Ministan Trump Ya Fallasa Yadda Suka Shirya Rikita Iran da Zanga Zanga

Ministan Trump Ya Fallasa Yadda Suka Shirya Rikita Iran da Zanga Zanga

  • Rahotanni sun fito game da yadda kasar Amurka ta jawo karancin Dala a Iran domin tunzura jama'a su cika titunan kasar da zanga-zanga
  • Ministan tattalin arzikin kasar Amurka, Scott Bessent ne ya fito da wasu bayanai game da zanga-zangar da aka yi a Iran da ta dauki hankali
  • Shugaba Donald Trump ya sha gargadi ga kasar Iran a lokacin zanga-zangar, yana mai cewa zai kai dauki idan aka aka kashe matasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Ministan tattalin arzikin Amurka, Scott Bessent, ya yi ikirarin cewa Washington ta ƙirƙiro ƙarancin Dala a Iran domin ta jefa kudin kasar cikin mummunar faɗuwa tare da haifar da zanga-zanga a kan tituna.

A Disamban 2025 da Janairun 2026, Iran ta fuskanci ɗaya daga cikin manyan zanga-zangar adawa da gwamnati tun bayan juyin juya halin Musulunci na shekarar 1979 sakamakon kalubalen tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Ramadan na karatowa, za a yi gyaran iskar gas da zai rage wutar lantarki a Najeriya

Donald Trump da wasu 'yan kasar Iran
Shugaba Donald Trump da wasu 'yan kasar Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al-jazeera ta rahoto cewa zanga-zangar adawa da tashin farashi a Iran ta fara ne da ‘yan kasuwa a Tehran da suka rufe shaguna suka fara zanga-zanga a ranar 28 ga Disamba, 2025.

Magana kan karancin dala

Ƙarancin dala na nufin yanayin da wata ƙasa ba ta da isassun Dalar Amurka domin biyan kuɗin abubuwan da take saye daga sauran ƙasashen duniya.

Dalar Amurka ita ce babbar kuɗin da ake amfani da ita a cinikayyar duniya, musamman wajen saye da sayar da mai, injuna da biyan bashin ƙasashe, wanda hakan ke nufin dole ƙasashe su kasance suna da wadatacciyar Dala.

Idan fitar da kaya ya ragu a kasa kuma takunkumin tattalin arziki ya hana ta samun damar shiga tsarin kuɗi na Amurka, Dala na iya yin ƙaranci.

Rahotanni sun nuna cewa sakamakon haka, kuɗin kasar zai rage daraja, farashin kayayyakin shigo da su ya tashi, kuma hauhawar farashi ya ƙaru.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Tinubu na shirin sayar da manyan kadarorin Najeriya

An samar da karancin Dala a Iran

Masanin tattalin arziki a Jami’ar Marburg ta Jamus, Mohammad Reza Farzanegan ya ce an ƙirƙiri ƙarancin Dala a Iran ne ta toshe manyan hanyoyi biyu na shigar kuɗin ƙasashen waje kasar.

A cewarsa, hanyoyin su ne fitar da mai zuwa ketare da kuma hana damar shiga tsarin bankunan ƙasa da ƙasa da aka kakabawa Tehran.

Amurka ta yi hakan ne ta hanyar kakaba takunkumi kan man Iran, wanda ke nufin duk wanda ya saya ko ya sayar da shi zai fuskanci hukunci.

Abin da Amurka ta ce da kanta

Da yake amsa tambaya kan yadda za a tafiyar da lamura da Iran a zaman majalisa a makon da ya gabata, Bessent ya bayyana dabarar Amurka ta jefa Iran a matsala.

“Abin da muka yi a Baitulmali shi ne ƙirƙirar ƙarancin dala a ƙasar,”

in ji Bessent, yana mai ƙarawa da cewa dabarar ta kai:

Kara karanta wannan

Masu zanga zanga sun mamaye Majalisar Dattawan Najeriya, sun bayyana bukatarsu

“Kololuwar nasara a watan Disamba, lokacin da ɗaya daga cikin manyan bankunan Iran ya rushe … kuɗin Iran ya faɗi, hauhawar farashi ya karu, kuma hakan ya sa muka ga al’ummar Iran sun fito kan tituna.”

Kafin wannan, yayin wata hira da Fox News a taron tattalin arziki na duniya da aka yi a Davos, Bessent ya bayyana rawar da takunkumin Amurka ya taka wajen tayar da zanga-zangar da ta bazu a Iran.

'Yan Iran masu adawa da Donald Trump
Yadda mutanen Iran suka nuna adawa da Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sojan Amurka ya rasu a teku

A wani labarin, kun ji cewa rundunar sojin ruwan Amurka ta tabbatar da rasuwar wani jami'inta dan asalin Najeriya a cikin teku.

Rahotanni sun nuna cewa an tabbatar da mutuwar sojan ne bayan shafe lokaci ana neman shi a teku da jirage amma ba a gan shi ba.

Rundunar ta bayyana cewa za a cigaba da tunawa da jajircewar da ya yi wajen kawo cigaba a dukkan ayyukan da aka sa shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng