Rikicin Kasashen larabawa: Kasashen Larabawa sun yanke hulda da kasar Qatar

Rikicin Kasashen larabawa: Kasashen Larabawa sun yanke hulda da kasar Qatar

- Ana yawan gwabza yaki a kasashen larabawa, inda kowacce kasa ke zabar inda take son mara wa baya

- Arzikin man fetur da albarkatun kasa sun arzurta da yawa daga cikinsu, sun kuma tunzura su yake-yake

- Ana zargin sarkin Qatar da mara wa ta'addanci baya

Kasashen Saudiyya, Masar, Dubai (UAE), da BAhrain sun yanke huldar diplomasiyya da kasar Qatar, bayan da suka zarge ta da mara wa ta'addanci baya, da tunzura 'yan kasarsu kan bore da zafin siyasa, dama aika kudade domin ta'addanci.

Kasar Qatar dai itace mai tashar talabijin ta aljazeera, kuma tayi arziki sosai da man fetur, inda har farkon hawan shugaban Najeriya mulki shekaru biyu da suka gabata, ya kai ziyara can, bayan barin kasar Saudiyya, don neman hadin kai kan batun fitar da mai na kasashen OPEC da ma batun tallafawa da kudade don yaki da barnar ta'addanci.

KU KARANTA KUMA: Matashin kabilar Ibo mazaunin Amurka zai tsaya takarar shugabancin kasa

Rikicin Kasashen larabawa: Kasashen Larabawa sun yanke hulda da kasar Qatar
Rikicin Kasashen larabawa: Kasashen Larabawa sun yanke hulda da kasar Qatar

A watan jiya dai anyi wa kamfanin dillancin labarai na Qatar kutse, an kuma ruwaito wasu zafafan kalamai da aka ce Sheikh Hamad Al-Thani, sarkin kasar ne ya furta su, zargin da ya musanta. Kasar Misra dai ta sha kame wakilan tashar aljazeera bisa zargin zuga bore da ta'addanci, haka ma kasar Amurka.

Sakataren Harkokin wajen Amurka dai Rex Tillerson ya ce a kai zuciya nesa a sasanta a hada kai domin a sami ci gaban da ake da yaki da ta'addanci.

Kasashen larabawa dai sun dade suna kokari iya hada kai, amma jiya i-yau, sai aikin ruguje kasashensu suke da kansu, Isra'ila kuma, ta zuba musu ido tana ciyar da kanta gaba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng