Matsalar da Trump Yake Fuskanta a Amurka bayan Ya Kaddamar da Hare Hare kan Iran
- Sakamakon bincike ya nuna cewa kashi 27 kacal na Amurkawa ne suka goyi bayan harin da Donald Trump ya kai wa kasar Iran
- Akalla sojojin Amurka uku ne aka kashe yayin da wasu biyar suka jikkata, lamarin da ya sa farin jin Trump ya ragu da kashi 39
- Amurkawa da dama sun bayyana aniyarsu ta janye wa daga goyon bayan Trump kan yaki da Iran idan har wasu abubuwa biyu suka faru
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Wani binciken jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a ranar Lahadi ya nuna matsayar wasu Amurkawa game da yakin da Donald Trump yake yi da Iran.
Binciken jin ra'ayin ya nuna cewa kashi ɗaya ne kawai cikin huɗu na Amurka suka amince da hare-haren da Trump ya kai Iran, da ya yi sanadin mutuwar Ayotallah Khamenei.

Source: Getty Images
Matsayar Amurkawa kan yaki da Iran
Kamfanin labaran Reuters/Ipsos ne ya gudanar da binciken, wanda ya tattara ra'ayoyin manyan Amurkawa 1,282 daga faɗin ƙasar.
Binciken ya nuna kashi 27 na waɗanda aka tattauna da su ne suka goyi bayan harin, yayin da kashi 43 suka nuna rashin amincewarsu, sannan kashi 29 ba su da tabbas.
Har ila yau, binciken ya bayyana cewa kusan rabin Amurkawa, har da kashi ɗaya cikin huɗu na ƴan jam'iyyar Republican, na ganin Shugaba Trump ya cika gaggawar yin amfani da ƙarfin soja.
Kusan kashi 90 na Amurkawa sun bayyana cewa sun ji labarin hare-haren da aka fara a safiyar ranar Asabar.
Binciken ya kuma nuna cewa kashi 56 na al'umma na ganin Trump, wanda ya bayar da umarnin kai hare-hare a ƙasashen Venezuela, Siriya, da Najeriya a cikin ƴan watannin nan, yana amfani da ƙarfin soja fiye da kima domin biyan buƙatun Amurka.
An samu asarar rayukan sojojin Amurka
Mafi yawan ƴan jam'iyyar Democrat (87%) na goyon bayan wannan ra'ayi, tare da kashi 23 na ƴan jam'iyyar Republican da kashi 60 na waɗanda ba su da jam'iyya.
An gudanar da wannan bincike ne kafin sojin Amurka su sanar da asarar rayukan sojojinsu na farko a wannan fafatawa.
Aljazeera ta rahoto cewa sojojin Amurka uku sun mutu yayin da wasu biyar suka jikkata sosai, lamarin da ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin wani sabon rikici da ba a san inda ya dosa ba.
Damuwa kan rayuwar sojoji da farashin mai
Duk da cewa kashi 55 na ƴan jam'iyyar Republican sun amince da harin, kashi 42 na mambobin jam'iyyar ta Trump sun ce za su janye goyon bayansu idan har yaƙin ya kai ga kashe sojojin Amurka a yankin.
Farin jinin Trump ya ragu zuwa kashi 39 yanzu, kamar yadda binciken ya nuna.

Source: Facebook
Wannan rikici ya ɓalle ne kwanaki uku kafin zaɓen fitar da gwani na raba-gardama wanda zai nuna ko jam'iyyar Republican za ta ci gaba da riƙe rinjaye a majalisa.
Wani babban abin damuwa shi ne hauhawar farashin man fetur, inda kashi 45 na Amurkawa suka ce ba za su goyi bayan yaƙin ba idan farashin mai ya tashi.
Tuni dai farashin danyen mai na Brent ya tashi da kashi 10 zuwa kusan $80 akan kowace ganga a ranar Lahadi, kuma masana na hasashen zai iya kaiwa $100 sakamakon wannan rikici.
Amurka ta hallaka jagoran addinin Iran
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Iran ta tabbatar da kisan jagoran Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei sakamakon harin hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila.
An kashe jagoran ne a ofishinsa dake rukunin Beit Rahbari yayin da yake gudanar da ayyukansa na yau da kullum a ranar Asabar.
Iran za ta gudanar da zaman makokin kwanaki 40 yayin da Isra'ila ta kaddamar da sababbin hare-hare kan makaman linzamin kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


