Yakin Iran da Amurka Ya Rutsa da Tsohon Kyaftin Din Najeriya, An Ji Halin da Yake Ciki
- Tsohon kyaftin din Super Eagles, William Troost-Ekong ya makale a kasar Qatar sakamakon yakin da ya barke tsakanin Iran da Amurka, Isra'ila
- Rahotanni sun nuna cewa Ekong da wasu matafiya sun gaza baro Qatar saboda matakin da kasar ta dauka na rufe sararin samaniyarta
- Har kawo yanzu babu wata sanarwa da ke nuna lokacin da mahukunta za su bude sararin samaniya a Qatar domin bai wa jirage damar tashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Qatar - Rahotanni da muka samu sun nuna cewa tsohon kyaftin din tawagar kwalllon kafa ta Najeriya watau Super Eagles, William Troost-Ekong ya makale a kasar Qatar.
Hakan ta faru ne sakamakon rikicin da ya barke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasashen Amurka da Isra'ila, lamarin da ya kai ga harba makamai masu linzami cikin Qatar.

Kara karanta wannan
Iran ce ta kakkabo su? Amurka ta yi magana kan jiragen yakinta 3 da suka fado a Kuwait

Source: Twitter
Tsohon kyaftin din Najeriya ya makale a Qatar
Leadership ta rahoto cewa tsohon kyaftin din Super Eagles, William Troost-Ekong, ya kasa baro Qatar bayan rufe sararin samaniya da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama.
Qatar dai ta rufe sararin samaniyarta ne sakamakon tashin hankalin da ke kara kamari a yankin Gabas ta Tsakiya bayan fara musayar wuta tsakanin Iran, Isra'ila da Amurka.
Bayanai sun nuna cewa Troost-Ekong mai shekaru 32 ya koma kungiyar kwallon kafa ta Al Ahli SC da taka leda bayan ya bar Saudiyya a watan Janairu, 2026.
Halin da Trust-Ekong da wasu matafiya ke ciki
Sai dai sakamakon halin tsaron da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, tsohon kyaftin na Super Eagles da wasu matafiya da dama sun makale a Qatar.
An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da kuma wasannin motsa jiki a Qatar da wasu kasashe yayin da kasashen yankin Gulf ke daukar matakan kariya saboda karuwar hare-haren Iran.

Kara karanta wannan
Bayan kashe 'dan kasarta, China ta maida martani kan yakin Iran da Amurka, Isra'ila
Tashin hankalin ya kara tsananta ne bayan Iran ta kaddamar da hare-hare kan muhimman wurare a matsayin martani ga hare-haren da ta danganta da Amurka da Isra'ila.
Qatar na kokarin kare rayukan jama'a
Ma’aikatar Tsaron Qatar ta tabbatar da cewa tsarin kariyar sararin samaniyarta ya dakile wasu makamai masu linzami, tana mai cewa hakan wani matakin tsaro ne don kare al'umma.
Sakamakon rufe sararin samaniya da ya shafi Qatar da makwabtan kasashe, an ce baki, ’yan wasa da matafiya na harkokin kasuwanci da dama sun makale har sai an dawo da zirga-zirgar jiragen sama yadda ya kamata.

Source: Twitter
Vanguard ta tattaro cewa har yanzu hukumomi ba su fitar da jadawalin lokacin da za a sake bude hanyoyin jiragen sama ko dawo da ayyukan tafiye-tafiye ba.
An kakkabo jiragen Amurka 3 a Kuwait
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Amurka ta tabbatar da cewa jiragenta guda uku sun gamu da tangarda, an kakkabo su bisa kuskure a Kuwait.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Kuwait ta tabbatar da aukuwar lamarin, adaidai lokacin da Iran ke ci gaba da kai farmaki sansanonin sojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.
Rundunar sojin Amurka ta ce dukkan ma’aikatan jirgin guda shida sun yi nasarar ficewa cikin gaggawa, kuma tuni aka dawo da su gida.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng