Trump Ya Sha Kunya a Hannun Birtaniya da Ya Zabura zai kai Hari Iran
- Rahoto ya nuna cewa Birtaniya ta hana kasar Amurka amfani da sansanoninta wajen kai hari Iran saboda wasu manyan dalilai
- Legit ta gano cewa an tattauna batun tsakanin Donald Trump da Keir Starmer, kuma jami’an Birtaniya sun nuna damuwa kan hakan
- Hakan na zuwa ne yayin da shugaba Donald Trump ya dage cewa sai ya kai hari Iran, ita kuma na cewa za ta yi martani nan take
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Britain - Birtaniya ta hana Donald Trump amfani da sansanonin sojinta domin yiwuwar kai hari Iran, sakamakon fargabar cewa irin harin zai iya saɓa wa dokar ƙasa da ƙasa.
An ruwaito cewa Shugaba Donald Trump ya tattauna da Firaministan Birtaniya, Keir Starmer, a ranar Talata game da shirin kai hari Iran.

Source: Getty Images
Rahoton jaridar the Times ya bayyana cewa Amurka na shirin amfani da sansanin rundunar sojin saman Birtaniya (RAF) da ke Fairford a Ingila, wanda ke zama cibiyar manyan jiragen yaƙin Amurka a Turai.
Barazanar Donald Trump ga kasar Iran
A ranar Laraba, 19 ga Fabarairun 2026 Donald Trump ya sake barazanar cewa zai kai hari Iran idan ta ki kulla yarjejeniya da shi.
Fox News ta rahoto ya ce:
“Idan Iran ta yanke shawarar ƙin kulla yarjejeniya, zai iya zama dole Amurka ta yi amfani da Diego Garcia da kuma filin jirgin saman da ke Fairford domin kawar da yiwuwar hari."
Ya ƙara da cewa:
“Hari wanda zai iya shafar Birtaniya da sauran ƙasashe abokan hulɗa. Za mu kasance a shirye ko yaushe mu kare Birtaniya, amma dole su tsaya da ƙarfi wajen fuskantar sauran matsalolin da ke gabansu.”
A ranar Alhamis, Trump ya shaida wa manema labarai cewa Iran na da wa’adin kwanaki 15 kacal domin ta cimma yarjejeniya, in ba haka ba abin zai zama mai muni a gare su.
Birtaniya ta ba Trump kunya
Sai dai jami’an Birtaniya sun nuna damuwa cewa bai wa Amurka izinin amfani da sansanonin RAF domin kai hari zai iya karya dokokin ƙasa da ƙasa.
A halin yanzu, akwai saɓani tsakanin Washington da Landan kan amfani da sansanonin Birtaniya. Bisa yarjejeniyoyi na dogon lokaci da ke tsakaninsu.
Wani rahoto ya nuna cewa ba za a iya amfani da sansanonin wajen kai hari kan wata ƙasa ba sai da amincewar gwamnatin Birtaniya.

Source: Getty Images
Sanata Lindsey Graham daga Amurka kuma ya ce amfani da sansanonin sojin Birtaniya domin kai hari Iran abu ne da ya zama wajibi, yana mai cewa zai yi matuƙar mamaki idan hakan bai faru ba.
Matakin Trump ya jefa 'yan Yobe a matsala
A wani labarin, mun kawo muku cewa matakan da Donald Trump ya dauka na dakatar da tallafin USAID ya jefa dubban jama'a a matsala a Yobe.
Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar ya bayyana cewa mutane da dama, musamman mata da yara na fuskantar barazanar abinci bayan janye tallafin.
Ya kara da cewa Amurka na cikin manyan masu bayar da tallafin kayan abinci da sauran fannoni a jihohin Yobe, Borno da Adamawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


