Ramadan 2026: Jerin Kasashen Duniya 4 da Suka Faɗi Ranar da Za a Fara Azumi
- Oman da wasu kasashen duniya uku sun tabbatar da cewa za a fara azumin watan Ramadana na shekarar 2026 a ranar Alhamis
- Hasashen masu ilimin taurari ya nuna cewa ba zai yiwu a ga jinjirin watan Ramadan ba a ranar Talata a yawancin kasashen duniya
- Za a iya samun bambancin ranar fara azumi sakamakon hanyoyin da ake amfani da su wajen tabbatar da shigar wata a kasashe
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yayin da watan Ramadan na 2026 yake ƙara karatowa, musulmi a sassan duniya sun fara shirin azumi da ayyukan jinkai da ibadu na musamman.
Hasashen kimiya na farko-farko ya nuna cewa watan na iya farawa a ranar 18 ko 19 ga watan Fabrairu, 2026 amma hakan ya dogara da ganin jinjirin wata.

Source: Getty Images
Hukumomin addini a kasashen musulmi daban-daban sun fara fitar da rahotannin kimiya waɗanda ke nuna yiwuwar ranar da za a fara azumin watan Ramadan na bana, in ji rahoton Gulf News.

Kara karanta wannan
Ramadan na karatowa, za a yi gyaran iskar gas da zai rage wutar lantarki a Najeriya
Hasashen ganin watan ramadan 2026
A ranar Talata, 17 ga Fabrairu, yawancin ƙasashen Musulmi za su duba wata, amma binciken kimiya na nuna cewa ba za a iya ganin jinjirin watan Ramadan a ranar ba.
A cewar Ƙungiyar Masana Taurari ta Hadaddiyar Daular Larabawa (EAS), ana sa ran za a “haifi” jinjirin watan Ramadan ne ranar Talata, 17 ga Fabrairu, 2026, da misalin karfe 4:01 na yamma agogon UAE.
Sai dai shugaban kwamitin gudanarwar ƙungiyar, Ibrahim Al Jarwan, ya bayyana cewa ana sa ran watan zai fadi ne minti guda kacal bayan faduwar rana a ranar Talata, lamarin da zai sa ba zai yiwu a gan shi da ido ko ma da na’urar hangen nesa ba.
Sakamakon haka, ana sa ran Laraba, 18 ga Fabrairu, za ta kasance ranar karshe ta watan Sha’aban, wanda hakan zai sa a fara azumin watan Ramadan ranar Alhamis, 19 ga Fabrairu, in ji rahoton Economy Middle East.
Kasashen da suka ayyana ranar fara azumi
Wasu ƙasashe da dama sun riga sun fitar da sanarwar ranar da za su fara azumin watan Ramadan na wannan shekarar domin jama’a su shirya.
Ga jerin ƙasashen da suka riga sun bayyana ranar fara azuminsu:
- Oman: Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026
- Turkiyya: Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026
- Singapore: Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026
- Australia: Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026

Source: Getty Images
Me yasa ranar fara zumi ke bambanta?
Ana samun bambancin ranar fara azumi a ƙasashen duniya ne sakamakon hanyoyin da hukumomin addini suke amfani da su wajen tabbatar da shigar wata.
Wasu kasashen suna dogara ne kawai kan ganin wata da ido, yayin da wasu kuma suke amfani da na'urorin zamani da lissafin kimiya na zamani, cewar rahoton Khaleej Times.
Wannan ya sa a kowace shekara ake samun bambancin kwana ɗaya a wasu lokutan tsakanin ƙasashen Larabawa da sauran sassan duniya baki ɗaya.
Manyan malaman addini sun yi kira da a girmama ra'ayoyin kimiya da na shari'a domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan al'ummar musulmi a duk inda suke a duniya.
Ramadan: Ranar fara duba wata a Saudiyya
A wani labari, mun ruwaito cewa, Saudiyya ta bukaci musulmi da su fara duba jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Talata, 17 ga watan Fabrairu, 2026.
Idan har an ga watan a ranar Talata, to za a fara azumin Ramadan ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairu, kamar yadda sanarwa ta nuna.
Idan ba a ga watan ba, to watan Sha'aban zai cika kwanaki 30, sannan a fara azumin Ramadan a ranar Alhamis, 19 ga watan na Fabrairu.
Asali: Legit.ng

