Bayan Kashe Imam Khamenei, Iran Ta Sake Yin Babban Rashi a Yakinta da Amurka da Isra'ila
- Kwanaki biyu bayan kashe jagoran addinin kasar Iran, Imam Ayatollah Ali Khamenei, matarsa ta riga mu gidan gaskiya a yau Litinin
- Rahotanni sun nuna cewa matar Ali Khameneu, Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh ta rasu ne sakamakon raunukan da ta samu a harin Amurka da Isra'ila
- Wannan dai na zuwa ne bayan harin hadin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka kai birnin Tehran, wanda ya taba ofishin jagoran addinin Iran
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh, matar jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ta rasu sakamakon munanan raunukan da ta samu a hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka kai.
A ranar Litinin, 2 ga watan Maris 2026, aka rawaito cewa ta “samu shahada” bayan hare-haren da aka kai kan Iran.

Source: Getty Images
Rahoton da Hindustan Times ta dauko ya nuna cewa har yanzu ba a samu cikakken tabbaci a hukumance daga Gwamnatin Iran ba.

Kara karanta wannan
Yakin Iran da Amurka ya rutsa da tsohon kyaftin din Najeriya, an ji halin da yake ciki
Amma kafar yada labarai ta gwamnatin Iran ta rawaito cewa Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh ta “samu shahada."
Rahoton rasuwarta na zuwa ne bayan kisan Khamenei mai shekaru 86, a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a ranar Asabar.
Wace ce Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh?
An haifi Mansoureh Khojasteh Bagherzadeh iyali mai bin addinin musulunci a birnin Mashhad, wanda ake cewa shi ne birni na biyu mafi girma a Iran.
Mahaifinta, Mohammad Esmaeil Khojasteh Bagherzadeh, ya kasance fitaccen dan kasuwa a yankin, yayin da dan uwanta, Hassan Khojaste Bagherzadeh, ya taba rike mukamin mataimakin darakta a gidan talabijin na gwamnatin Iran (IRIB).
Ta hadu da Ali Khamenei a karon farko a shekarar 1964 a wani taro na musamman. Sun yi aure a 1965, inda aka ce babban malamin addini Mohammad Hadi Milani ne ya jagoranci daura auren.
Dalilin da ya sa ba a ganin matar Khamenei
Duk da kasancewarta matar daya daga cikin mafi tasiri da karfin iko a Jamhuriyar Musulunci, Bagherzadeh ta kasance mai kauce wa fitowa fili.

Kara karanta wannan
Bayan kashe 'dan kasarta, China ta maida martani kan yakin Iran da Amurka, Isra'ila
Ba kasafai take halartar tarukan gwamnati ba, kuma ta nisanci harkokin siyasa, tana mai mayar da hankali kan harkokin kula da iyalanta da ayyukan addini.

Source: Twitter
Bayanai aun nuna cewa Ita da Imam Khamenei sun haifi ’ya’ya shida, maza hudu da mata biyu, cewar rahoton India TV News.
Tun farko dai an tabbatar da cewa wasu daga cikin iyalan Khamenei na kusa, diyarsa, surukinsa da jikarsa sun mutu a harin da aka kai ofishinsa ranar Asabar.
China ya bukaci a tsagaita wuta a yakin Iran
A wani rahoton, kun ji cewa China ta bukaci kasashen Amurka, Isra'ila da Iran su dakatar da kai wa juna hare-hare, su koma teburin tattaunawa domin a samu sulhu.
China ta nuna damuwa kan rikicin da ke kara zafi a Gabas ta Tsakiya bayan barkewar yaki tsakanin Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Gwamnatin China ta yi gargadi, a makon da ya gabata ga ’yan kasarta, da cewa kada su yi tafiya zuwa Iran a halin yanzu saboda yanayin tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng