Firayim Ministan Birtaniya Ya Yi Magana kan Kama Bature Zai kai Hari Masallaci da Gatari

Firayim Ministan Birtaniya Ya Yi Magana kan Kama Bature Zai kai Hari Masallaci da Gatari

  • Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya yi magana game da wani mutum da aka kama da makami yana shirin shiga masallaci a birnin Manchester
  • Keir Starmer ya bayyana matakan tsaro da za a cigaba da dauka a masallatai domin kare Musulmai masu ibada, musamman a watan Ramadan
  • Jami'an tsaron Birtaniya sun bayyana cewa ana yi wa wanda aka kama tambayoy domin sanin dalilin yunkurin shiga masallaci da makamai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Birtaniya - Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya bayyana damuwa bayan da ake zargin wani bature dauke da makamai ciki har da gatari zai kai hari wani masallaci a birnin Manchester.

An kama wanda ake zargin, mai kimanin shekaru kusan 50 bayan ya shiga masallacin a lokacin da ake yin sallah a watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Wani ya shigo masallaci da makami tsirara, masallata 5000 sun fice ana azumi

Masallacin Manchester da ke Birtaniya
Jama'a a bakin masallacin Manchester. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Arab News ya nuna cewa wanda aka kama yana tare da wani bakar fata lokacin da suka shiga Masallacin Manchester a daren Talata.

’Yan sanda sun kama mutumin bisa zargin daukar makami mai hadari da kuma mallakar miyagun kwayoyi. Har yanzu yana tsare domin ci gaba da yi masa tambayoyi.

Martanin Firaministan Birtaniya, Starmer

Biyo bayan tabbatar da kama wanda ake zargin, Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya rubuta a shafinsa na X cewa:

“Na damu da jin labarin abin da ya faru a Masallacin Manchester Central a daren jiya. Na san wannan zai tayar da hankalin al’ummar Musulmi, musamman a lokacin Ramadan, wanda lokaci ne d ake son zaman lafiya.
“Ina godiya ga masu aikin sa kai da jami’an agajin gaggawa bisa gaggawar da suka yi wajen daukar mataki.

Game da matakan tsaurara tsaro, Keir Starmer ya ce:

“Mun bayar da tallafin har Fam miliyan 40 ($51m) domin ƙarin tsaro a masallatai, makarantun Musulmi da cibiyoyin al’umma, kuma za mu ci gaba da daukar matakai domin tabbatar da cewa al’umma na rayuwa ba tare da tsoro ba.”

Kara karanta wannan

An rikita malaman Musulunci da miliyoyi a Kaduna, sun nuna goyon bayansu ga APC

Firaministan Birtaniya Keir Starmer
Firaministan Birtaniya Keir Starmer yana wani jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayanin 'yan sandan Birtaniya

Da yake magana a wajen masallacin a yammacin Laraba, mataimakin babban jami’in ’yan sanda, John Webster, ya ce:

“A daren jiya, wani lamari mai tayar da hankali ya faru a nan a Masallacin Manchester Central.
“Wani mutum dauke da jaka mai dauke da gatari yana aikata abin da ya jawo zargi a lokacin da daruruwan masu ibada ke sallah...
“Ba a samu wata barazana kai tsaye ba, amma yana da matukar muhimmanci cewa jami’an tsaro da masu aikin sa kai sun yi aiki bisa zarginsu da fahimtarsu wajen kiran mu. Ina gode musu bisa abin da suka yi.”

Malamin Kur'ani ya rasu a Madina

A wani labarin, kun ji cewa wani dan Najeriya mai suna Usama Ahmad Musa ya rasu a Madina, kasar Saudiyya bayan fama da rashin lafiya.

Shugaban gwamnonin jihohin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana rasuwar malamin Kur'anin a matsayin babban rashi ga Musulmi.

Malaman addinin Musulunci da suka hada da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da Sheikh Isa Ali Pantami sun yi ta'aziyyar rasuwar Usama Ahmad.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng