Rasha Ta Soki Amurka da Isra'ila bayan Sun Kai Farmaki Iran, Ta Fadi Taimakon da Za Ta Kawo

Rasha Ta Soki Amurka da Isra'ila bayan Sun Kai Farmaki Iran, Ta Fadi Taimakon da Za Ta Kawo

  • Kasar Rasha ta yi tir da matakin da Amurka da Isra'ila suka dauka na kaddamar da hare-hare kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Rasha, wacce ke da kyakkyawar alaka da Iran ta ce barkewar yaki tsakanin kasashen na iya yaduwa, ya hana Gabas ta Tsakiya zaman lafiya
  • Gwamnatin Rasha ta bayyana cewa a shirye take ta bada gudummuwa wajen daidaita kasashen domin samar da zaman lafiya da kawo karshen yakin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Moscow, Russia - Kasar Rasha ta nuna damuwarta kan illar da yaki tsakanin kasashen Amurka da Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ka iya haifarwa a Gabas ta Tsakiya da ma duniya baki daya.

Rusha ta yi Allah-wadai da hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, tana mai kiran su da “mummunar kasada” da ka iya haddasa “bala’i” a yankin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta tsoma baki a rigimar Iran da Isra'ila, ta ba da shawara

Shugaban Rasha.
Shugaban kasar Rasha, Viladimir Putin a fadar gwamnatinsa da ke birnin Moscow Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran da ka kyakkyawar alaka da Rasha

A rahotannin kai tsaye da jaridar Al-Jazeera ke daukowa, Rasha ta bukaci duka ’yan kasarta su fice daga Iran da kuma Isra'ila cikin gaggawa.

Tehran ta zama daya daga cikin manyan kawayen Rasha tun bayan kaddamar da farmakin Moscow a kan Ukraine.

Bisa haka ne gwamnatin Rasha ta yi kira da a kwantar da hankali yayin da ake samun karuwar tashin hankali yayin da aka fara samun rahotannin farmakin da Amurka ta kaddamar a Iran.

Abin da Rasha ta ce kan fadan Amurka da Iran

Gwamnatin Rasha ta hannun ma’aikatar harkokin waje ta ce,

“Washington da Tel-Aviv sun sake shiga wata mummunar kasada da ka iya jefa yankin cikin hadarin harkokin jin kai, tattalin arziki, har ma da matsalolin da ba za a iya kauce masu ba.
"Manufar masu kai harin a bayyane take kuma sun bayyana ta karara: rusa tsarin mulkin kasa da kifar da gwamnatin wata kasa da ba sa so, wadda ta ki mika kai ga tilasci da danniyar su.”

Kara karanta wannan

Macron ya fadi shirin da Faransa ke yi bayan Amurka da Isra'ila sun kai wa Iran hari

“Alhakin duk wata mummunar illa da za ta biyo bayan wannan rikicin da aka kirkira da gangan, ciki har da yiwuwar yaduwar tashin hankali da kara tsananta rikici, yana kan su gaba daya.”

Wace gudummuwa Rasha za ta bayar?

Rasha ta ce a shirye take ta bayar da gudummawa wajen nemo mafita ta zaman lafiya wadda ta dogara da dokokin kasa da kasa, mutunta juna, da daidaiton bukatu.

Moscow ta bukaci ’yan kasarta su fice daga Iran, sannan ta fitar da irin wannan gargadi ga ’yan Rasha da ke Isra’ila, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Shugaba Trump.
Shugaban Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A shekarar 2025, Rasha da Iran sun rattaba hannu kan yarjejeniyar kawance ta dabarun siyasa da tsaro domin karfafa alaka, ciki har da bangaren soja.

Shugaban Faransa ya nuna damuwa

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya ce rikici tsakanin Amurka da Isra’ila da Iran na barazana ga zaman lafiya a duniya.

Macron ya ce duk wata arangama kai-tsaye tsakanin waɗannan ƙasashe uku za ta iya haddasa rikici mai faɗi wanda zai shafi yankinBGabas ta Tsakiya da sassan duniya.

Shugaban na Faransa ya jaddada muhimmancin tattaunawa a matsayin hanya mafi dacewa ta warware sabani, yana mai kira ga Amurka, Isra'ila da Iran su koma teburin sulhu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262