Trump Ya Taso Ali Khamenei a Gaba, Ya Tabo Batun Tuge Shi a Jagorancin Iran

Trump Ya Taso Ali Khamenei a Gaba, Ya Tabo Batun Tuge Shi a Jagorancin Iran

  • Shugaban Amurka, Donald Trump, ya magantu kan tsarin mulki da ake bi a Iran inda ya bayyana damuwa game da haka
  • Amurka na kara matsin lamba kan Tehran tare da tura jirgin ruwan yaki USS Gerald R. Ford zuwa Gabas ta Tsakiya
  • Iran ta ce ba za ta amince da bukatun da ta kira masu tsauri ba, duk da tattaunawar yarjejeniyar nukiliya da ke gudana

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana game da abin da ke faruwa a kasar Iran da Ali Khamenei.

Trump ya bayyana cewa sauyin mulki a kasar Iran shi ne “mafi alherin abin da zai iya faruwa,” yana mai nuna goyon bayansa ga maye gurbin shugabancin malaman addini.

Trump ya magantu kan sauyin gwamnatin Iran
Shugaba Donald Trump da Ayatullah Ali Khamenei. Hoto: @khamenei_ir, @RealDonaldTrump.
Source: Getty Images

Trump na bukatar sauyin gwamnati a Iran

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gano talakawan da suka fi bukatar taimako a Najeriya

Trump ya ce tsawon shekaru 47 ana ta magana ba tare da cimma matsaya ba, yana mai cewa hakan ya jawo asarar rayuka masu yawa, sai dai bai fadi wanda yake son ya jagoranci Iran ba, cewar France 24.

Shugaban addinin Iran, Ali Khamenei, bai mayar da martani kan kalaman ba, yayin da Amurka ke kara matsin lamba kan Tehran domin cimma sabuwar yarjejeniyar nukiliya.

Trump ya sanar da cewa jirgin ruwan yaki mafi girma na Amurka, USS Gerald R. Ford, zai koma Gabas ta Tsakiya nan ba da jimawa ba, inda USS Abraham Lincoln tuni yake aiki.

Ya ce:

“Tsawon shekaru 47 suna ta magana suna maimaita magana ba tare da tsayawa ba, a wannan lokacin kuwa, mun yi asarar rayuka da dama.”
Trump na neman ganin bayan tsarin mulki da ake yi a Iran
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Donald J Trump.
Source: Getty Images

Abin da Amurka ke bukata daga Iran

Gwamnatin Amurka na bukatar Iran ta dakatar da tace sinadarin uranium, yayin da gwamnatin Isra’ila karkashin Firayim Minista Benjamin Netanyahu ke neman Tehran ta daina shirin makamai masu linzami.

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya gargadi cewa kasarsa ba za ta mika kai ga bukatun da ya kira masu wuce gona da iri ba, duk da yiwuwar rage ayyukan nukiliya domin sassauta takunkumi.

Kara karanta wannan

'Daga Allah ne': Fasto ya gina makeken masallaci, ya tabo batun shiga Musulunci

A baya, Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar zamanin Barack Obama tare da dawo da takunkumi da suka yi illa ga tattalin arzikin Iran, cewar BBC.

Gwamnatin da ke kan mulki a yanzu ta sake farfado da tattaunawa a bara domin cimma sabuwar yarjejeniya kafin barkewar yakin kwanaki 12 tsakanin Isra’ila da Iran

Amurka ta yi magana kan zanga-zanga a Iran

A baya, mun ba ku labarin cewa majiyoyi sun fito game da yadda kasar Amurka ta jawo karancin Dala a Iran domin tunzura jama'a su cika titunan kasar da zanga-zanga.

Ministan tattalin arzikin kasar Amurka, Scott Bessent ne ya fito da wasu bayanai game da zanga-zangar da aka yi a Iran da ta dauki hankali da kuma jawo asarar dukiyoyi a kasar.

Shugaba Donald Trump ya sha yin gargadi ga kasar Iran a lokacin zanga-zangar, yana mai cewa zai kai dauki idan aka aka kashe matasa a kasar ba tare da alhakinsu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.