Yaki da Iran: Isra'ila Ta Rufe Masallacin Kudus, Ta Hana Falasdinawa Yin Sallah

Yaki da Iran: Isra'ila Ta Rufe Masallacin Kudus, Ta Hana Falasdinawa Yin Sallah

  • Isra'ila ta hana Musulmai Falasdinawa gudanar da ibada a masallacin Al-Aqsa a rana ta uku a jere duk da ana cikin watan Ramadan
  • Sheikh Ikrima Sabri ya bayyana cewa rufe masallacin ya saba wa hakkin gudanar da ibada kuma kokari ne na karbe ikon masallacin
  • Ma'aikatan hukumar Wakafi sun koka kan yadda aka hana su kai abinci ga masu tsaron masallacin tun fara yaki da Iran

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Isra'ila - Isra'ila ta rufe masallacin Al-Aqsa, watau Kudus a rana ta uku a jere, inda ta hana musulmi Falasɗinawa yin sallah a masallacin a wannan wata mai alfarma na Ramadan.

Wannan mataki, wanda aka kwatanta da keta alfarma mafi girma, ya zo ne a ƙarƙashin dokar ta-ɓaci da hukumomin Isra'ila suka kafa biyo bayan ɓallewar yaƙi da ƙasar Iran tun a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

An ji duriyar Firaministan Isra'ila, Netanyahu ana tsaka da rade radin Iran ta tura shi lahira

Isra'ila ta rufe masallacin Kudus yayin da take yaki da Iran
Musulmai sun taru a masallacin Kudus (Al-Aqsa) a ranar Juma'a ta biyu a Ramadan. Hoto: Mostafa Alkharouf/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

Isra'ila ta rufe masallacin Al-Aqsa

Falasɗinawa sun yi gargaɗin cewa Isra'ila na amfani da yanayin tsaro ne domin ƙarfafa ikonta kan masallacin da ke Gabashin Kudus, in ji rahoton Middle East Eye.

Masallacin, wanda ke a Gabashin Kudus (Jerusalem), zai ci gaba da kasancewa a rufe har sai gwamnati ta fitar da wata sanarwar nan gaba.

Sheikh Ikrima Sabri, tsohon babban mufti na Kudus kuma ɗaya daga cikin limaman masallacin Al-Aqsa, ya yi tir da wannan mataki da ya kira na "rashin adalci."

Ya shaida wa kafar labarai ta Al Jazeera cewa rufe masallacin na nufin ƙwace ikon gudanarwa daga hannun hukumar Waqf ta Musulunci yau.

Wannan rufe masallaci a cikin watan Ramadan abu ne da ba a saba gani ba a tarihi, domin ko a lokacin rikice-rikicen 2014 da 2017 ma, ba a rufe shi na tsawon lokaci haka ba.

Kara karanta wannan

Rana ta 3: Hezbollah ta shigar wa Iran fada, an kashe mutane 31 a harin sama

"Sabon yanayi a masallacin Al-Aqsa"

Wani ma'aikaci a hukumar Wakafi ta Kudus, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa yanayin masallacin yanzu abin takaici ne.

Ya ce an taƙaita yawan masu tsaron masallacin, sannan an hana sauran ma'aikata shiga. Tun ranar Asabar, ba a ba jami'an Wakafi damar kai wa masu tsaron abinci ba.

Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da mazauna Kudus kusan 1,000, ciki har da manyan limamai da ma'aikatan Wakafi 39, aka ba su takardar haramcin shiga masallacin.

Falasdinawa suna korafin cewa Isra'ila na kokarin hana su ibada tare da kwace masallacin Kudu.
Musulmai sun taru a masallacin Kudus (Al-Aqsa) a ranar Juma'a ta biyu ta Ramadan. Hoto: Mostafa Alkharouf/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

Tasirin rufe masallacin ga Musulmai

Ko da yake an taɓa rufe Al-Aqsa lokacin annobar COVID-19 kamar yadda rahoton Daily Sabah ya nuna, amma Falasɗinawa na kallon wannan sabuwar rufewar a matsayin wata dabarar Isra'ila ta hana Musulmai yin ibada a masallacin.

Wannan shi ne karon farko da aka samu tsaiko mai girma a masallacin a watan Ramadan, lokacin da dubun-dubatar Musulmai suka saba taruwa domin yin ibada.

Kara karanta wannan

Iran ta dauki manyan matakai 3 bayan Amurka ta kashe jagoran Musulunci, Khamenei

Yakin da ya barke tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran, ya sa dukkan wurare masu tsarki a yankin Gabas ta Tsakiya cikin yanayi na rashin tabbas.

Kudus: Trump ya juya wa Isra'ila baya

A wani labari, mun ruwaito cewa, Donald Trump ya bayyana adawarsa ga shirin Isra’ila na kara mamaye yankin Yammacin Kogin Jordan da Falasdinawa ke zaune a ciki.

Wani jami’in White House ya ce shugaban kasar Amurka na ganin cewa kwanciyar hankali a Yammacin Kogin Jordan na taimakawa wajen kare Isra’ila.

A cewarsa, duk wani mataki da zai kara tayar da hankali ko dagula al’amura a yankin Kogin Jordan na iya jefa shirin samar zaman lafiya cikin barazana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com