Amurka da Isra'ila Sun Kashe Jagoran Addinin Musulunci na Iran? Gaskiya Ta Bayyana

Amurka da Isra'ila Sun Kashe Jagoran Addinin Musulunci na Iran? Gaskiya Ta Bayyana

  • An tabbatar da cewa babban jagoran addini na kasar Iran, Imam Ayatollah Khamenei na nan a raye tare da manyan jami'an gwamnati
  • Ministan Harkokin Waje na Iran, Abbas Araghchi ne ya bayyana hakan biyo bayan yakin da ya barke tsakanin kasar da Amurka da Isra'ila
  • Iran ta jaddada cewa za ta dauki matakin kare kanta daga hare-haren Amurka da Isra'ila, inda tuni ta fara harba makamai sansanonin Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Rahotanni sun tabbatar da cewa ana ci gaba da musayar wuta tsakanin kasashen Amurka da Isra'ila da kuma jamhuriyar musulunci ta Iran.

Hakan na zuwa ne bayan Amurka da Isra'ila sun kaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan wasu biranen Iran, lamarin da aka ce ya jawo asarar rayuka da dama.

Ayatollah Khamenei
Jagoran addini na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Imam Ayatollah Khamenei Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar Al-Jazeera ta tattaro cewa Iran ta maida martani ta hanyar harba makamai masu linzami zuwa sansaninin sojin Amurka da ke kasashen Gabas ta Tsakiya kamar Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki a rigimar Iran da Isra'ila, Najeriya ta ba da shawara

Sai dai rahotanni sun cewa hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai sun nufi jagoran juyin juya hali na Iran, Imam Ayatollah Ali Khamenei da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar.

Shin Amurka, Isra'ila sun kashe Imam Khamenei?

Ministan harkokin wajen Iran ya tabbatar da cewa jagoran koli na kasar, Imam Ayatollah Ali Khamenei yana nan a raye, tare da dukkan manyan jami’an gwamnati.

Ya shaida wa NBC News cewa jagoran koli, Ayatollah Ali Khamenei, yana raye “gwargwadon sani na”, a wata hira da ya yi daga Tehran tare da kafar yada labarai ta Amurka.

Abbas Araghchi ya kuma tabbatar wa manema labarai cewa “dukkan manyan jami’ai a gwamnatin Iran suna raye.”

Iran ta tattauna da kasashen yankin Gulf

Araghchi ya ce ya tuntubi kasashen yankin Gulf, inda ya yi masu bayanin cewa Iran ba ta da niyyar kirkirar yaki a tsakaninsu, amma ta kai hari ne kan sasanonin Amurka domin kare kanta.

Ministan ya ce:

“Na tuntubi kasashen da ke makwafata da mu na yankin Gulf kuma na yi musu bayani cewa ba mu da niyyar kai musu hari, amma muna kai hari kan sansanonin Amurka ne a matsayin kare kai.”

Kara karanta wannan

Rasha ta soki Amurka da Isra'ila bayan sun kai farmaki Iran, ta fadi taimakon da za ta kawo

Netanyahu, Trump da Khamnei.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, Shugaba Donald Trump na Amurka da jagoran addinin Iran Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya kara da cewa duk da cewa babu wata hulda da Washington a yanzu, “idan Amurkawa na son tattaunawa da mu, sun san yadda za su tuntube ni. Tabbas muna sha’awar rage zafin rikici.”

Rasha ta yi magana kan rikicin Amurka da Iran

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Rasha ta yi tir da matakin da Amurka da Isra'ila suka daukaNna kaddamar da hare-hare kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Rasha ta yi Allah-wadai da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, tana mai kiran su da “mummunar kasada” da ka iya haddasa “bala’i” a yankin.

Ta ce a shirye take ta bayar da gudummawa wajen nemo mafita ta zaman lafiya wadda ta dogara da dokokin kasa da kasa, mutunta juna, da daidaiton bukatu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262