Magana Ta Girma: Trump Ya Yi wa Iran Gagarumar Barazana, Ya ba Ta Wa’adin Mako 2

Magana Ta Girma: Trump Ya Yi wa Iran Gagarumar Barazana, Ya ba Ta Wa’adin Mako 2

  • Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ba ƙasar Iran wa’adin kwanaki 10 zuwa 15 game da yarjejeniyar da suke shirin kullawa
  • Trump ya ce idan tattaunawa ta gaza, sakamakon zai kasance “mafi muni” ga Iran, yana mai jaddada cewa dole ne a samu mafita ta kowace hanya
  • Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce an samu ci gaba amma ba za a kai ga matsaya cikin gaggawa ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake yin gagarumar barazana ga kasar Iran kan yarjejeniyarsu.

Donald Trump ya bayyana cewa ƙasar Iran na da kwanaki 10 zuwa 15 kacal domin cimma yarjejeniya da Amurka.

Trump ya sake yi wa Iran barazana
Shugaba Donald Trump da Ayatullah Ali Khamenei. Hoto: @khamenei_ir, @RealDonaldTrump.
Source: Getty Images

Yarjejeniyar da Trump da Iran ke neman kullawa

Trump ya yi wannan jawabi ne yayin da yake cikin jirgin sama, yana mai gargadin cewa lokaci na kurewa matuƙa, cewar Fox News.

Kara karanta wannan

Trump ya sha kunya a hannun Birtaniya da ya zabura zai kai hari Iran

Tattaunawar dai ta fi mayar da hankali kan shirin nukiliyar Iran wanda jami’an Amurka suka ce ya kusanci matakin kera makamin nukiliya.

Amurka da Isra’ila suna son Iran ta dakatar da makamai masu linzami masu dogon zango tare da daina tallafa wa ƙungiyoyin yankin Gabas ta Tsakiya.

Trump ya ce:

“Za mu samu yarjejeniya ko ta halin ƙaƙa,” yana nuna cewa gwamnatinsa ba za ta sassauta ba."
Trump ya ba Iran wa'adin mako 2 kan yarjejeniyarsu
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Donald J Trump.
Source: Getty Images

Barazanar da Trump ya yi ga Iran

Sai dai ya ƙi bayyana ko rushe gaba ɗaya shirin nukiliyar Iran ne babban burin tattaunawar duba da yadda alakarsu ke kara tsami a kullum.

Donald Trump ya kuma jaddada cewa idan diflomasiyya ta gaza, sakamakon zai zama abin takaici ga Iran domin za su fuskanci ukuba wanda ba su yi tsammani ba.

Iran ta yi martani ga barazanar Trump

A nasa ɓangaren, Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar Geneva.

Araghchi ya ce hanya ta fara buɗewa ta yarjejeniya, amma ya yi gargadin cewa ba za a kai ga matsaya cikin sauri ba domin tabbatar da yin haka cikin natsuwa.

Kara karanta wannan

Manya sun fara nuna damuwa da jibge sojojin Amurka da aka soma a Najeriya

Rahotanni sun ce Iran na nuna ƙin amincewa da wasu buƙatun Amurka da Isra’ila, musamman batun makamai masu linzami.

A lokaci guda, jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, ya yi gargadin daukar matakin soja duk da ci gaba da tattaunawa, cewar rahoton Forbes.

Maganganun Trump sun zo ne yayin da Iran ke gudanar da atisayen soja tare da Rasha, yayin da jiragen ruwan Amurka ke matsawa yankin.

Trump na neman ganin bayan Khamenei

Kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya magantu kan tsarin mulki da ake bi a Iran inda ya bayyana damuwa game da haka da neman kawo sauyi.

Amurka na kara matsin lamba kan Tehran tare da tura jirgin ruwan yaki USS Gerald R. Ford zuwa Gabas ta Tsakiya domin tabbatar da ikonta a yankin.

Iran ta ce ba za ta amince da bukatun da ta kira masu tsauri ba, duk da tattaunawar yarjejeniyar nukiliya da ke gudana a tsakaninsu na tsawon lokaci zuwa yanzu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.