Bayan Hari a Saudiyya, Iran Ta Gamu da Farmakin Isra'ila, an Gano Asarar da Aka Yi
- Ana ci gaba da kai hare-hare tsakanin Isra'ila da Iran wanda a yanzu aka dauki kwanaki ana gwabzawa a yankin Gabas ta Tsakiya
- Isra’ila ta kaddamar da sababbin hare-hare a Tehran da Beirut bayan rikicin da ya biyo bayan harin Amurka da kasar kan Iran
- Rikicin ya tsananta bayan kashe jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, lamarin da ya jawo ramuwar gayya da hare-hare a yankin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Sojojin Isra’ila sun kaddamar da sababbin hare-hare a biranen Tehran da Beirut a ranar Talata 3 ga watan Maris, 2026.
Sababbin hare-haren sun biyo bayan harin jiragen sama marasa matuki guda biyu da suka kai farmaki ofishin jakadancin Amurka a Riyadh da wasu wurare a Saudiyya.

Source: Getty Images
Hare-hare tsakanin Isra'ila, Iran sun cigaba

Kara karanta wannan
Rikicin Iran/Isra'ila: An 'gano' yadda Ronaldo ya lallaɓa ya bar Saudiyya ana tsaka da rikici
Mahukuntan Saudiyya sun ce harin ya haddasa karamin gobara da lalacewa kadan, ba tare da asarar rayuka ba a yankin, cewar CNN.
Isra’ila ta ce dakarunta na kasa za su ci gaba da kutsawa cikin Lebanon domin kwace karin muhimman wurare don dakile hare-hare kan iyakarta.
Rikicin ya fara ne ranar Asabar 28 ga watan Maris, 2026 bayan Amurka da Isra’ila sun kai hari kan Iran, inda aka kashe jagoran kasar, Ayatollah Ali Khamenei, tare da iyalansa da manyan jami’ai.
Bayan haka, Iran ta mayar da martani da jerin hare-hare a sassa daban-daban na yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya kara dagula al’amura, cewar Al Jazeera.
Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya gargadi Iran cewa manyan hare-hare mafi muni na nan tafe.

Source: Twitter
Umarnin Amurka ga yan kasarta a Gabas ta Tsakiya
Amurka ta kuma umarci ‘yan kasarta da ke kasashen Iraki, Bahrain, Jordan, Iran, Lebanon, Syria, Kuwait, Oman, Yemen, UAE, Saudiyya, Masar da Qatar su fice.
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bukaci su bar wuraren cikin gaggawa ta hanyoyin sufuri na kasuwanci saboda barazanar tsaro mai tsanani.
Ramuwar gayyar Iran ta shafi kayayyakin makamashi a yankin Gulf, lamarin da ya jawo tashin gwauron zabi a farashin mai da iskar gas.
Kamfanin mai na Saudiyya mallakin gwamnati, Saudi Aramco, ya dakatar da ayyukan matatar Ras Tanura bayan harin jiragen Iran.
Rundunar juyin juya halin kasar Iran ta gargadi cewa duk jirgin ruwa da zai ratsa mashigar Strait of Hormuz zai fuskanci hari, bayan sanar da rufe ta.
Faransa ta tura jiragen yaki UAE
Mun ba ku labarin cewa Faransa ta tura jiragen yaki zuwa Gabas ta Tsakiya yayin da Iran ke cigaba da harba makamai masu linzami kan kasashe a yakin Amurka/Isra'ila.
Ministan harkokin wajen kasar Faransa, Jean-Noel Barrot ne ya bayyana haka a ranar Talata, 3 ga watan Maris 2026 a wata hira da ya yi da manema labarai.
Rahotanni sun tabbattar da cewa Jean-Noel Barrot ya bayyana abubuwan da jiragen yakin za su a yankin da ke fama da hare-hare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
