Jakadan Amurka Ya Kira wa Trump Ruwa, Kasashen Musulmi Sun Fusata kan Kalamansa
- Kasashen Larabawa da Musulmi sun yi martani bayan kalaman jakadan Amurka a Isra'ila game da mamayar ƙasar a yankin
- Larabawan sun yi tir da kalaman jakadan, Mike Huckabee, kan batun fadada ikon Isra’ila a yankin Gabas ta Tsakiya
- Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) ta bayyana kalaman a matsayin masu hatsari, tana cewa suna saba dokokin kasa da kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Riyadh, Saudi Arabia - Kasashen Larabawa da na Musulmi sun yi Allah-wadai da kalaman da jakadan Amurka a Isra’ila, Mike Huckabee ya yi.
Martanin ya zo ne bayan Jakadan ya yi magana kan batun fadada ikon Isra’ila a yankin Gabas ta Tsakiya.

Source: Getty Images
Kasashen Larabawa sun caccaki jakadan Amurka
Hakan na cikin wata da sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya ta wallafa a shafin X wanda Legit Hausa ta leko.
Sun bayyana kalaman a matsayin barazana ga tsaro da zaman lafiyar yankin, tare da cewa suna iya tunzura rikicin addini da na kasa.
A yayin wata hira, an tambaye shi game da alkawarin Littafi Mai Tsarki na kasa daga kogin Nilu zuwa kogin Yufiretis ga zuriyar Annabi Ibrahim.
Carlson ya bayyana cewa yankin zai hada da Isra’ila, Jordan, Syria, Lebanon da wasu sassan Saudiyya da Iraki.
Da yake mayar da martani, Huckabee ya ce ba lallai ne a kai har wannan nisa ba, amma zai yi kyau idan aka karbe su gaba daya.
Sai dai ya jaddada cewa Isra’ila ba ta neman fadada iyakarta, amma tana da hakkin kare kanta a kasarta da take rike da ita bisa ka’ida.
Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi ta bayyana kalaman a matsayin masu hatsari da rashin daukar alhaki.

Source: Getty Images
Matsalolin da ke cikin kalaman Jakadan Amurka
Kungiyar ta ce kalaman kira ne da ba za a amince da su ba na fadada ikon Isra’ila a matsayin kasa mai mamaya.
Ta kara da cewa sun sabawa ikon kasashe, ka’idojin diflomasiyya, dokokin kasa da kasa da kundin tsarin United Nations.
Kungiyar ta kuma yi gargadin cewa irin wannan tsattsauran ra’ayi na iya karfafa mamayar Isra’ila da kuma kokarin kwace karin yankunan Falasdinawa.
Masar ta ce kalaman sun saba dokokin kasa da kasa, tana mai cewa Isra’ila ba ta da ikon mallakar yankunan Falasdinawa da aka mamaye.
A wata sanarwa ta hadin gwiwa da Saudiyya, Masar da sauran kasashe suka sanya hannu, sun ce kalaman sun saba da shirin zaman lafiya na shugaban Amurka, Donald Trump.
Gumi ya soki Larabawa kan fadan Iran, Isra'ila
An ji cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya zargi wasu daga cikin kasashen Larabawa ke kin tara makaman nukiliya.
Gumi ya bayyana cewa Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya umurci Musulmi da su tanadi makaman zamani masu linzami domin kare kai daga barazana.
Ya yaba wa kasashen Iran da Pakistan bisa yadda suka kera makaman kare kai, yana mai cewa hakan ne ya kamata a yi domin kare rayuwar Musulmi.
Asali: Legit.ng

