Yakin Iran da Amurka: Bama Bamai Sun Tarwatse a Dubai da Wasu Kasashe 2
- An ji karar fashe-fashe a biranen Dubai da wasu kasashe 2 a Gabas ta Tsakiya yayin da aka shiga ta na uku ta hare-haren Iran da Amurka
- Akalla mutane hudu ne suka riga mu gidan gaskiya a kasashen UAE da Kuwait sakamakon hare-haren makaman linzamin kasar Iran
- Wannan na zuwa ne yayin da aka rahoto wasu jiragen yakin Amurka sun yi karo da juna a Kuwait, da kuma mutuwar wasu sojojin kasar
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
An ji karar fashe-fashe masu karfi a biranen Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Doha, babban birnin Qatar, a rana ta uku na harin ramuwar gayya da Iran ke kaiwa makwabtanta.
Wannan martani ne ga ci gaba da kai wa Iran hare-hare da Amurka da Isra'ila suke yi a sassan babban birnin Tehran.

Source: Getty Images
Iran ta fadada hare-hare a Gabas ta Tsakiya
Haka kuma, an ji karar harbe-harbe da jiniyar gargaɗi a kasar Kuwait da safiyar Litinin din nan, inda ganau suka shaida wa kamfanin labarai na Reuters cewa an ga hayaki yana tashi kusa da ofishin jakadancin Amurka.
Hukumar tsaron farin kaya ta Kuwait ta bayyana cewa dakarun kariyarsu sun kakkabo mafi yawancin jirage mara matuƙa na Iran a kusa da unguwannin Rumaithiya da Salwa.
A birnin Doha kuma, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Qatar, Majed Al Ansari, ya shaida wa CNN cewa kasarsa ta kakkabo makaman Iran da suka nufi wuraren fararen hula, har da filin jirgin saman kasa-da-kasa.
Ya kara da cewa:
"Mun samu akalla mutane 20 da suka jikkata daga wadannan hare-hare."
Jiragen Amurka sun yi karo a Kuwait
Ma'aikatar tsaron kasar Kuwait ta sanar da cewa wasu jiragen yaƙin Amurka da dama sun fado a kasar, kodayake dukkan ma'aikatan jirgin sun tsira kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.
Hotunan bidiyo sun nuna yadda wani jirgin yaƙi yake fadowa daga sararin samaniya yayin da matuƙin jirgin ya yi nasarar fita ta hanyar amfani da na'urar gaggawa.
Hukumomin Kuwait sun ce an gudanar da aikin ceto tare da haɗin gwiwar Amurka, inda aka garzaya da sojojin zuwa asibiti kuma likitoci sun ce suna samun sauƙi sosai.

Source: Getty Images
Dokar ta-baci a kasar Bahrain
A kasar Bahrain, ma'aikatar cikin gida ta kunna karar gargaɗin harin sama tare da shawartar mazauna kasar da su nemi wuraren tsira, in ji rahoton Iran International.
An rufe gadar Shaikh Khalifa bin Salman da ta hada birnin Manama da wasu garuruwa, sannan ofishin jakadancin Amurka ya gargadi ƴan ƙasarsa da su guji zama a manyan otal-otal domin ana fargabar ƙungiyoyin ta'addanci za su iya kai musu hari.
Wannan rikici ya fara raba mutane da rayukansu, inda aka tabbatar da mutuwar mutum guda a Kuwait, mutane uku a UAE, yayin da mutane 16 suka jikkata a kasar Qatar.
Matsalar da Trump ke fuskanta a yakin Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, bincike ya nuna cewa kashi 27 kacal na Amurkawa ne suka goyi bayan harin da Donald Trump ya kai wa Iran.
Akalla sojojin Amurka uku ne aka kashe yayin da wasu biyar suka jikkata, lamarin da ya sa farin jin Trump ya ragu da kashi 39.
Amurkawa da dama sun bayyana aniyarsu ta janye wa daga goyon bayan Trump kan yaki da Iran idan har wasu abubuwa biyu suka faru.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


