Bidiyo: Yadda Jirgin Sama Ya Rikito Kasa, Ya Fada kan Motoci a Babbar Hanya
- Wani matuki da dalibinsa sun tsira daga mutuwa bayan karamin jirginsu ya yi hatsari a kan babbar hanya a jihar Georgia
- Matukin jirgin Thomas Rogers ya yi ban kwana da iyalinsa ta hanyar aika sakon murya bayan ya fahimci cewa injin jirgin ya daina aiki
- Wani bidiyo da Legit Hausa ta gani ya nuna yadda jirgin ya fada kan babbar hanya, ya rika karo da motoci yana neman gun tsayawa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Georgia - Mutane biyu da ke cikin wani ƙaramin jirgi sun tsira bayan jirgin ya rikito daga sama ya fada kan wata babbar hanyar mota a Georgia, a ranar 9 ga Fabrairu, 2026.
A ranar Litinin, 9 ga Fabrairu, wani jirgi mai inji ɗaya ya yi "sauƙar gaggawa" kusa da wata mahaɗar hanya a Browns Bridge Road dake Gainesville inda ya faɗa kan motoci da dama.

Kara karanta wannan
Hankali ya tashi: NSIB ya fitar da jawabi da jirgi ya samu matsala a sararin Samaniya

Source: Instagram
Yadda jirgi ya fada kan babbar hanya
A cewar rahotanni daban-daban, ciki har da na gidajen talabijin na FOX 5 da WSB, jirgin ya fuskanci matsalar inji ne jim kaɗan bayan ya tashi daga filin tashi da sauka na Lee Gilmer Memorial.
A cikin jirgin akwai matuƙi da kuma ɗalibin da yake koyon tuƙi a lokacin da wannan mummunan lamari ya faru
"Muna tashi daga Gainesville injinmu ya mutu, mun yi ƙoƙarin ganin ya tashi a sararin samaniya, mun yi komai kamar yadda littafin ƙa'ida ya tanada, amma mun fahimci ba za mu iya ko da komawa inda muka tashi ba saboda nisan da muke da shi, shi ya sa muka sauka a kan hanya," in ji Thomas Rogers.
Thomas Rogers, wanda shi ne ke tuƙin jirgin, ya bayyana cewa ya yi ƙoƙarin komawa filin jirgin lokacin da injin ya fara ba su matsala, amma ya rasa dukkan ikon sarrafa injin.
Sakon ban kwana mai ban tsoro
A cikin wani sautin murya na sadarwar sararin samaniya, an ji Rogers yana ban kwana da iyalinsa, yana tsoron cewa ba zai tsira daga wannan hatsari ba.
“Ba za mu iya kaiwa ba,” in ji shi a kiran.
Ya kara da cewa:
“Don Allah a gaya wa matata, Molly, ina ƙaunarta ... da iyayena. Ina ƙaunarsu sosai.”

Source: Instagram
Mutane sun ga faduwar jirgin saman
Wani bidiyon da shaidun gani da ido suka ɗauka ya nuna yadda jirgin ya fada kan babban titin kafin ya riƙa hankadar motoci tare da yin babakere a tsakiyar ababen hawa.
Sauran motoci sun riƙa kaucewa da sauri domin guje wa karo da jirgin a kan hanyar, kamar yadda aka gani a bidiyon da ABC 7 ya wallafa a shafinsa na YouTube.
Abin mamaki shi ne, jirgin motoci uku kawai ya yi karo da su, in ji Kyaftin Kevin Holbrook, inda ya ƙara da cewa rashin samun asarar dukiya ko rai wani babban abin mamaki ne.
Kalli bidiyon hatsarin jirgin a nan kasa:
Jirgin Arik Air ya samu matsala a samaniya
A wani labari mun ruwaito cewa, jirgin saman Arik Air ya yi saukar gaggawa a Benin City bayan samun matsalar inji yayin da yake kan hanyar zuwa Fatakwal.
Kamar yadda rahoto ya nuna, masana kanikanci za su tantance jirgin samfurin Boeing kafin ya koma aiki domin tabbatar da tsaro da kiyaye rayukan fasinjoji.
Hukumar da ke binciken hadurra ta Najeriya (NSIB) ta fitar da sanarwa game da halin da fasinjoji 80 da ma'aikatan jirgin suke ciki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

