Zargin Kashe Kiristoci: Matakai 6 da Ake Son Trump Ya Ɗauka a kan Najeriya

Zargin Kashe Kiristoci: Matakai 6 da Ake Son Trump Ya Ɗauka a kan Najeriya

  • Majalisar wakilan Amurka ta mika rahoto ga Donald Trump tana neman a dauki matakai masu tsauri domin kare Kiristoci a Najeriya
  • Riley Moore ya ba da shawarar sanya takunkumi da janye wasu tallafi ga Najeriya har sai an soke dokokin batanci da hukuncin kisa
  • Rahoton ya bukaci kafa yarjejeniyar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya domin yaki da kungiyoyin jihadi da ke addabar garuruwan Kiristoci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Majalisar wakilan Amurka ta miƙa wasu manyan bukatu shida a rahoton bincike kan zargin muzgunawa da kashe Kiristoci a Najeriya ga Shugaba Donald Trump.

Rahoton wanda ɗanmajalisa Riley M. Moore ya jagoranci haɗa shi, ya biyo bayan umarnin da Trump ya bayar tun a Oktoban 2025 lokacin da ya sanya Najeriya a jerin ƙasashe masu damuwa na musamman (CPC).

Kara karanta wannan

Kwamitin Amurka ya gama bincike, Shugaba Trump zai dauki matakai masu tsauri kan Najeriya

An bukaci Amurka ta dauki wasu matakai kan Najeriya bayan binciken muzgunawa Kiristoci.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump (hagu) da Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu (dama). Hoto: SAUL LOEB, Ton Molina / Getty Images
Source: Getty Images

An gabatar wa Trump rahoto kan Najeriya

'Dan majalisa, Riley M. Moore ne ya sanar da hakan, a sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, 23 ga Fabrairu, 2026.

Moore ya bayyana cewa rahoton sakamakon bincike ne na watanni da dama, wanda ya haɗa da ziyarar gani da ido da jami'an Amurka suka kawo Najeriya domin tattaunawa da mazauna yankunan da abin ya shafa da kuma jami'an gwamnati.

A cikin sakon, dan majalisar ya ce:

"A yau, dan majalisa, Riley M. Moore ya shiga sahun sauran mambobin kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar wakilai zuwa fadar White House don gabatar da cikakken rahoton da ke kunshe da matakan da za a dauka na kawo karshen muzugunawa Kiristoci a Najeriya da kuma dakile batun tsatstsauran ra'ayi a kasar."

Matakai 6 da ake so Trump ya dauka

Rahoton BBC Hausa ya nuna cewa an gabatar wa gwamnatin Trump jerin matakai masu tsauri da ya kamata ta ɗauka domin kare Kiristocin Najeriya, waɗanda suka haɗa da:

Kara karanta wannan

Amurka ta kawo shawara kan hukuncin wanda ya taba mutuncin Manzon Allah SAW a Najeriya

1. Yarjejeniyar tsaro ta musamman:

Kafa wata yarjejeniyar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya musamman domin kare garuruwan Kiristoci daga harin kungiyoyin mayaƙa masu iƙirarin jihadi.

2. Dakatar da tallafin kuɗi:

Janye wasu tallafi na tattalin arziƙi da na soja da Amurka ke ba Najeriya har sai gwamnatin ƙasar ta nuna jarumta wajen hana muzguna wa Kiristoci.

3. Takunkumi da hana biza:

Sanya tsauraran takunkumi da hana biza ga dukkan ƙungiyoyi ko ɗaiɗaikun mutane da aka samu da hannu wajen tauye ƴancin gudanar da addini a ƙasar.

4. Daƙile ayyukan Fulani masu makami:

Ba gwamnatin Najeriya tallafin gaggawa na fasaha da na soja musamman domin magance hare-haren Fulani masu riƙe da makami.

5. Soke shari'ar Musulunci:

Neman gwamnatin Najeriya ta soke tsarin shari'ar Musulunci da kuma hukuncin kisa kan laifin ɓatanci, waɗanda rahoton ya ce ana amfani da su wajen zalunci.

6. Haɗin gwiwa da kasashen duniya:

Kara karanta wannan

Babban jami'in gwamnatin Amurka zai dura a Najeriya kan batun ta'addanci

Yin aiki tare da manyan ƙasashe irin su Faransa, Hungary, da Birtaniya domin fuskantar wannan matsala ta hanyar diflomasiyya ta bai ɗaya.

Dan majalisar Amurka, Riley M. Moore ne ya jagoranci tattara rahoton muzgunawa Kiristoci a Najeriya.
Dan majalisar Amurka, Riley M. Moore, wanda ya jagoranci tattara rahoton zargin muzgunawa Kiristoci a Najeriya. Hoto: @RepRileyMoore
Source: UGC

'Wahalar da Kiristocin Najeriya ke fuskanta'

A cikin sanarwar tasa, Riley Moore ya jaddada cewa Kiristocin Najeriya sun daɗe suna shan wahala ba tare da sun yi magana ba, amma yanzu duniya tana kallon abin da ke faruwa.

Ya yaba wa Shugaba Trump bisa jajircewarsa wajen sanya ido kan Najeriya, inda ya bayyana cewa wannan matakin zai tilasta wa hukumomi a Najeriya gudanar da gyara cikin gaggawa yau.

"Ina so in sake jaddada godiyata ga Shugaba Trump. Wannan rahoton zai taimaka wajen kare ƴanuwanmu Kiristoci da kuma taimaka wa Najeriya kanta wajen yaƙi da ta'addanci yanzu."

- Riley M. Moore.

Babban jami'in Amurka zai zo Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, wani babban jami’in Amurka, Jonathan Burke, zai ziyarci Najeriya yayin da sojojin kasar nan suka sauka a wasu jihohin Arewa.

Idan Mista Burke ya sauka a kasar nan, ana sa ran za a tattauna kan ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da yaki da yadda ake samun kudi taimakon yan ta'adda.

Ziyarar za ta haɗa gana wa da ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu domin magana kan haɗarin da ke tattare da barin kudi suna shiga hannun bata-gari.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com