amfani da su a babban samamen nan na "Operation Epic Fury".
Wannan gagarumin samame, wanda aka kaddamar a ranar Juma'a, 27 ga Fabrairu, 2026, ya farmaki muhimman wurare a Iran, ciki har da ma'aikatun makaman linzami, sansanonin dakarun ruwa, da kuma wuraren dake kusa da ofishin marigayi Ayatollah Khamenei.

Source: Getty Images
Samamen Operation Epic Fury a Iran
Wannan na kunshe ne a cikin bayanan samamen Operation Epic Fury na awanni 48 da CENCOM ta wallafa a shafinta na X.
Manufar Operation Epic Fury ita ce kawar da duk wata barazana ga dakarun Amurka da kawayenta, tare da aika sako mai karfi game da shirye-shiryen nukiliya na Iran.
Amurka ta yi amfani da makamai masu hatsari a ranar Asabar, 28 ga Fabrairu, ciki har da jirage mara matuka na "Lucas", makaman linzami na "Tomahawk", da kuma jiragen yaki masu sulken kauce wa radar (stealth).
Wani sabon abu shi ne yin amfani da jirage mara matuka da ake kira one-way attack drones a turance, wadanda aka kwaikwayi kirarsu daga kasar Iran.
Takaddamar AI da fasahar Anthropic
Wani babban labari da ya bayyana shi ne yadda Shugaba Donald Trump ya ba da umarnin dakatar da yin aiki da kamfanin fasahar nan na Anthropic a yaki da Iran.

Kara karanta wannan
Iran ce ta kakkabo su? Amurka ta yi magana kan jiragen yakinta 3 da suka fado a Kuwait
Gwamnatin Amurka ta bayyana kamfanin a matsayin "barazana ga tsaron kasa" a ranar 27 ga Fabrairu, kamar yadda rahoton Business Insider ya nuna.
Ko da yake fasahar AI ta Anthropic an saba amfani da ita a hukumomin leken asiri da na soji ta hanyar Amazon, kafar labaran Reuters ba ta iya tabbatar da takamaiman yadda aka yi amfani da wadannan kayan aiki a wannan yaki ba.
Makaman Amurka a yaki da Iran

Source: Twitter
Ga jerin jirage da sauran miyagun makamai da rundunar sojin Amurka ta bayyana cewa tana amfani da su a samamen Operation Epic Fury:
1. Jiragen yaƙi masu sulke da masu euwan wuta
- B-2 Stealth Bombers
- F-35 Stealth Fighters
- F-22 Raptor
- F-18 Fighter Jets
- F-16 Fighter Jets
- A-10 Attack Jets
- EA-18G Electronic Attack Aircraft
2. Jirage mara matuƙa
- Lucas Drones
- MQ-9 Reapers
- One-way Attack Drones
3. Jiragen leƙen asiri da sadarwa
- Airborne Early Warning & Control (AWACS)
- Airborne Communication Relay
- P-8 Maritime Patrol Aircraft
- RC-135 Reconnaissance Aircraft.
4. Jiragen dakon kayan yaki da mai
- C-17 Globemaster
- C-130 Cargo Aircraft
- Refueling Tanker Aircraft
Karanta rahoton a nan kasa:
Dalilin Trump na kai hari Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, Donald Trump ya bayyana manyan dalilan da suka sanya ya ba da umarnin kai hare-hare a kasar Isra'ila da kashe Ayotallah Khamenei.
A karshen makon nan ne, Isra'ila da Amurka suka kai jerin hare-hare a Iran, lamarin da ya yi ajalin manyan sojojin kasar, ciki har da jagoran addini, Khamenei.
A ranar Litinin, Trump ya ce ya ba da umarnin kai hari kan kasar Iran ne domin dakile shirye-shiryenta na kera makaman nukiliya da makaman linzami masu dogon zango.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

