Iran Ta Ki Tsorata Ta Barazanar Trump, Ta Fadi Illar da Za Ta Yi Wa Amurka
- Ana ci gaba da zaman dar-dar kan yiwuwar Amurka ta kai wa Iran hari biyo bayan barazanar da Donald Trump ke ci gaba da yi
- Shugaba Trump dai ya sake yin barazanar cewa Amurka za ta farmaki Iran muddin ba a cimma yarjejeniya ba kan shirinta na nukiliya
- Kasar Iran ta yi martani mai zafi kan barazanar, inda ta bayyana abin da za ta yi muddin Amurka ta kai mata hari
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Iran - Kasar Iran ta yi martani kan barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi ta kai mata hari.
Iran ta yi gargaɗin cewa dukkan sansanonin sojojin Amurka, gine-ginensu da kadarorinsu za su zama “halastattun wuraren kai hari” muddin Amurka ta kai mata hari.

Source: Twitter
Tashar France24 ta ce Amir Saeid Iravani, jakadan Iran a majalisar dinkin duniya ne ya bayyana hakan a cikin wata wasiƙa da ya aika.
Jakadan na Iran ya wasikar ne ga shugaban majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, da kuma shugaban kwamitin tsaro na majalisar.
Trump na yi wa Iran barazana
Shugaba Donald Trump ya tura jiragen yaƙi na ruwa, jiragen yaƙi na sama, da sauran kayan yaƙi zuwa yankin Gabas ta Tsakiya da nufin hana Iran kera makamin nukiliya, abin da mahukunta a Tehran suka ce ba su da niyyar yi.
Wasikar ta yi nuni da wani sako da Trump ya wallafa a kafafen sada zumunta ranar Laraba, inda ya ce Amurka na iya buƙatar yin amfani da sansanonin sojojin Burtaniya (UK), ciki har da wani da ke kan wani tsibiri a Tekun Indiya, "muddin Iran ta ki amincewa da yarjejeniya."
Wane martani Iran ta yi?
Jakada Iravani ya rubuta cewa:
“Irin wannan furuci da Shugaban Amurka ya yi, yana nuna akwai gagarumin haɗarin faruwar kai hari, wanda abin da zai biyo baya zai zama masifa ga yankin kuma zai zama babban barazana ga zaman lafiyar duniya baki ɗaya.”
Ya yi kira ga kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da su tabbatar da cewa Amurka ta daina barazanar yin amfani da karfin soja ba tare da bin ka’ida ba, tashar TRT World ta kawo labarin.
Wasiƙar ta kara da cewa Iran tana nan daram kan tsarin diflomasiyya domin warware saɓani game da shirinta na nukiliya, muddin za a yi hakan cikin girmama juna.
Amma Iravani ya yi gargaɗin cewa idan har aka kai wa Iran hari, to dukkan sansanonin sojojin ƙasar da ta kai harin a yankin za su fuskanci martani.
Trump ya sha barazanar kai hari ga Iran
Trump dai ya sha yin barazanar kai wa Iran hari, inda ya dogara da zargin murƙushe masu zanga-zangar adawa da gwamnati da aka yi a watan jiya, da kuma batun shirinta na nukiliya.

Source: Facebook
A ranar Alhamis ma, Trump ya ce Iran tana da kwanaki 15 kacal don cimma yarjejeniya, inda ya sake nanata cewa Amurka za ta kai hari idan ba a yi hakan ba.
Wannan furuci nasa ya zo ne bayan tattaunawar da aka yi a Geneva ranar Talata tsakanin wakilan Amurka, Steve Witkoff da surukin shugaban kasa Jared Kushner, waɗanda suka gana (ba kai-tsaye ba) da babban jami’an diflomasiyyar Iran, wanda ya ce an samu ci gaba a tattaunawar.
Burtaniya ta watsawa Trump kasa a ido
A wani labarin kuma, kun ji cewa Burtani ta ki amincewa da bukatar Donald Trump ta yi amfani da daya daga cikin sansanoninta domin yiwuwar kai wa Iran hari.
Amurka na son yin amfani da sansanin rundunar sojojin saman Birtaniya (RAF) da ke Fairford a Ingila, wanda ke zama cibiyar manyan jiragen yaƙin Amurka a Turai.
Jami’an Birtaniya sun nuna damuwa cewa bai wa Amurka izinin amfani da sansanonin RAF domin kai hari zai iya karya dokokin kasa da kasa
Asali: Legit.ng


