Bayan Kashe 'Dan Kasarta, China Ta Maida Martani kan Yakin Iran da Amurka, Isra'ila
- China ta bukaci kasashen Amurka, Isra'ila da Iran su dakatar da kai wa juna hare-hare, su koma teburin tattaunawa domin a samu sulhu
- Ma'aikatar Harkokin Wajen China ta tabbatar da mutuwar dan kasarta guda daya a Tehran sakamakon hare-haren Amurka da Isra'ila
- Martanin China na zuwa ne bayan shiga kwana na uku a yakin da ya barke tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran, wanda ya yi sanadin rasa rayuka
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
China - Kasar China ta nuna damuwa kan rikicin da ke kara zafi a Gabas ta Tsakiya bayan barkewar yaki tsakanin Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A safiyar yau Litinin, China ta yi kira da a tsagaita wuta, a koma kan teburin tattaunawa domin kawo karshen rikicin Gabas ta Tsakiya, yayin da yake shiga rana ta uku.

Source: Getty Images
Tashar NBC News ta tattaro cewa Isra'ila da da Amurka na ci gaba da kai hare-hare kan Iran da Lebanon, inda rikicin ya bazu zuwa makwabtan yankin.
China ta kawo mafita a yakin Iran
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Mao Ning, a taron manema labarai, ta bukaci a warware matsalar da jawo yakin tsakanin kasashen uku ta hanyar tattaunawa da sulhu.
Ning ta ce:
“Mafi muhimmanci a yanzu shi ne tsagaita wuta da kuma hana rikicin yaduwa a Gabas ta Tsakiya."
An kashe 'dan kasar China a Tehran
Ta ce wani 'dan kasar China daya ya mutu sakamakon yakin a Tehran, inda Isra’ila da Amurka ke kai hare-hare a wani samame da aka ce ya yi sanadin mutuwar jagoran Jamhuriyar Musulunci.
“Ma’aikatar harkokin wajen ta umarci ofishin jakadancin China da ke Iran da ya bayar da taimako ga wanda lamarin ya shafa da iyalansa,” in ji Mao, ba tare da karin bayani ba.
Ta kara da cewa tun farko ba a sanar da China shirin Amurka na kai hari ba, tana mai cewa Beijing da Moscow sun bukaci Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da ya kira taron gaggawa.
China ta gargadi 'yan kasarta kan zuwa Iran
Gwamnatin China ta yi gargadi, a makon da ya gabata ga ’yan kasarta, da cewa kada su yi tafiya zuwa Iran a halin yanzu saboda yanayin tsaro, kamar yadda Arab News ta kawo.
Sama da ’yan kasar China 3,000 ne aka ruwaito cewa sun bar kasar Iran zuwa ranar Litinin, 2 ga watan Maria, 2026.

Source: Getty Images
Ana sa rana shugaban Amurka, Donald Trump, zai ziyarci China daga 31 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, 2026, a tafiyarsa ta farko zuwa kasar ta Asiya a zangon mulkinsa na biyu.
Da aka tambaye ta game da ziyarar, Mao ta ce Beijing da Washington “na ci gaba da tuntubar juna kan ganawar shugabannin kasashen biyu,” ba tare da bayar da cikakken bayani ba.
Iran ta yi ikirarin kai hari ofishin Netanyahu
A wani rahoton, kun ji cewa Iran ta ce makaman masu linzami na Kheibar da ta harba sun sauka a ofishin Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da kuma hedkwatar sojin Isra'ila.
Wannan hari, wanda Iran ta kira "rukuni na 10" na hare-hare, ya afku ne a matsayin martani ga kashe jagoran ƙasar Ayatollah Ali Khamenei.
Iran ta kuma bayyana cewa makamin Kheibar yana da ikon ratsa dukkan na'urorin kariya na sararin samaniya, ciki har da na Iron Dome.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


