Abubuwa 4 da Suka Haddasa Yaki tsakanin Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Abubuwa 4 da Suka Haddasa Yaki tsakanin Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran

A ranar Asabar da ta gabata, 28 ga watan Fabrairun 2026 aka wayi gari da labarin hare-haren hadin gwiwa da kasashen Amurka da Isra'ila suka kai kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wadannan hare-hare sun yi babbar illa a kasar Iran kuma sun ja hankalin kasashen duniya, inda wasu ke goyon bayan matakin Amurka da Isra'ila, wasu kuma ke nuna adawa da hakan.

Jagororin kasashen Isra'ila, Amurka da Iran.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, Shugaba Donald Trump na Amurka da marigayi jagoran addinin Iran, Imam Ali Khamenei Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An kashe jagoran addinin Iran, Ali Khamenei

Rahoton Reuters ya nuna cewa bayan kai wadannan hare-hare, Iran ta dauki matakin ramuwar gayya, inda ta maida martani ta hanyar harba makamai kan sasanonin sojojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya.

Haka zalika, Iran ta kai hare-hare cikin biranen Isra'ila duk a wani mataki na kare kanta da kuma rama barnar da aka mata.

Kara karanta wannan

Yaki ya rincabe a rana ta 4, Iran ta farmaki Amurkawa a Saudiyya

Sai dai duk da kokarin ramuwa da Iran ta yi, Amurka da Isra'ila sun mata barna a hare-haren da suka kai na ranar Asabar, ciki har da kashe jagoran addini, Imam Ayatollahi Ali Khamenei.

Abubuwan da suka haddasa yakin Amurka da Iran

Yayin da kasashen ke ci gaba da musayar wuta, Legit Hausa ta yi duba zuwa ga abubuwan da suka jawo barkewar yaki tsakanin Amurka/Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

1. Murkushe masu zanga-zanga a Iran

Zanga-zangar nuna adawa da matsin tattalin arziki da ta barke a Tehran da matakin da gwamnatin Iran ta dauka na daya daga cikin abubuwan da ake ganin sun fusata Amurka da Isra'ila.

A karshen watan Disamba, 2025 ne wata zanga-zanga ta barke a Tehran, kafin daga bisani ta bazu zuwa sassan kasar, inda ta rikide zuwa babban yunkurin adawa da gwamnati, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta kawo.

Hakan ya sa hukumomin Iran suka kaddamar da shirin dakile lamarin bisa zargin Amurka ke rura wutar zanga-zangar da nufin kawo sauyin gwamnati a kasar.

Masu zanga-zanga.
Yadda wasu yan Iran suka gudanar da zanga-zanga a birnin Tehran Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Cibiyar kare hakkin bil’adama ta HRANA da ke Amurka ta ce sama da mutum 7,000 ne suka mutu, galibinsu masu zanga-zanga, tana mai gargadin cewa adadin na iya zarce haka, tare da kama sama da mutum 53,000.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: Trump ya fadi wasu dalilai 2 da suka sa ya kai hare hare Iran

A nata bangaren, gwamnatin Iran ta amince da mutuwar sama da mutum 3,000, amma ta dora laifin kan “ayyukan ta’addanci” da ta ce Amurka da Isra’ila ne suka shirya.

A ranar 13 ga Janairun 2026, Shugaba Donald Trump ya yi alkawari ga ’yan Iran cewa “taimako na kan hanya,” tare da ba da umarnin girke rundunonin soji mafi girma a yankin Gabas ta Tsakiya.

2. Shirin nukiliyar Iran

Bayan batun zanga-zanga, Amurka ta karkata hankalinta kan shirin nukiliyar Iran, wanda aka jima ana takaddama a kai.

Kasashen yamma sun zargi Tehran da neman kera makamin nukiliya, zargin da Iran ta sha musantawa, tana mai cewa shirinta na samar da ababen more rayuwa ne ga fararen hula.

Amurka na son a haramta duk wani tace sinadarin uranium gaba daya, har ma da wanda ake yi domin ayyukan farar hula, cewar rahoton NBC News.

Khamenei da Trump.
Marigayi jagoran addinin Iran, Imam Ali Khamenei da Shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Washington da Tehran sun fara tattaunawa ta bayan fage a Geneva domin farfado da yarjejeniya kan shirin nukiliyar, inda Shugaba Trump ya yi zargin cewa Iran na shirin kera makaman da za su iya kai hari Amurka.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da musayar wuta, Iran ta samu gagarumin goyon baya a yaki da Amurka da Isra'ila

Tattaunawa kan shirin nukiliyar ya kare ba tare da cimma matsaya ba, bayan da Amurka ta nemi a hada da batun makamai masu linzami da kuma kungiyoyin da Iran ke mara wa baya a yankin.

3. Kera makamai masu linzami

Haka zalika zargin da Amurka ta yi cewa Iran na shirin kera manyan makamai masu linzami da za ta iya kai mata hari kai tsaye na daga cikin abubuwan da suka kara jawo wannan rikici.

Amurka ta nuna takaici bayan Iran ta ki yarda a tattauna kan shirinta na kera makamai masu linzami, wanda Isra’ila ma ta nemi a tattauna batun, tana cewa makaman masu gajere da matsakaicin zango barazana ne kai tsaye ga tsaronta.

Harin makami.
Harin makamai mai linzami a lokacin yakin Isra'ila da Iran Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaba Trump ya ce Iran ta kera makamai da za su iya barazana ga Turai da sansanonin sojin Amurka, yana mai gargadin cewa tana kuma kera makaman da “nan ba da jimawa ba” za su iya kai farmaki kasar.

A rahoton jaridar The Hindu, Iran ta ce ba za ta tattauna kan batun makamai masu linzaminta ba, tana mai jaddada hakkinta na kare kai.

4. Kungiyoyin da Iran ke goyon baya

Kara karanta wannan

Bayan kashe Imam Khamenei, Iran ta sake yin babban rashi a yakinta da Amurka da Isra'ila

Bugu da kari, kungiyoyin da ake zargin Iran na marawa baya kamar Hezbollah a Lebanon, Hamas, mayakan Houthi a Yemen, da wasu kungiyoyin mayaka a Iraki ma cikin abubuwan da suka jawo wannan yaki.

Amurka da Isra’ila dai sun sha alwashin rusa abin da suka kira “axis of resistance” na Iran, wato cibiyar kungiyoyin da take daukar nauyi da makamai.

Trump ya ce za su tabbatar da cewa wadannan kungiyoyi ba za su sake dagula zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya ko kai hari kan sojojinsu ba, in ji rahoton New York Times.

Masoud Pezeshkian.
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump na fuskantar matsala a Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa bincike ya nuna cewa kashi 27 kacal na Amurkawa ne suka goyi bayan harin da Donald Trump ya kai wa kasar Iran.

Binciken ya bayyana cewa kusan rabin Amurkawa, har da ɗaya cikin huɗu na ƴan jam'iyyar Republican, na ganin Shugaba Trump ya cika gaggawar yin amfani da ƙarfin soja.

Amurkawa da dama sun bayyana aniyarsu ta janye wa daga goyon bayan Trump kan yaki da Iran idan har aka ci gaba da kashe sojojin Amurka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262