Iran Ta Karyata Amurka kan Neman Komawa Teburin Tattaunawa bayan Kashe Khamenei
- Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi, ya zargi Amurka da Isra’ila da karya dokokin ƙasa da ƙasa wajen kai mata hari
- Araghci ya bayyana haka ne yayin da kasarsa ke mayar da martani a kan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai kasarsa
- Tehran ta kuma yi martani ga kalaman Shugaban Amurka Donald Trump da ya ce Iran na neman a koma kan teburin tattaunawa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Tehran, Iran – Ministan harkokin wajen ƙasar Iran, Abbas Araghchi, ya yi Allah-wadai da farmakin soji da Amurka da Isra’ila suka kai wa ƙasarsa.
Abbas Araghchi ya bayyana cewa wadannan hare-hare sun keta dokokin ƙasa da ƙasa ne da ya jawo asarar rayuka da dama.

Source: Facebook
CNN ta wallafa cewa a cikin wasiƙar da ya aike wa Majalisar Ɗinkin Duniya, Araghchi ya bayyana harin a matsayin abin da ya sabawa ƙa’idojin da ke jagorantar hulɗar ƙasashe.
Iran ta tsaya kan aniyarta
The Strait Times ta wallafa cewa Amurka da Isra'ila sun kai hari kasarta da gangan, saboda haka ba za ta saurara ba.
Araghchi ya kuma bayyana cewa kashe jagoran addini kuma shugaban koli na Iran, Ali Khamenei, hari ne da zai jawo martani da za a dade ana gani.
Ya sha alwashin cewa waɗanda suka aikata hakan ne kaɗai za su ɗauki cikakken alhakin abin da zai biyo bayan kisan.
A cewar ministan, abin da ya faru ba zai hana Iran amfani da haƙƙinta na kare kanta ba kamar yadda dokokin ƙasa da ƙasa suka tanada.
Babu maganar sasanci in ji Iran
Iran ta bayyana cewa tana da ikon kare kanta kuma za ta yi hakan ba tare da shiga wata tattauna wa ko yarjejeniya da Amurka ba.
Ya ce:
“Wannan ba zai taɓa kawar da haƙƙin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke da shi na kare iko da yancin al’ummarta ba, bisa tanadin Sashe na 51 na yarjejeniyar majalisar 'dinkin duniya.”

Source: Twitter
Sashe na 51 na yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya ya bai wa kowace ƙasa damar kare kanta idan aka kai mata hari.
A wani ɓangare kuma, babban jami’in tsaron Iran ya bayyana cewa Tehran ba za ta shiga wata tattaunawa da Amurka ba yayin da rikicin ke ƙara faɗaɗa.
Ya ce matsayar ƙasar a bayyane take, yana mai jaddada cewa Iran za ta mayar da hankali kan kare kanta da muradunta maimakon shiga tattaunawar siyasa a wannan lokaci.
Dakarun Iran sun shirya daukar fansa
A baya, mun wallafa cewa Iran ta tabbatar da mutuwar jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei, a hare-haren Amurka da Isra’ila da aka kai kasar a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairu, 2026.
Gwamnatin Iran ta ayyana kwanaki 40 na zaman makoki da hutun jama’a bakwai domin jimamin wannan babban rashi da ya same su yayin da jama'a suke cikin bakin ciki.
Rundunar tsaron ƙasar ta IRGC ta yi alkawarin ɗaukar fansa kan waɗanda ta kira “makasan” jagoran addini a Iran, inda ta ce ba za ta saurara wa kowa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

