Zargin Kashe Kiristoci: Amurka Ta Taso Kwankwaso da Ƙungiyoyin Fulani a gaba

Zargin Kashe Kiristoci: Amurka Ta Taso Kwankwaso da Ƙungiyoyin Fulani a gaba

  • Wasu 'yan majalisar dokokin Amurka sun gabatar da kudirin dokar takunkumi kan wasu ’yan Najeriya da kungiyoyi
  • Wannan mataki ya biyo bayan zargin da kasar ke yi na cewa ana kashe mabiya addinin kirista da zummar kawar da su
  • Sabon kudirin da aka gabatar na neman a kakaba takunkumi da daskarar da kadarori tare da hana wasu 'yan siyasa da kungioyi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States of America – ’Yan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore da Chris Smith, sun gabatar da wani kudirin doka mai suna Nigeria Religious Freedom and Accountability Act of 2026.

A cikin wannan sabon kudiri, 'yan majalisa sun bayar da shawarar kakaba takunkumi kan wasu ’yan Najeriya da kungiyoyi.

Yan majalisar Amurka sun sako Kwankwaso a gaba
Dan majalisa, Riley Moore da Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: RMKwankwaso/RepRileyMoore
Source: Twitter

'Dan majalisa, Riley Moore ya tabbatar da gabatar da kudirin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya bayyana farin ciki da samun nasarar gabatar da kudurin.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Tinubu na shirin sayar da manyan kadarorin Najeriya

Majalisar Amurka ta gabatar da kuduri kan Najeriya

Arise TV ta wallafa cewa kudurin ya ba da shawarar a kakaba takunkumi na musamman, da suka hada da daskarar da kadarori da hana biza ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Haka kuma yan majalisar sun nemi a yi irin wannan hukunci a kan kungiyar MACBAN, Miyetti Allah Kautal Horé da kuma abin da suka kira Kungiyoyin makiyaya Fulani masu yawo dauke da makamai.

Riley Moore ya nemi tallafin kasashen Turai a kan Najeriya
Riley Moore, 'dan majalisar dokokin Amurka Hoto: Rley Moore
Source: UGC

Moore ya yi zargin cewa mutanen da kungiyoyin da aka ambata suna da alhakin take hakkin ’yancin addini a Najeriya.

Kudirin ya kunshi alkaluma da bayanan tarihi kan hare-haren da aka kai wa Kiristoci, da kuma Musulman 'da ke goyon bayan zaman lafiya a tsakanin addinai.'

'Yan majalisar Amurka sun sake sukar Najeriya

’Yan majalisar sun zargi gwamnatin Najeriya da gazawa wajen gurfanar da masu aikata ayyukan ta’addanci da 'jihadi' ga hukuma domin a hukunta su.

Sun ce akwai bukatar hadin kan kasashen duniya domin tabbatar da an hukunta wadanda ake zargi.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun riƙewa minista wuta a kan 'bacewar' kayan Gwamnatin Tarayya

Sun bukaci kasashe irin su Faransa, Birtaniya da Hungary su ba da goyon baya wajen tabbatar da an dauki matakin da ya dace kan masu aikata laifuffukan da suka shafi take hakkin addini.

Har ila yau, kudirin dokar na neman a gudanar da bincike kan zargin tilasta wa wadanda ba Musulmai ba bin dokokin Shari’a ko na batanci.

Daga cikin sunayen da aka ambata a matsayin wadanda abin ya shafa akwai Rhoda Jatau da Deborah Yakubu.

Tawagar majalisar Amurka ta zo Najeriya

A baya, kun samu labarin cewa 'Dan majalisar wakilan Amurka, Riley Moore, wanda ya shahara wajen caccakar gwamnatin Najeriya kan batun kisan Kiristoci.

Moore ya bayyana cewa ganawar ta bude wata sabuwar kafa ta fahimtar juna tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa an samu sakamako mai kyau da zai taimaka sosai.

Moore ya gana da mashawarcin Shugaban kasa a kan tsaro Nuhu Ribadu, yayin suka yo tawagar zuwa Najeriya domin tattauna batutuwan tsaro da rikice-rikice a yammacin Afrika.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng